Free chapter 路 Read without an account

Chapter 25&26

by Nanameera 路 IMARA

***

*IMARA 馃拫 馃拫*

25&26

Mikiya writers asso...

***

A hankali ta shiga bu蓷e idanunta, a 蓷an firgice ta tashi zaune tana 茩arewa 蓷akin kallo, turo 茩ofar 蓷akin a kayi, tayi saurin kallon wajen dan ganin wanda zai shigo. Wata irin bugawa zuciyar Imara tayi sanda tayi ido biyu dashi, ya 茩araso hannunsa ri茩e da tray. A kan table 蓷in dake gefen gadon ya ajiye sannan ya zauna kusada ita yana kallonta, saurin matsawa tayi muryarta na rawa ta ce"a'a, lafiya?, ina ne nan?, dan Allah ka mayar dani gidanmu" murmushi Maheer ya yi bai ce komai ba ya zaro wayarsa yana dannawa a hankali, kallonsa Imara tayi sai kuma ta sake kallon da茩in, tayi saurin mi茩ewa tsaye tana kallonsa ta ce"ni ka mayar dani gida, bangane wannan abun ba" wayarsa ya mayar aljihu ya mi茩e tsaye yana kallonta ya ce"ya kamata ki kwantar da hankalinki Imara, ki zauna ki ci abinci" wani kallo tayi masa ta 蓷auke kanta tana jijjiga 茩afa, murmushi ya yi ya ce "shikenan, zauna ki ci abinci sai muyi maganar" kallonsa tayi sai kuma ta kalii inda ya ajiye tray 蓷in abincin, yunwa take ji sosai hakan yasa ta nemi waje can gefe dashi ta zauna. Kallonta Maheer ya yi ya 蓷auko tray 蓷in ya ajiye mata a gabanta ya juya ya fice daga 蓷akin, da idanu ta bishi sai kuma ta gyara zamanta ta bu蓷e abincin, Irish potato ne aka soya shi da kwai sai plantain da akayi garnishing da ita. Tea ta ha蓷a sannan ta fara cin abinci. Saida ta cinye komai tas saboda yunwar dake cikinta, ta yi gyatsa. Kamar jira yake ta gama ci ya shigo 蓷akin, wannan karan ya sauya kaya, t-shirt ce white colour a jikinsa sai wando jins blue colour, kallo 蓷aya tayi masa ta sunkuyar da kanta tana wasa da fingers 蓷inta. 茦arasowa ya yi ya zauna gefenta, 茩amshin turarensa ya daki hancinta tayi saurin lumshe idanunta, a 蓷an firgice ta juyo ganin yanda ya ri茩e hannunta cikin nasa, kallonsa tayi taga murmushi yake, saurin janye hannun nata tayi tana turo baki ta ce"akan me zaka dinga ri茩eni?" Maheer couldn't help it but smile, above 2mins kafin ya ce"tashi mu je" tana kallon wani wajen daban ta ce"ina zaka kaini?, gida?" girgiza kansa ya yi ya ce"idan mun je zaki gani" ta蓳e baki tayi ta ce"ni to babu inda zanje" ta fa蓷a tana tura baki gaba. Murmushi ya yi ya ce"idan bazaki iya tafiya ba sai na 蓷aukeki" da sauri ta mi茩e tsaye tana zaro ido ta ce"Allah ya kiyaye" da hannu ya yi mata da su tafi, ta kalleshi sai kuma ta kalli hanyar, kamar wacce kwai ya fashewa a jiki haka ta fara tafiya.

A bakin shopping mall 蓷in ya yi parking, ta kalli wajen, idan bata manta ba sun ta蓳a zuwa wajen da Daddynta, sunkuyar da kanta tayi tana jin wata irin kewa, Allah sarki rayuwa ta tabbata idan da Daddynta na raye da zuwa yanzu ba wannan 茩addarar ce ta afka mata ba, Daddynta bazai ta蓳a aurar da ita a shekarunta ba. Kallonta Maheer ya tsaya yana yi ganin kamar bata jin abin da yake cewa, ta蓳a ya yi tayi saurin kallonsa sai kuma ta ha蓷e fuska,

"Meke damunki?"

