Free chapter 路 Read without an account

2

by Kansa'u Bello 路 MATAR MANYA

馃挀MATAR MANYA馃挀

By

OUM FATIMA

GAJEREN LABARI

PAGE 2

BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM

Tafiya nake cikin yanga da taku 蓷ay-蓷aya wanda na san yana jan hankalin duk wani wanda yayi tozali dani, tasowarmu kenan daga Makaranta wacce nake ajin 茩arshe a Secondary. Sanye nake cikin Uniform 蓷ina kalar blue da fari wanda yayi matu茩ar haska farar fata ta dake ta she茩i sabo da tana samun isasshen gyara. Kai in ka ganni kai tsaye bazaka ce shekaruna duka basu wuce goma sha takwas ba sabo da yanda nake da cika ido, sai ka 蓷auka 拼ar jami'a ce ba 拼ar secondary ba.

Tarkon dana 蓷ana kuwa ya kama kurciya domin wata zu茩e茩iyar Mota ce data zo wucewa ta dawo da baya tana min horn, yi nayi tamkar ban san dani ake ba nayi gaba ina jan ajina. Direban dake tu茩a Motar ne ya fito ya tare ni da sallama yace "Madame yalla蓳ai ne yake son magana dake, Bismillah." Ya fa蓷a yana nuna min Motar daya bu蓷e mun gidan baya inda mai gidan nasa yake hakimce a ciki.

Juyawa nayi zanci gaba da tafiya duk don jan zarena yanda ya kamata, amma a 茩asan zuciyata fata nake kar ya 茩yaleni yaci gaba da naci. Kamar yanda nayi fatan kuwa bina yayi yana cewa "Madame kin san waye kuwa yake son ganinki kike 茩o茩arin yiwa kanki ba茩in ciki?." Jin abinda ya fa蓷a yasa zuciyata yin tsallen murna tana ayyana cewar ba 茩aramin kamu nayi ba.

Amma a zahiri sai na ha蓷e rai na fuskance shi nace "Ko waye shi ai bai kamata ya tare yarinyar mutane a titi ba ko?."

"Ke ba irin su yalla蓳ai ake yiwa musu b..." Sallamar da muka ji a bayanmu da wata dattijuwar murya yasa direban bai 茩arasa maganar ba ya juya da rawar jiki yana yiwa uban gidan nasa magana. Ni kuma da wutsiyar ido nake 茩are masa kallo ba tare da kowa ya lura ba. Babban mutum ne da a 茩alla zai kai shekara hamsin koma fiye da hakan, amma kallo 蓷aya zaka masa ka san cewa naira ta zauna masa. Sai dai fa ba茩ine sosai irin mai shaining 蓷in nan, ba za'a kira shi mummuna ba kai tsaye sabo da gyara da hutu sun 蓳oye hakan.

Duka a cikin 拼an seconds 蓷in da basu wuce goma ba na 茩are masa wannan kallon, "Wa'alaikumussalam." Na amsa masa sallamar kafin na 蓷ora da gaishe sa "Am kiyi ha茩uri an tsayar dake a titi kuma hakan ba girmanki bane, ga katina idan kin koma gida ki kirani sai muyi magana." Ya fa蓷a yana mi茩a min katinsa daya fito da shi. Hannu nasa na amshi katin na masa godiya nayi gaba abina.

Suna wucewa naji kamar in kwaso shoki tsabar jin da蓷i amma na maze, ban san daga ina ya taho ba sai gani nayi kawai ya sha gabana ya mi茩amin hannu "Bani katin nan." ya fa蓷a fuska a 蓷aure ba alamar wasa.

"Wai Suhail meye haka kawai zaka sha gabana ba ko sallama kace in baka kati, ajiyarsa ka bani da zakace in baka." Na fa蓷a nima fuska a ha蓷e don ko mai zai yi ba zan bashi ba ya jawo min asara naga samu in ga rashi, don haka na 茩ara dam茩e katin a hannuna.

"Salma ki bani katin nan nace ko?."

"Bafa zan baka ba Suhail, gara ma ka ha茩ura."

"Wai me yasa kike irin haka ne, shike nan ke ba damar kiga Mutum da 茩atuwar Mota sai kibi ki tada hankalinki, kin manta cewar Allah shine mai azurta bawa a lokacin da yaso, Salma kin san ina sonki tsakani da Allah kuma aurenki zanyi amma kin ki tsaida hankalinki wuri 蓷aya, haba Salma me kike nema ne a duniya ina sana'a ta dai-dai gwargwado kuma sannan ina karatuna, in sha Allah kafin lokacin daza muyi aure zan kammala karatuna kuma in sami aikin yi muyi aurenmu muyi zaman mu cikin rufin Asiri."

