Free chapter 路 Read without an account
Chapter 39-40
by Amanarcool 路 RAMIN 茦ARYA...
馃挮 *RAMIN 茦ARYA....* 馃挮
*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*
_WRITING BY AMANAR COOL_鉁嶏笍
Free book 馃摎
Page 39&40
____________"Why Afnan i m deeply in love with you. Ya ki ke so na yi da rayuwata? Afnan you are the one my heart chose. Ta ya za ki yi mini haka? Me yasa tun farko ba ki fa蓷a mini ki na da saurayi ba? Sai da ki ka bari na fa蓷a soyayyar ki, Afnan what do you mean da 蓳oye minin da ki ka yi?".
"Dan Allah ka yi ha茩uri, ni ma ba da sanina hakan ta faru ba, ka yi ha茩uri, ka yi ha茩uri my Haidar".
"Afnan Afnan"
Cikin razani ta farka da ga baccin daya 蓷auke ta sakamakon kiran da Mama ke yi mata, cike da mamaki Mama ke bin Afnan da kallo, jin ta na ambatar sunan namiji a cikin baccin ta, abin da ko a fili ba ta ta蓳a yi ba.
Afnan kuwa sunkuyar da kai tayi ta na tuna mafarkin da tayi da Haidar.
Mama ta ce "Afnan lafiya ki ke kuwa? Waye Haidar? Me ye ala茩arki da shi da har ki ke ambatar shi a cikin baccin ki? Ko a zahiri banta蓳a jin sunan sa a bakin ki ba, waye shi?"
Cikin kasala da sanyin jiki Afnan ta ce "Mama ni ma ban san shi ba, kawai sharrin mafarki ne"
Shiru Mama tayi ta na 茩are mata kallo sannan ta ce "Allah ya kyauta, zazza蓳in ya sauka ne?"
"Eh ya sauka da sau茩i"
"To Allah ya 茩ara afuwa, ta so ga Bilki nan na jiran ki".
Ta amsa da "To" Mama ta fita a 蓷akin, ita ma a hankali ta mi茩e ta fita daga 蓷akin, a zaune ta tarar da Inna Bilki ta na ri茩e da kofi a hannun ta, ta na juya wani abu da bata san ko meye ba, zama tayi ta gaishe ta.
Cikin sakin fuska Inna Bilki ta amsa gaisuwar, tare da yi mata ya jikin.
"Da sau茩i" Afnan ta ba ta amsa, tare da tambayar Mama su Maryam basu dawo daga makaranta ba. Mama ta ce "Suna hanya ba su fara dawowa ba".
Inna Bilki ta dubi Afnan ta mi茩a mata kofin hannun ta ta ce "Kar蓳i ki shanye wannan abin". Duban kofin tayi, ta kalli Inna Bilki sarai ta gane meye amma sai ta ce "Inna wannan fa?"
"Maganine" ta ba ta amsa.
"To ai na ji dama, zazza蓳in ma ya sauka"
茒aure fuska Bilki tayi ta ce "Kar蓳i kisha ba na son gardama" ganin babu alamar wasa a fuskar ta, ya sa ta kar蓳i kofin tsikar jikinta na tashi ta kafa kofin ta shaye.
Ta na gama sha ta ji zuciyar ta na tashi, ya mutsa fuska ta fara yi. Inna Bilki ta ce "Kar ki yarda ki amayar da maganin nan, ko anjima sai kin kuma sha, sauran kuma sai dai ki tafi da su can, ki ci gaba da amfani dasu".
Kafin Afnan tayi magana Hajara ta shigo da sallama amsa mata suka yi, su na binta da kallo, Hajara ta ce "To gamu mun shigo ko ba a gayyace mu ba, mu ma a yi shirye shiryen tariyar da mu" ta maida duban ta ga Mama ta kuma cewa "Amina to barkanmu su Afnan dai an yi arzikin shiga daga ciki, duk da auren na ha蓷i ne, Allah ya nuna wa 拼an baya".
Bilki tayi caraf ta ce "Yawwa barka dai, ai ba ita za ki yi wa barka ba ni, domin ni ce uwar Afnan, yarinya kam tayi arziki babba, kin san ko a kai tallan ka kuma asamu wanda zai siya arziki ne, wasu ba na jin ko tallan su a ka kai za su samu masaya, dan abin rabo ne, kowa na son siyen abu mai inganci da kyaun kallo".
Hajara sakin baki tayi kamar garkar wawa, ta na bin Bilki da kallo. Da ga bisani ta ce "Bilki ina fatan dai ba magana ce ki ka fa蓷a mini ba?".
"Akan me zan fa蓷a miki magana Hahara? Amsa ce na baki dai-dai da maganar da ki ka yi".
Wani takaici ne ya 茩ular da Hajara, domin sarai ta gane magana Bilki ta ya蓳a mata, amma sai ta danne ta ce "Amina ba wani abin da za a yi ne? Kin san fa su mutanen 茩auye abin magana baya musu wuya. Duk da dai abin ya zo a bazata, gara a shirya 蓷an wani abin da za a kai ta da shi, saboda gudun barwa yaro abin fa蓷a".
Mama ta ce "Hajara ba abin da zan yi, wa拼anda suka ha蓷a auren su je suyi, idan kuma ba za suyi ba, sai a kai ta hakan, in ya so gidan mijin idan ba za su iya kar蓳arta a haka ba, sai a dawo mini da ita".
"Subhanallah Amina in jin dai ba baki ki ke yi wa auren ba? Ahh bai kamata ki na irin wa蓷annan maganganun ba gaskiya".
"Wai ke Hajara me ye naki a ciki ne, dama abin da ya kawo kenan? to ina ruwan ki, tayi wa auren baki sai ki je ki fa蓷a, dama aikin ki ne kin saba".
Ita ma Hajara cikin masifa ta hayayya茩owa Bilki "Wai Bilki ina ruwan ki da ni ne? Na sakaki a magana ta ne?".
"Eh kin sakata, ai ita ba munafuka ba ce, sannan ba ta son ganin 蓷an uwanta a damuwa, ita 蓷in ta 蓷auki damuwar 蓷an uwanta ta ta ce". Gaba 蓷aya suka juya duban su zuwa ga Maryam da shigowar ta kenan, ta ji Hajara na wannan maganar.
Hajara ta ce "Maryam ni ki ke gayawa magana haka? Saboda baki da kunya?"
"Eh na fa蓷a 蓷in uwata ce ke, ko dan kunga kwana biyu na 蓷aga muku 茩afa shi ne za a zo har inda muke a yi muna rashin kunya".
Mama ta ce "Ke Maryam ba na son na sake jin bakin ki a wurin nan".
"To Mama sai ta zo har...." "Ba na ce ki rufe mini bakin ki ba, maza zo ki wuce daga wurin nan".
Hajara ta ce "Korar me za ki yi mata? Ai duk abin da tayi dai-dai ne, tun farko idan ba a basu damar yin hakan ba ai ba za suyi ba".
Mama ta ce "Hajara ba na son tashin hankali, dan Allah idan har fitina ce ta shigo da ke wurin nan ki yi tafiyar ki". " Ai ko baki kore ni ba tafiya zan yi, dan ba zama zan yi ba, wato tunda ita wadda ta ha蓷a auren tafi 茩arfin ku shi ne kuka juye haushin ku a guna? To aure dai ne sai dai ku mutu, kuma 茩auye ne zuwa babu fashi".
"Ai wasu suna bi蓷ar ko na 茩auyen ya zo ya ce ya na son su basu samu ba, to Alhamdulillah ita 蓷in da har ta samu na 茩auyen, idan fitsari banza ne kaza tayi mu gani" Bilki ta bata amsa.
Haka dai suka yi baran baran kafin Hajara ta bar wurin.
Maryam zama tayi ta na 茩un茩uni, don ta ji haushin hana ta maganar da Mama tayi.
Afnan da tunda aka fara magana ko tari ba ta yi ba, sai yanzu ta ce "Mama wai tariyar me na ji ana magana ne?".
Mama ta ce "Hmmm Gwaggo ce ta ce lallai yau sai kin tare a 蓷akin ki..." Kafin Mama ta 茩arasa magana Maryam ta yi wata zabura ta ce "Bala'i amma wannan tsohuwar ba Allah a ranta. Allah ya kasheta kowa ma ya huta".
Mama ta ce "Ke Maryam ki na da hankali? Gwaggon ki ke yi wa fatan mutuwa? Kar ki manta ita ta haifi mahaifin ku, kar na sake jin wannan maganar a bakin ki, idan ba haka zan yi mugun za蓳a miki".
Kuka Afnan ta fashe da shi ta ce "Mama wallahi ba inda za ni, ko lafiya ba ni da, abari sai na warke tukuna".
"Ai Afnan sai dai ki yi ha茩uri, tunda har ta furta hakan, to wallahi babu wanda isa ya hanata". Cewar ina Bilki. Maryam kam ta cika tayi fam da ta na da iko, da ta la茩a蓷awa Gwaggo shegen duka ko sanyi ta jiya.
Rarrashin Afnan Bilki ta shiga yi, tare da bata ha茩uri, ta ce "Ki yi ha茩uri Afnan bawa baya wuce 茩addarar sa, duk abin da ya same shi da sanin Ubangiji, kin ga su Bahijja sun dawo daga makaranta, yanzu sai ta zo tayi miki 茩unshi".
Cikin kuka ta ce "A'a Inna ba na so, ni a barni a haka".
Sallama Baba ya yi ya shigo, amsa masa suka yi, suna gaishe shi, bai ida shigowa ba sai ga Gwaggo ta shigo babu sallama, sakamakon zuwan da Hajara tayi, ta fa蓷a mata 茩arya da gaskiya.
"Eh lallai Amina kin gawurta, wuyan ki ya yi kauri ya isa yanka, sa茩on ki ya same ni, to ina son ki sani, wallahi na rantse da girman Allah duk ki ka kashe auren nan, ke ma sai naki auren ya mutu, ke ma wannan A'isha 蓷in duk ki ka 茩i zama a gidan auren ki, to sai dai ki zauna a gidan nan ba tare da uwarki ba. Ke kuma 蓷ayar marar kunya na san maganin ki, sai kin gane baki da wayo, ina ji dai Umar 蓷ana ne ko? To bari ya dawo ki ga mai zai faru". Tayi maganar ta na nuna Bilki.
Da sauri Baba ya dubi ta ya ce " Subhanallah Gwaggo lafiya? Mai ya yi zafi haka".
"Tukuna saurara mini ban fara zuwa ta kan ka ba".
"Ke kuma jarababbiyar yarinya, da tayi gadon masifa can dangin uwarki, duk ki ka 茩ara yi wa Hajara rashin kunya to ba ita ki ka yi wa ba, uwarki da ubanki gasu nan su ki ka yi wa".
"Kai kuma na dawo gareka, ina son maza maza ka je kasuwa ka siyo mata katifar kwanciya, da filo, da zanin gado, ka ha蓷o mata da labulayen 蓷aki guda biyu, ni kuma nan ina da tukunya, da buta, da bokitin wanka. Hadda kwanukan cin abinci, Ina so yau 蓷in nan a sada ta da gidan mijinta, kuma yanzu nan, nake bu茩atar ka je kasuwa, ka kira 蓷an uwanka a waya ku ha蓷u ku je tare a siyo komai da ya kamata, sai ku bi蓷o mota a can. Tunda na ga uwarta ba ta da niyyar yin wani abin arziki".
Shiru Baba ya yi dan har cikin zuciyar shi ya ji babu da蓷in wannan abin da Gwaggo tayi.
"Ya na ji kayi shiru ne? Ko kaima gardamar za ka yi mini ne? To wallahi umarni ne na baka ba shawara ba, maza ka wuce yanzun nan, kar ku 蓳ata mini lokaci".
Jiki a sanyaye Baba ya amsa da "To Gwaggo"
Ta kuma duban su ta ce "Ke kuma sai ki tashi ki shirya, don ba na son a zo ana jira, kuma kin ji abin da na fa蓷a miki". Ta na gama fa蓷ar haka ta bar wurin.
