Free chapter 路 Read without an account

Page 2

by SaNaz deeyah 路 SUMAYYA

SUMAYYA

Wattpad@SaNazdeeyah_

Arewabooks@sanazty

KARAMCI WRITERS ASSOCIATION馃摎

[karamci tushen mu'amula tagari]

```Part 2```

"Sumayya a yanzu kuka ba naki bane, saboda abinda ke cikinki, da kuma samun mafita a kansa, ki bar kuka mu tsaya mu yi dogon tunani."

茒ago rinannun idanunta tayi ta sauke su akan Amarya tare da fa蓷in "Iyarmu, na gwammace ace fya蓷e aka min na kuma san anyi, ko kuma ace nice na bada kaina aka lalatani har ciki ya shiga da irin wannan abin. Iyarmu me zan fa蓷awa 蓷an cikina idan yazo duniya? Waye ubansa? Sannan kafin ma na kawo shi duniya me mutane za su fa蓷a a kaina da abinda ke cikina, na rasa wace irin 茩addara ce wannan?"

"Ya isa haka kar kiyi sa蓳o, duk wata 茩addara daga Allah take wala mai kyau ko marar kyau, Allah baya bacci Sumayya, kuma nayi imani dashi ne zai kawo mana mafita akan wannan."

"Iyarmu ki duba irin gwagwarmayar da aka sha akan Kamal, bana son shi na aure shi Iya, 'yan gidan nan har gani suke Baffa ya fi sona shiyasa ni ya samo min mai ku蓷i, aka yi ta zin蓷anmu, yanzu gashi auren babu inda yaje, 蓳ullowar wannan cikin ya saka Kamal sakina bayan ya gama wula茩antani tare da min gori da kuma kirana da munanan suna, nayi dana sanin auren shi dama ba son shi nake ba, umarnin Baffa kawai na bi."

"Sumayya ki sani shi aure rai ne dashi, duk lokacin daya 茩are dole ya mutu, ki manta komai ki shiga sabuwar rayuwa, kar damuwar nan ta saka miki wani ciwon da za azo ana dana sani"

"Dana sani ai nayi shi ya fi a 茩irga"

"Kuma kin san haramun ne, kar蓳i kisha fura kafin a gama abinci na san baki ci komai ba."

**** **** ****

Safa da marwa kawai yake a 蓷akin ya kasa zama sam. Mommy da ta shigo hannunta ri茩e da glass cup ta kalleshi "Dan Allah ka yi ha茩uri ka sakawa zuciyarka salama"

Kallonta ya yi tare da sauke ajiyar zuciya kafin ya zauna kan sofa. Itama kusa dashi ta zauna tana mi茩a masa abin sha tana fa蓷in "Zo蓳o ne mai sanyi nayi maka, yaji kayan itatuwa, na san za ka ji da蓷insa."

Kar蓳a ya yi ya kur蓳i ka蓷an, sannan ya kalleta ya ce "Har yanzu abin nan 蓷aure min kai yake"

"Ba fa abin mamaki bane Alhaji, duk abinda aka ce yaran yanzu za suyi to wallahi kar kayi mamakin komai"

"Na yi wa Kamal aure ne dan ya nutsu to itama matar ba nutsatstsiya ba, to wai 蓷iyar waye nutsatstsua tunda ba a samu a 蓷iyar Malam ba?"

Shiru ta yi kafin ta ce "Kar fa ka manta kirarin da ake yiwa 'ya'yan Malam 蓷in, 蓷an malam ka茩i halin Malam, Malam na masallaci kai kana gidan 'yan bori, ai Alhaji ni dama tun ranar dana ga yarinyar naga kamar idanunta a tsaytsaye suke"

"Ban yi tunanin haka daga gurin iyalan Malam Bala ba, mutum ne da ake kwatance dashi wurin ibada da kuma tarbiyya ga ahalinsa, dan hatta almajiransa sun bambanta da sauran almajirai."

"To dama ai dole a cikin 'ya'ya sai an samu zakka, kaima a naka ba ga Kamal 蓷in ba, amma duk laifin ka ne, domin yarinyar nan sam bata dace dashi ba, da ka bari na aura masa 蓷iyar Haj Mariya wallahi na tabbatar sai ta saisaita tunaninsa."

"To ni dai for now bani da abin cewa har sai na huce akan abinda ya faru."

****** ***** ******

"Saki?"

"Of course yes saki, mene na fa蓷a a tashin hankali kamar wata 'yarka"

"No ba haka bane Yaya, kawai ban ji da蓷i bane da yaushe aka yi bikin naka muna ta murna, ni ba茩in cikina ma ban ta蓳a ganin matar ba kuma ace wai har anyi saki"

"Ganinta ai ba abu bane da zai maka wahala zan iya kai ka gidansu idan ka dawo sai ka ganta tunda akwai amfanin da hakan zai maka"

"No! Ni fa ba wani abu zai min ba, calm down please don't be offended"

Murmushi ya yi yana fa蓷in "Lallai da alama kayi hankali, kai da baka bayar da ha茩uri yau kaine da ba da ha茩uri"

"So nima fa Yaya na girma, dan tuni na samu matar aure"

"Wow am so excited 'yar waye?"

"To ka san dai ba zan yi za蓳en da bai dace ba, to na za蓳o mace mai ilmi da kuma aji"

"Oh abin har da 'yar gori"

"No ba haka ba, kawai dai ni ba zan yarda ayi min irin abinda aka maka ba, auren dole fa, haba ai tuni aka daina yayin nan"

Nihal da ta fito daga kitchen zama tayi tana fa蓷in "Yauwa bro dan Allah ka fitar damu outing"

"Lallai ma yarinyar nan" Ya furta yana kallonta.

"Nihal ce wai na fitar dasu outing, seems like ni bani da aikin yi ko kuma na zama driver 蓷insu ne, kaga let's talk later, bye!" Ya yi hanging wayar yana kallon Nihal.

"Kin san Allah nima akwai inda zan je, dan haka babu inda zan kaiku kima sani"

Ayrah da ta fito a lokacin turus tayi, dan a shirye ta fito tana tunanin zai kaisu kamar yadda Nihal ta fa蓷a mata.

"Yaya dan Allah har mun shir..."

"Ke ba zan kaiku ko ina ba na fa蓷a muku" Yana gama maganar ya 蓷auki key 蓷in motarsa ya fice.

"Tofah! Tunda ya saki matarsa ya zama masifaffe fa" Ayrah ta fa蓷a tana zama.

"Dama haka yake ba wani wanda ya canja sa."

Yana driving ya kira number Laila, ta 蓷aga tare da fa蓷in "Babe naji ka shiru"

"Sorry ban san ma time ya tafi haka ba"

"Ina fata dai ba tunanin tsohuwar matarka ne ya sa ka manta da al茩awarinmu ba"

"Tunaninta kuma? Macen da tayi cikin shege a gidan aurenta, Haba Laila ki daina wannan maganar ma"

"Anyway ni dai na shirya kai kawai nake jira"

"Am on my way, nima ai na matsu mu ha蓷un"

murmushi kawai tayi ta kashe wayar.

Driving ya cigaba da yi yana sauraren wa茩o茩insa masu da蓷i na turanci wa茩o茩in Ayra star. A bakin layinsu dake cikin lami蓷o crescent ya tsaya sannan ya kirata "Ina jiranki a bakin layi"

"Na yi tunanin za ka 茩araso ku gaisa dasu Mom"

"Yanzu ai ba a kamal nazo ba, fita fa zamuyi kuma zamu da蓷e bamu dawo ba, so kike su hanani aurenki su ce nine ke 蓳ata ki"

"Ai babu wanda ya san ina wannan harkar kuma har nayi aure ba wanda zai sani, saboda kai ka蓷ai nake kulawa"

"Babe ina jiranki" Ya yanke kiran.

Bai 蓷auki tsawon mintuna da yawa ba sai gashi ta bu蓷e motar ta shiga. "Babe ina fatan dai ban 蓳ata maka lokaci ba"

"Never mind" Ya furta yana mata peck a kumatu"

"Baby sarkin zumu蓷i ina muka nufa yanzu?"

"Gidana"

"Akwai kayan chaji dai ko?"

"Duk abinda kike bu茩ata an tanada."