Shiru tayi masa, ya ce"mu je ko?" sauka tayi daga motar ta tsaya tana jiransa, kashe motar ya yi ya fito yana kallonta ya ce"muje" tafiya ta fara yi tana kallonsa, suna shiga ya nemi kujera ya zauna, 蓷aya daga cikin ma'aikatan wajen ce tazo tana kallonsa ta ce"u are welcome sir" jinjina mata kai ya yi ta ce" me ake so?" Imara ya nuna mata ya ce "kaya wanda zai yi mata nakeson ki ha蓷a" cikin girmamawa ta ce"okay sir, ta kalli Imara ta ce"mu je Madam" kallonsa Imara tayi ya gya蓷a mata kai sannan tabi bayanta. Kaya sosai aka siya mata masu tsada kafin su bar mall 蓷in, a wani restaurant ya tsaya ya yi parking yana kallonta ya ce"mu je kici abinci" da sauri ta kalleshi sai kuma ta 蓷auke kanta tana kallon titi ta ce"bayan wanda naci, ni bana jin yunwa" murmushi Maheer ya yi ya ce"ai tunda rana kika ci abinci, kuma kinga yanzu magrib akayi"

"Nidai a 茩oshe nake, naga 蓷azu naci abincin, kawai ka mayar dani gida mana" ta fa蓷a ba tareda ta kalli inda yake ba. Bai sake magana ba ya sauka daga motar kai tsaye kuma cikin restaurant 蓷in ya nufa, binsa tayi da harara a 茩ufule ta ce"aikin banza, ko ana dole" .

Bayan minti goma Maheer ya fito hannunsa ri茩e da ledoji guda biyu, kallo 蓷aya Imara tayi masa ta 蓷auke idanunta, har suka je gida babu wanda ya sake magana a cikinsu. Bayan ya yi parking ya kalleta ya ce"ki shiga ciki zan je na dawo" bata ce masa komai ba ta bu蓷e handle 蓷in motar ta sauka, ledojin daya mi茩o mata ta kalla sai kuma ta ce"amma nace maka na 茩oshi ko?" murmushi ya yi ya ce"ai ba cewa nayi ki ci ba, ki shiga dashi kawai" 蓷an tura baki ta yi sannan ta amsa ta juya ta shige gidan. Da idanu Maheer ya bita sai kuma ya girgiza kansa fuskarsa fal murmushi ya yiwa motar key ya bar gidan.

Imara nashiga ta wuce sama kai tsaye, 蓷akin da ta zauna 蓷azu nan ta shiga. Ta ajiye veil 蓷inta kan gadon sannan ta shige toilet ta 蓷auro alwala, tana fitowa ta tsaya jikin mudubi tana kallon veil 蓷in data ajiye, ya yi 茩arami da sallah hakan yasa ta bu蓷e wardrobe 蓷in dake 蓷akin ko zata samu wani abu, 蓷an kwa蓳e fuska tayi ganin babu komai a ciki, ta koma ta zauna ta zuba uban tagumi.

Sai bayan sallahr magrib sannan Maheer ya shigo gidan, time 蓷in tana zaune bayan ta idar da sallah da veil 蓷in nata, sallama ya yi ya turo 茩ofar ya shigo, a ciki ta amsa sallamar ya 茩araso ya zauna gefenta yana kallonta ya ce"tashu muje 茩asa kici abinci" kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta ce "sai yaushe zaka mayar dani gidanmu?" numfasawa ya yi ya ce "Imara Inason kibar wannan maganar, idan Allah ya kaimu next week zamu tafi gida, kinsan yanzu ke matata ce, saboda haka ni ne nakeda ikon tafiya dake duk inda zani, kuma bakida wani waje sai inda na ajiye ki, nayi miki al茩awarin zan kula da ke fiye da yanda kike tunani. Zan kai ki cikin ahalina, zan zame miki uwa zan zame miki uba, abinda kawai nakeso shine yardar ki" ya 茩arashe maganar yana dafa hannunta, kallon hannun nata tayi sai kuma ta kalli fuskarsa, haka kawai ta ji ta yarda da Maheer, ta yi shiru na wasu mintuna sannan ta ce"meyasa ka aureni?" murmushi Maheer ya yi ya ce"saboda ina sonki" cikin rawar murya ta ce"zan yarda da kai amma dan Allah karka juyamin baya, karka sakani kuka, ka 蓷aukeni matsayin 茩anwarka wacce ba zaka cutar da ita ba, kaji Yaya!"

Da sauri Maheer ya 蓷ago ya kalleta sai kuma ya yi murmushi ya kamo hannunta ya ri茩e cikin nasa ya ce"Thank you" 蓷an murmushi tayi har saida beauty point 蓷inta ya loma ta ce"nima nagode" hannunta ya kama ya tashi ya ce"muje ki ci abinci" gya蓷a masa kai tayi ya nuna mata hanya, tayi gaba ya bita a baya.

Tun daga wannan ranar suke zaune lafiya da Maheer a kullum sha茩uwa 茩ara shiga tsakaninsu take, a haka har suka 茩arasa wannan satin, ranar Lahadi tana zaune bakin mirror tana gyara kanta ya shigo, 茩arasowa gabanta ya yi yana murmushi ya tsaya a gefenta yana kallonta ta jikin mudubi, kallonsa itama tayi tana murmushi

"Madam idan kin kammala muna iya tafiya" tashi tsaye tayi bayan ta yi parking gashin nata ta ce"Eh na shirya" gya蓷a kai ya yi sannan ya kama hannunta suka fita daga 蓷akin. A compound 蓷in gidan suka tsaya, ya bu蓷e mata backseat ta shiga sannan shima ya shiga driver ya ja motar suka tafi, kai tsaye airport suka shige, not too long kuma jirgin su ya tashi i zuwa Qatar.

Around 7pm suka shigo fadar, babu kowa a babban parlon hakan yasa kai tsaye yaja hannunta zuwa 蓷akinsa, ha蓷a蓷蓷en 蓷aki ne wanda yaji kayan more rayuwa, komai na 蓷akin blue colour ne, domin shine favourite colour na Maheer, kallonta ya yi yana murmushi ya ce"yawwa Katalina shiga kiyi wanka, akwai kayan ki zan 蓷ebo miki" da wani irin mamaki Imara ta kalleshi sai kuma tayi murmushi ta ce"yaya manta sunan nawa kayi?, ko kuma tsokanata kake?" girgiza kai ya yi fuskarsa babu alamar murmushi sa蓳anin 蓷azu ya ce"akan me zan manta sunan ki?, sunan da kika ji na ambace ki dashi shine sunan dana za蓳a miki, kuma muddin kina cikin fadar nan shine sunan da zaki dinga amfani dashi"

Tunda ya fara magana Imara ke kallonsa baki bu蓷e, kwata-kwata bata gane abinda yake fa蓷a, 茩wa茩walwarta ta tunkushe tunani ya yi mata yawa, ganin yana shirin fita yasa tayi saurin shan gabansa tana ri茩e rigarsa ta ce cikin rawar murya

"Yaya Maheer bangane abinda ka fa蓷a ba, ka daina yimin irin wannan wasan, tsoro nakeji, zan daina kula ka wlh, banaso, tsoro nakeji...!" Ta 茩arashe maganar tana fashewa da kuka, ta rungumeshi, 蓷an tsaki Maheer ya yi kafin ya janyeta daga jikinsa yana kallon fuskarta wacce ta ji茩e da hawaye ya ce"it's better for you to obey my rules or else..." Ya yi mata gargadi da hannunsa sannan ya fice daga 蓷akin.

Zubewa Imara tayi akan tiles 蓷in 蓷akin, banda tsuma babu abinda jikinta ke yi, wace irin masifa ce ta tunkarota?, wane hannu ta fa蓷a?, wace Katalina?, me Maheer ke nufi?, ko dai mafarki take, tunanin hakan yasa tayi saurin dukan fuskarta idan ma mafarki take ta farka, amma ga mamakin ta sai taga idanunta biyu. Kifa kanta tayi bisa gwuiwoyinta ta fashe da wani sabon kukan.

茦arfe takwas da rabi Maheer ya bu蓷e 蓷akin ya shigo, zaune ya sameta kan tiles idanunta sun kumbura, 茩arasawa ya yi ya sanya hannunsa ya 蓷agota yana watsa mata wani kallo ya ce"kee!, ina wasa dake ne?, baki ji abin da na ce miki ba?, kina son ranki ya 蓳aci right?" girgiza kai Imara ta shiga yi ta ce"a'a wlh, tsoro naji yaya, dan Allah mu koma Jigawa, ka mayar dani gida, tsoro nakeji, bazan iya zama a nan ba" wani tsaki yaja yana kallonta ya ce"karki sake kiramin sunan wani gari anan, ki shirya yanzu ki sakko 茩asa, nasan kin iya yaren su, dan basa jin Hausa" juyawa ya yi ya fita kafin ta bu蓷e bakinta. Dafe kanta tayi ta jingina da wardrobe cikin wata raunatacciyar murya ta ce"inna lil lahi wa ina ilayhi raji'un, nashiga uku, wayyo Allahna, meke faruwa da rayuwata ne?, wace irin masifa nashiga?" Rashin sanin wanda zai bata wa蓷annan amsoshin ya sanya ta sake fashewa da wani sabon kukan.

A hankali tafara taka stairs 蓷in benan, sanya take da wata Abaya white colour ta yafa veil 蓷in Abayar tana tafiya tana kallon fadar. Daga can gefe taji ance

"Tabarakallah"

A 蓷an firgice ta juya, sai kuma ta hangi jama'ar gidan zaune akan dinning table. A hankali ta 茩arasa bakinta na rawa ta gaishesu cikin harshen larabci, fuska a sake suka amsa mata musamman Shammah, ta kalleta cikin sakin fuska ta ce"zauna mana" ta fa蓷a cikin harshen larabci, cikin sanyin jiki Imara ta zauna ta sunkuyar da kanta, a hankali ya tura kujerar ya tashi, da sauri suka kalleshi, Immi ta ce"lafiya?" bai ce mata komai ba ya juya ya bar wajen, da idanu duk suka bi shi, banda Imara wacce har sannan kanta yake a sunkuye. Girgiza kai Shamma tayi ta cigaba da cin abincin ta, dakyar Imara taci abincin bayan takurawar da Shamma tayi mata.

12:30am.

Zaune take gefen gadon ta jingina da jikinsa, tunani ne fal zuciyarta, duk da dare ya yi sosai amma babu alamar bacci a tare da ita, tanada bu茩atar ta yi magana da Maheer. Ta kasa gane abin da yake shirin faruwa da rayuwarta. Tana cikin wannan tunanin ya shigo 蓷akin yana sanye da wasu pyjames black colour, s hankali ta saki ajiyar zuciya dan har ga Allah taji da蓷in shigowar tasa, zama ya yi gefen gadon yana kallonta, gyara zamanta ta yi, tana 茩o茩arin magana ya 蓷aga mata hannu.

"Nasan abinda zaki ce, nasan me za ki tambaya, wane ne ni?, meyasa na aureki?, me nake nufi dake?. To bar kiji, ni Maheer ne kamar yanda kika sani, kuma 蓷a ga Amir wato Sheikh Fahad bin saleem al-kuwari, na aureki saboda wani dalili, ba lallai bane na sanar dake, the main thing shine ki yi duk wani abu dana umarce ki, daga yau ba irin wannan shigar nakeson kiyi ba, kuma daga yau sunanki Katalina a idona ba IMARA ba, idan har kika kuskura kika ce zaki sa蓳amin to ba zaki ji da蓷in zama cikin fadar nan ba, saboda haka ki kasance yanda nakeso shine kawai abinda zai ceceki.

Kallonsa kawai Imara take tana hawaye, cikin rawar murya ta ce"daman ba saboda Allah ka aureni ba?, daman 茩arya kayimin?, meyasa zaka yaudareni?, meyasa zaka sanya mini soyyarka a zuciya sannan ka cutar dani?, akan me ka rabo ni da dangina?, meyasa! meyasa Maheer!!"

Tashi tsaye ya yi yana kallonta ya ce"ke kika ga zaki iya wahalar da kan ki, kina sona, bakya sona wannan bai dameni ba, abinda nakeso shine kawai abinda nake aiwatarwa, saboda haka za蓳i ya rage naki, kiyi biyayya ki zauna lafiya. Kuma ma da kike magana akan na raboki da kasarku, wa kike dashi a 茩asar?, wane gatanki?, zaman kanki fa kike, ai auranki da nayi taimako ne a gareki, saboda haka ni ba abin rainawar ki bane, fact.

Da idanu Imara ta bishi har ya 蓳acewa ganinta, ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, dan kuka ma ya gagareta sai na zuci, komawa tayi ta jingina da gadon tana numfashi sama sama, kafin kuma ta samu ta fashe da wani raunataccen kuka mai shiga zuciyar mae sauraro. Yanda Imara taga rana haka taga dare cikin masarautar Udaid sanda taji anfara kiran sallah asuba ta tashi ta 蓷auro alwala ta zauna kan ladduma tana ro茩on Allah ya kawo mata mafita.

A haka ta cigaba da rayuwa a cikin gidan cikin takurawar Maheer, ko ka蓷an baya barinta ta sake, gaba蓷aya ta rame kamar ba ita ba, kullum sai zama a 蓷aki tana kuka. Yau ma kamar kullum tana zaune kan kujera cikin 蓷akinta ta zuba uban tagumi, akayi sallama aka shigo, a hankali ta 蓷aga kanta jin ba muryar Maheer ba, Ameer da ta gani ya sanya tayi saurin mi茩ewa tana 茩a茩alo murmushin 茩arya ta ce"sannu da zuwa Ameer" lumshe idanunsa ya yi sannan ya bu蓷e su akanta, cikin rawar baki ta ce"na manta Ameer ka zauna" gya蓷a mata kai ya yi sannan ya zauna gefen gadonta cikin wata kamilalliyar murya ya furta

"Bismillah"

Zama Imara tayi itama tana kallonsa ta ce "Ameer lafiya?" kallonta ya yi da dara-daran idanunsa ya ce"IMARA"

"Na'am Ameer"

Numfasawa ya yi sannan ya ce"nasan zaki yi mamakin abinda zai fito daga bakina, duk da nima abun ya zo mini a bazata, bansan yaushe ba, bansan kuma dalili ba, amma naji na kamu da sonki tun ranar dana fara 蓷ora idanuna akan ki, inaji kamar ba ranar nafara ganinki ba. Nayi 茩o茩arin ganin na cire tunanin daga raina amma nakasa, inason ki Imara, ina sonki, soyyaya irin wacce bansan iyakarta ba, duk da ke matar 蓷ana Maheer ce amma ina fa蓷a miki haka, wlh ina sonki har cikin raina"

A 蓷imauce Imara ta tashi tsaye tana nuna shi da yatsa amma ta kasa cewa komai, ta shiga girgiza kanta hawaye na zuba akan fuskarta, tayi saurin dafe kanta tana rusa kuka, tashi tsaye Ameer ya yi yana kallonta sai kuma ya girgiza kai ya ce"ban fa蓷a miki sirrin dake zuciyata dan naga hawayen ki ba Lolo, Inason ki zauna kiyi tunani akan magana"

"Tunani?!, tunani fa Ameer?, me zanyi tunani?, ni ce fa IMARA matar Maheer 蓷anka, amma ni kake so?, meyasa kuke son ganin 茩arshena ta hanyar irin wa蓷annan halayen naku, nakasa fahimtar komai, nakasa ganewa, 茩wa茩walwata tayi 茩arama ba zata iya 蓷aukan irin wa蓷annan tashin hankalin ba, kallon uba mahaifi nake maka nayi tunanin kaima zaka yimin kallon 蓷iyarka wacce ka haifa, meyasa kake 茩o茩arin cutar da rayuwarta?, akan me zaka bari she蓷an ya shiga zuciyarka har ya sakaka furta irin wa蓷annan zantukan. Dan Allah ka tuba tun wuri Ameer, babu wanda zan fa蓷awa, wlh nayi maka al茩awari, amma karka sake irin wannan maganar. Numfasawa Ameer ya yi idanunsa na kallon 茩asa, s hankali ya 蓷ago ya kalleta, gaba蓷aya launin idanunsa ya koma ja ya girgiza mata kai zai yi magana tayi saurin shigewa toilet saidai kafin ta rufo 茩ofar har Ameer ya rigada ya shigo.

Cigaban labari.

Banda kuka babu abinda take yi Mama na taya ta, saida tayi mai isarta sannan ta 蓷ago kanta tana kukan ta ce "meyasa Mama?, bayan duk wannan wahalar dana sha ya rabu dani, duk wanda ya ra蓳eni a rayuwa da niyyar naji da蓷i sai ya tafi ya barni, kowa baya zama tare dani, nafiso ma na mutu. Ta kalli Mama dake kuka ta ce"dan Allah Mama ki bani abinda zanci ko nasha na mutu, nagaji da rayuwar, banida kowa, banida kowa Mamah! Ni marainiya ce, wacce batada mai sonta, duk sun mutu, meyasa ni nake a raye Mamah?, meyasa!?, dan Allah ki bani abin mutuwa..." Rungumeta Mamah tayi tana shafa kanta ta ce"karki sake cewa haka Imara, kinada kowa, mu zamu zama dangin ki, ba za ki sake maraici ba IMARA, ki daina kuka kinji" ta cigaba da shafa sumar kanta, ajiyar

zuciya Abaan ya sauke kafin ya juya ya bar wajen ba tareda ya shiga 蓷akin ba.

# *Heart touching 馃挃*

# *IMARA馃拫馃拫*

# *Nanameera*

# *2025*.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.