Yana maganar cikin rarrashi amma wani irin 蓳acin rai take sa min, ji nake kamar in make shi wai wani yana sana'a yana karatu sannan in ya gama zai samu aiki, ni kuma ina zaune sabo da ga Salmar mahaukata in yi ta zaman jiransa sai ya samu aiki bayan ga manyan Alhazawa masu Naira a hannu ina gani.

"Kaga Suhail sai an jima, daga Makaranta na dawo ko hutawa banyi ba ka tare ni da Wa蓷annan magan-ganun naka." Na 茩are maganar ina yin gaba abina. Bin bayanta yayi da kallo yana jin rashin da蓷i a ransa na abinda take masa, Allah ne ya jarabceshi da soyayyar Salma so mai tsananin da baya ganin laifinta akan abubuwan da take masa, duk irin tarin 拼ammatan dake haukar son sa ciki harda ya'yan masu ku蓷i amma bai ga wacce tayi masa ba sai ita, gashi ita kuma ku蓷i kawai take ganin daraja da 茩imarsu shi kuma baya dasu shi yasa yake matu茩ar shan wahalar ta.

A kullum bashi da burin daya wuce yaga ya faranta mata shi yasa duk abinda ya samu yake 茩o茩arin ganin ya kyautata mata, amma sai dai kyauta 蓷aya wani saurayin mai ku蓷i zai yi mata ta manta da duk tarin kyautatawarsa a gare ta. Hakan da take masa bai ta蓳a sawa sonta ya ragu ko ka蓷an a zuciyarsa ba, shi yasa ya dage yake karatu tu茩uru yake kuma ta蓳a sana'ar sayar da katin waya, ajiyar zuciya ya sauke ya juya ya nufi inda za shi.

*****Sallama nayi lokacin dana shiga zauren gidanmu wanda koda yaushe baya rasa mutane masu shige da fice wurin Baba Mari don sayen abincin da take sayarwa. Da Karima da Aliya na ha蓷u a zauren 蓷auke da kwanikan abincin da suke sayarwa yayinda 茩annensu Maza ke 蓷auke da manyan kulolin abincin sayarwar tasu.

Ido muka ha蓷a suka kalli juna suka bushe da dariya "Kaga 拼ar Malam Shehu matar manya, da girman kujerarki." Karima ta fa蓷a cike da sha茩iyanci. Tsaki naja na tsartar da miyau nace "瞥an wahala kanku ake ji, ku dai kuje kuyi ta fama da kayan talla kuna zaune wani hamsha茩in zai aureni, 蓷an ba茩in ciki sai dai ya mutu." Ina gama fa蓷a nayi gaba na barsu suna cewa "Idan hamsha茩in bai aureki ba an ba wani almajirin sadakarki duk randa Baba ya gaji da iskancin da kike wa mutane 拼ar mai da dogon burin tsiya." Aliya ta fa蓷a cikin jin haushin maganar dana fa蓷a musu.

"Oho dai kanku ake ji 拼an ba茩inciki." Na fa蓷a ina 蓷aga murya don nayi nisa.

"To sababbiya yau kuma keda waye kike faman yiwa mutane tijara daga shigowarki." Baba Mari ta fa蓷a daga bakin murhun da take sallamar masu sayen abincinta.

"Nida wanda ya shiga gonata." Na fa蓷a ina murgu蓷a baki na shige 蓷akinmu ina jin Baba Mari na fa蓷in "Uwarki Hadiza kika yiwa ba ni ba, fitsararriya mara kunya."

Zan 蓷aga baki in maida mata Mama ta wurgo min wani mugun kallon daya sa naja bakina nayi shiru ina turo shi gaba. "Kin kyauta Salamatu, nace kin kyauta, ko me tayi min bake kika jawo ba, ai dama hausawa sunce 蓷an kuka shike jawa uwarsa jifa. Ace baki da aiki kullum sai janyo min magana a gidan nan kullum ke Salamatu ko 茩annenki gasunan basa abinda kike yi, mai kike son zama ne wai ni kam?." Ta 茩are maganar tana kafe ni da ido.

"Allah ya baki ha茩uri Mama, ni kam na matsu in gama wannan makarantar in samu wani Alhajin in aure in bar wannan azababben gidan in huta da ciwon kan Mutanen cikinsa." Ma 茩are maganar a hankali sosai yanda Mama baza taji abinda na fa蓷a ba.

"Allah ya shirya." Kawai ta fa蓷a ta kabbarta sallarta ni kuma na aje jakar Makararanta ta na shiga cire kayan jikina don yin wanka in yi sallar nima....

Oum Fatima

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol