Free chapter 路 Read without an account
Barrister Hibba
馃挜 BARRISTER HIBBA 馃挜
鉁嶏笍 Nusy bee
Page 3
Yana kallon kiran su Mifra yana shigowa a wayar ummin nashi amma bai 蓷aga ba,daga baya ma sai ya danna musu busy ya kashe wayar,a lokacin gaba 蓷aya ya manta da wata Hibba da alwashin da ya 蓷auka akanta, saboda tunawa da matar shi abar 茩aunar shi wadda ya rasa ta shekaru biyu da suka wuce a haihuwar ta ta biyu,tabbas yaso Namra, Namra ta so shi, soyayyar da suka yiwa juna ba ka蓷an bace, family 蓷in su har tsokanar su sukeyi Layla da majnun,yau gashi a doron duniya amma babu Namra,kuma ya san samun kamar Namra a rayuwa abu ne mai wahala,mace ce selfless,mai kirki da damuwa da damuwar wasu,a kowanne lokaci damuwar shi tana gaba da tata, shiyasa yake jin har abada bazai samu mace kamar Namra ba
Jiki a mace ya mi茩e ya bar office 蓷in ba don lokacin tashin shi yayi ba,sai don babu wani aiki da zai iya 茩ara yi yanzu
ALI MUHAMMAD KABO AREA, RAILWAY ESTATE, KANO STATE
"Mtseeeeewwww,dalla malama kiyi ki fito,You are wasting my time,kizo kiyi ta sme sme kina 蓳ata wa mutane lokaci,haba!"a cewar Marwa cikin fusata
A kaikaice Arwa ta kalli Marwa tana fa蓷in"dalla malama kar ki dame ni,ki bar ni naga shiryawa a nutse,kar ki rikita min kai"
"Okay in tsaya ki cigaba da 蓳ata min lokaci, wallahi zanyi tafiya ta,yamma tana yi kuma kin san yaya ta hana mu yin yamma a waje"
"Mtseew sai kiyi ai,拼ar wahala"
"Ni kike kira 拼ar wahala? wallahi bazan sake tafiya da ke ba,aikin banza kawai"daidai nan mama ta iso wajen tana fa蓷in"to Tom and Jerry,kun fara raba halin ko?ku dai Allah ya shirye ku,ban san ranar da zaku girma ba wallahi"
"Tun 蓷azu fa na sanar mata zamu je shopping,kin gani wai sai yanzu take shiryawa fa,na mata magana zata fara min rashin kunya"
Arwa tayi shewa tace "sai dai uwar rashin kunya,idiot ke yanzu a mentality 蓷in ki kece babba akaina ko?"Marwa tayi kan Arwa da duka,mama ta ri茩e ta ta fara fa蓷a"wato a gaba na zaku cigaba da raba hali ko?to wallahi idan baku kama kai kun daina shiririta ba zan kira yayar ku in fa蓷a mata,don bazan iya tashin hankali ba"Arwa dai bata sake magana ba,ta 蓷auko tsadaddiyar jakar ta irin ta Marwa,dama kayan jikin su ma iri 蓷aya ne,wasu tsadaddun English wears ne riga da skirt sai mayafi da suka 蓷ora, Marwa tayi gaba Arwa ta bi bayan ta tana fa蓷in"mama sai mun dawo"
Suna zuwa lokacin Muyassar ya fito da mota yana jiran su, kallo 蓷aya yayi musu ya 蓷auke kai,don har yau bai manta abinda Marwa tayi masa ba,gashi dukkan su ba gane su akeyi ba ballantana ya ware wadda tayi masa ya ajiye ta a gefe,babu wadda ta damu da shan 茩amshin shi,don Marwa ma wayar ta take dannawa, Arwa ta dube shi fuska babu yabo babu fallasa tace"maya global house zaka kaimu,zamuyi shopping ne"batare da ya kalle su ba yace"to ba matsala"
Sun hau titi sosai,wayar Marwa tayi 茩ara,da zumu蓷i ta ciro wayar daga jaka,don ringing tone da ta saka wa mai kiran ta dabam ce,itama Arwa cike da zumu蓷i ta 茩ara matsowa, Marwa ta 蓷aga,a tare suka ha蓷a baki suna kiran"miss You so much Yaya,how are you doing?"
"I'm good,how was your holiday?"
Marwa tace"is not funny doing holiday without you and Maryam, please come back Yaya"a shagwa蓳e take maganar
茒an murmushi matar tayi tace"I'm coming soon, where is Arwa?"Arwa tayi karaf tace"I'm here Yaya,how was little?"
"She is missing you, what are doing now?"