Baba ya mi茩awa Mama maganin da ya zo wa Afnan da shi, sannan ya ce "Sai ta tashi ta shirya" da ga haka bai ko tsaya ba, ya juya ya fita.
Kuka Afnan take yi ba na wasa ba, Maryam ma kuka take, Mama kuwa 蓷aki ta shiga ta kasa fitowa sai tausayin 拼arta take ji, banda sharar 茩walla ba abin da take. Da 茩yar Bilki ta lalla蓳a Afnan ta tashi ta shiga wanka sai kuka take yi.
Gaba 蓷aya unguwa ta 蓷auki anyi wa Afnan auen sadaka a 茩auye, sakamakon kawu Sanusi da yake ta ya蓷a maganar a waje.
Sai yau Feena take samun labari, babu shiri ta zo gidan su Maryam, sai dai jikin ta ya yi san yi ganin Maryam 蓷in na kuka, ita ma kukan ta fara.
Gwaggo kuwa da kanta ta bi ma茩ota ta na sanar dasu batun auren Affan, sannan ta ce duk wanda ke samun zuwa ya shirya a je kai amarya da shi yanzu nan, sai dai a gidan Yayan ta ne za a kai ta, kafin mijinta ya ida gyara wurin da za a sakata. Mutane da son gulma nan fa suka ce za su je, sai dai wasu daga ciki mazan su ba su bar su ba, duba da tafiyar ta bazata ce.
Cikin abin da bai fi awa 蓷aya ba, su Baba suka kammala duk wani abu da Gwaggo ta ce, sannan suka bi蓷o babbar motar nan mai 蓷aukar mutum goma sha takwas.
A lokacin Afnan tayi wanka ta sanya doguwar rigar atamfa, da hijabinta, banda kuka ba abin da take, Mama ma kukan take yi, ta na mamakin wannan aure haka ace babu komai da ango kewa amarya, babu kayan lefe, sadaki gashi basu ganshi da idonsu ba.
A 茩ofar gidan motar ta tsaya a nan ciki suka bar kayan, suka shiga ciki, kai tsaye inda Gwaggo suka nufa, cikin murna ta fito da sauran kayan, ta mi茩awa Hajara, ta ce ta kai mota. Ita kuma ta nufi wurin su Mama.
Ta na zuwa ta ce "A fito da ita ga motar nan ta iso". Babbar Yayar Mama ta ce "Haba ai kya bari ta gama ganawa da uwarta"
"Wace irin ganawa kuma, bayan duk tsawon lokacin da suka yi tare, dan Allah ban son 蓳ata lokaci, ku fito da ita".
Afnan jin hakan ta 茩ara riri茩e Mama ta na kuka "Ta ce Mama dan Allah ka da ki bari a tafi da ni, Mamata ki yi mini addu'a".
Itama Mama cikin kuka ta ce "Afnan ki je Allah ya na tare dake, Allah ya baki ha茩uri da juriya a gidan auren ki, Ubangiji ya wanzar da kwanciyar hankali a cikin rayuwar auren ki".
Gwaggo ganin Afnan ta 茩i fitowa ya sa ta shiga 蓷akin da 茩arfi ta jawo Affan ta na kuka ta yi waje da ita, Inna Bilki da su Maryam da 茩awarta sai Bahijja da Aunty Murja yar Mama gaba 蓷aya suka mara mata baya. Haidar na gefe cikin napep 蓷in sa zuwansa kenan ya ga an fito da Afnan ta na gunjin kuka, an sakata a mota, su Maryam ma duk sun shiga motar da sauran mutanen da ke wurin.
Kawu Sanusi ne a gaban motar, Baba na tsaye ya na musu fatan sauka lafiya. Duk da 茩asan zuciyarsa wani irin zafi yake ji, bayan mutane sun gama shiga motar ta tashi Gwaggo na 蓷aga musu hannu har sai da mutar ta bacewa ganin ta, sannan ta kuma ciki.
A hankali Haidar ya sauke a jiyar zuciya ya ta da napep 蓷in sa ya bar wajan.
Amanar cool ce 鉁嶏笍
***