Arwa tace"maya global house muka nufa,zamuyi shopping ne"abinda ta fara fa蓷a ne ya sanya su kallon juna cikin mamaki da takaici,don fa蓷a takeyi ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,a 茩arshe ta tabbatar musu da kar su je ko'ina su koma gida
Muyassar yana gaba yana jinsu, zuciyar shi cike da mamakin wannan ji da kai da isa irin ta yayar tasu,da alamu bata bar kowa, Arwa ce tace"driver ku koma gida kawai"cikin 茩unar rai tayi magana
"Sai muyi shopping 蓷in online kawai, tunda yaya tace mu koma gida"a cewar Marwa
Har suka je gida babu wadda ta sake magana saboda takaici,amma still basu ji haushin yayar tasu ba,suna fitowa kowacce ta wuce 蓷akin ta
ANNASTRASSE, FRANKFURT CITY, GERMANY
茦aton luxury room ne da ban ta蓳a ganin mai kyau da ha蓷uwar shi ba,daga kan royal bed, cupboard,hatta da su bed side lamp rantsatstsu ne,duba na nakai kan kantamemen gadon,wanda aka shimfi蓷a masa farin bed sheet 茩al,ta lullu蓳a da farin duvet,dogon gashin ta da ya sha gyara da kula ya zuba ya rufe mata fuska,a hankali naga tana 茩o茩arin bu蓷e idanun ta,zaunawa tayi kan gadon tana karanta addu'ar tashi daga bacci a zuciyar ta,ta kai a 茩alla mintuna biyar kafin ta sanya hannayen ta ta mayar da gashin ta bayan kunnuwan ta,sai a lokacin na samu 茩are mata kallo
Tsananin kammanin ta da twins Arwa da Marwa na gani,sai dai ita bata kai su haske ba,kai tsaye baza'a kira ta fara ba kuma baza'a kira ta ba茩a ba,tashi tayi ta sauko daga gadon,daga yanayin tafiyar ta na fuskanci cewa the lady is unique and classy,Kai tsaye ban蓷akin da ke cikin 蓷akin ta shiga,ta kai a茩alla one hour kafin ta fito, shiryawa tayi cikin riga da wando track suit farare masu tambarin 茩ungiyar wasan 茩wallon 茩afa ta PSG,ta 蓷aura scarf a kanta ta 蓷aura agogon ta na diamond sannan ta fice daga 蓷akin
茒akin kusa da ita ta bu蓷e ta shiga,wow!ya ha蓷u sosai amma bai kai nata ba,daga can gefe 蓷an madaidaicin gado ne,sai dai tsadadde ne sosai, yarinya ce wadda a茩alla zata iya kai wa shekaru biyar zuwa shida, a kallo 蓷aya mutum zai tabbatarwa kanshi yarinyar baturiya ce,yanayin kalar fatar ta da gashin kanta,ta nutse a tsakiyar gadon ta sai bacci take peacefully
Tun tashin ta batayi murmushi ba sai da tayi arba da lovely soul 蓷in tata,tayi murmushi sosai kafin ta matsa kusa da ita ta fara bubbuga pillow 蓷in ta tana fa蓷in"time up baby!it is getting late,wake up!wake up sweetheart!!!"
A hankali yarinyar ta fara bu蓷e blue eyes 蓷in ta, murmushi ta 茩ara yi tana fa蓷in"say your dua best friend"蓷an murmushi yarinyar tayi tana karanto addu'ar tashi daga bacci,bayan ta gama ta mi茩e zaune,ita kuma ta kama hannun ta har bakin toilet,cikin Yaren German tace mata"kiyi alwala kiyi sallah,zan yi miki wanka,yau zamu wuce UK wani aiki,daga can zamu wuce Nigeria"
Tuni yarinyar ta wartsake cikin Yaren German itama take fa蓷in"zamu ga su Aunty twins?
Da murmushi cikin harshen turanci tace" of course dear,our flight is in next two hours, please be hurry"daga haka ta fice daga 蓷akin
Tana komawa 蓷akin ta wayar ta ta fara 茩ara,sai da ta 蓳ata sakwanni kafin ta 蓷aga batare da tace komai ba
A 蓳angaren Barrister Khadijat ta soma magana don ta san halin mutuniyar tata
"BARRISTER HIBBA AIYO! I hope you are doing good!"
Yatsina fuska Hibba tayi tana fa蓷in"I'm normal,how was your husband and children?"
"They are all fine, barrister,it is about that case,you are not saying a word"
Yatsina fuska tayi tace"yeah! I'm aware, everything is moving smoothly, don't bother yourself, and, don't say a word to barrister Awwal tofa"
Murmushi mai sauti Barrister Khadijat tayi tana fa蓷in"Hibba kenan,do you said anything to me ne da kike tunanin zan gayawa wani?"
Hibba tace"na dai fa蓷a miki,don't say anything to barrister tofa, talkless of another person"tana kaiwa nan ta kashe wayar ta,ta jefar kan gado sannan ta wuce wajen kayan ta ta zari abubuwan ta masu amfani ta zuba a 蓷an 茩aramin akwati
茦arfe takwas da mintuna goma sha bakwai suka fito daga gida ita da yarinyar ta,sanye suke da jacket ta sanye manya manya, Hibba ce ke jan akwatin yayin da ta ri茩e hannun Maryam,kai tsaye Frankfurt airport suka nufa,basu kara awa guda a Frankfurt ba jirgin su ya 蓷aga zuwa manchester na 茩asar United kingdom (England)
Suna sauka basu 蓳ata lokaci ba kai tsaye suka wuce saint Mary's hospital da ke nan manchester,sai da hibba tabi dukkan 茩a'idojin asibitin sannan akayi leading 蓷in ta zuwa 蓷akin wadda take bu茩atar gani,duk da 蓳ata mata lokaci da query da ta amsa bata wani damu ba
#Nusy_bee