Kai tsaye can ya nufa, a farfajiyar gidan ya parker mota ta fito tana 茩ara 茩arewa gidan kallo, shi kuma ya 茩arasa ya rufe gate.

"Shiyasa na茩i yarda na ajje maigadi dan bana son sa ido"

"Hakan ma yana da kyau, dan masu gadi a yanzu munafukai ne, amma kuma bu蓷e gate baya maka wuya?"

Sa蓳arta ya yi, 蓷aukar jarirai ya nufi ciki yana fa蓷in indai ina tare dake Laila ba zai min wuya ba"

"Kamal...!" Ta furta da wata iriyar murya, shi kuma sai daya direta a saman bed sannan ya tsaya yana 茩o茩arin cire kayan jikinshi.

Mi茩ewa tayi zaune tana kallon 蓷akin "Anan ake cin amanata ko?"

Murmushi ya yi lokacin da yake zare belt 蓷in trouser 蓷insa yana fa蓷in "Ai babu wanda ya isa ya sa naci amanarki, tunda na auri Sumayya har muka rabu ban ta蓳a ri茩e ko da yatsarta ba"

"Kai Babe fa蓷i gaskiya"

"Gaskiyar kenan" Ya furta yana hayewa kan gadon.

"Nayi tunanin sai mun fara chaji"

"Nafi so mu fara cikin hayyacinmu, ai yau muna tare har 10 na dare"

Ya fa蓷a yana 茩o茩arin zage zip 蓷in rigarta.

***** ***** *****

"Sumayya! Sumayya!! Sumayya!!!" Amarya ta furta tana jijjigata, sai dai gani take tana ta wani abu kamar mai farfa蓷iya. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, mene ke damunki Sumayya?" Da sauri ta mi茩e tare da fita tsakar gidan, ganin za tayi hanyar waje ya saka Hadiza fa蓷in "Lafiya kuwa? Za ki fita babu ko mayafi bayan kin san yamma ce Malam na karatu da almajirai a 茩ofar gida"

"Sumayya ce take wani abu kamar bata cikin hayyacinta" Ta furta a ki蓷ime.

"To kuma shi ne hakan zai saka ki fita a yadda kike, ke ko irin karar nan ta 'ya'yan fari baki yi" Cewar Inna Dije da ta fito daga 蓷akinta.

"Yo ina za tayi ai babu kunya a 蓷iyar bahaushe" Hadiza ta amshe da fa蓷in haka.

"A'a Hadiza kar kuma ki zagi Hausawa dan hausawan ma ai kala-kala ne ni dai ina da kunya"

Ita dai Amarya da sauri ta koma ciki, dan yaran gidan duk basu nan suna waje tare da Malam. Kallon Sumayya tayi wanda tana kwance kamar gawa sai dai kuma a yanzu babu wannan jijjigar da take. Da sauri ta zari hijab ta fice.

"Ita kuma wannan ina za taje?"Cewar Iya Zulai da ta fito daga bayi.

"Wa ya sani mata"

Da sauri Zulai ta tare 茩ofar tare da fa蓷in "Babu inda za kije muddin ba karatu aka gama ba"

"Wallahi ke baki isa kin hanani fita ba, dan kun ga ina 茩yaleku to a wannan ga蓳ar ba zan yarda ba"

"Mene ba za ki yarda ba? Irin tarbiyyar taki ce fa 'yarki ta 蓷auka, a garin yawan kwalta har da ribar ciki ta samu"

"Kul Hadiza, ina ganin mutuncinki"

"To ki daina gani mana ki ga in abin zai dameni, an fa蓷a yawan dandi take shiyasa ma a baya ta kasa auruwa, yaro yazo aka yi masa rufa-rufa ya gano ya sako 'yar banza"

"Waye banza ni ko ita?"

Jin maganar Malam ya saka suka kalli gurin gaba蓷aya. Hadiza ta 蓷an sosa kai, ita kuwa Inna Dije da sauri ta fara tattare kaya kamar mai gyara tsakar gidan.

"Tun daga waje nake jiyo hayaniyarku ina karatu, wai meyasa ba zaku ta蓳a zaman lafiya ba?"

"Malam zaman lafiya fa baka so ayi shi ba, dan babu yadda za ai ka fifita 'ya'yan Amarya kayi tunanin zaman lafiya, ko dan ai ga 茩arshen sangarta mun gani" Cewar Iya Zulai.

"Ke Zulai ki kiyayeni, kibar ganin muna da tarin 'ya'ya da jikoki dake kiyi tunanin ba zan iya hukuntaki ba, ba zan lamunci cin kashi ba"

"Tunda an ta蓳o matar so ai zaka ce haka, a kaf tarihin gidan nan duk yawan 'ya'yanka ba a ta蓳a samun wanda ya 蓷auko abin kunya ba sai a tsatson Amarya, ta ja maka zagi har mu kishiyoyinta bamu tsira ba" Tana gama fa蓷a ta wuce rai a 蓳ace.

"Amarya lafiya?"

"Malam Sumayya ce ke wani irin abu"

"Tana ina?"

"Tana 蓷aki" Da sauri suka nufi 蓷akin, ya ta蓳ata yaga tana numfashi amma kuma ba bacci take ba. Addu'o'i ya yi sosai a ruwa ya bayar aka bata sannan ya ce Amarya ta shafa mata a jiki. Sai da ta gama sannan suka ga kuma ta bu蓷e ido, sai kuma kuka.

"Sumayya kiyi ha茩uri babu wanda yafi karfin 茩addara, na gamsu da bayanan da kika mana akan cikin nan, kuma muna ta addu'a koma waye uban yaron zai bayyana da iznin Allah, kiyi ha茩uri kin ji"

Shiru amarya tayi kafin ta ce "Malam ina da shawara idan ba zaka damu ba"

"To ina jin ki"

"Malam nace me zai hana na kai Sumayya can Katsina gidan 茩anwata ta haihu acan, ina ganin kamar hakan zai fi mata samun sau茩in abin, tunda ka ga acan babu wanda ma zai mata sababi bare har taji ciwon abin"

"To shawarar ki akan Sumayya abu ne mai kyau, amma kuma gaskiya bana so taje gurin danginki, dan abu idan aka ce dangi zai zama magana, amma dai zan yi magana da Yayanta taje can legas har zuwa ta haihu"

"Legas kuma Malam"

"Eh nan dai nake ganin sai yafi ai"

"Sai naga kamar in Legas ne ta mana nisa"

"To inda aure ne ya kai ta nan ace me? Hakan dai za ayi dan shi ne kawai mafita a garemu da ita baki 蓷aya, in ta haihu sai ta dawo"

Shiru Amarya tayi duk da bata so amma kuma babu yadda za ai tayi masa musu tunda ita ta fara kawo shawarar, kuma tana so Sumayya ta 蓷an manta wasu abubuwan, ta san muddin tana wannan gidan ba zata manta ba.

Bayan Kwana Biyu

Tana kwance akan gadon Amarya, hannunta ri茩e da carbi tana ja, sai hawaye da ya yi mata dafifi, dan in dai idanunta biyu sai tayi hawaye, shiyasa kullum idanunta ja suke, kasancewarta fara sol, yanzu kuma kullum cikin kuka take ya saka fuskarta ta 蓷an yi ja.

Ji tayi an dafa ta, ta 蓷ago kai a hankali.

"Sumayya wai sai yaushe hawayen ki zai bar zuba? Ko so kike sai kin saka wa kanki wani ciwo?"

"Iyarmu..." Sai kuma ta kasa 茩arasa fa蓷ar saboda yadda kuka ke 茩o茩arin kubce mata. "Mu rungume 茩addararmu Sumayya" Ta fa蓷a tana goge mata hawaye.

"Ki kwantar da hankalinki dan Allah"

"Iyarmu dana fita gori suke min"

"Ki bar su ai Allah baya bacci, ki manta komai kin kusa bar musu gidan ma gaba蓷aya."

"Ina zan je?" Ta tambaya da dasashshiyar murya.

"Babanku ya ce zai yi magana da Saminu za ki je can gidansa ki 茩arasa idda sannan kuma ki haihu acan"

"A'a Iyarmu ba zan iya tafiya mai nisa na barku ba" Ta furta tana hawaye.

"Sumayya dole ce ta saka, wannan ita ka蓷ai ce hanyar da za a bi wajen ganin an magance damuwarki, bamu so wani ciwo ya riske ki"

Hannu ta saka tana goge mata sabbin hawayen da suka fara zubo mata.

Sallamar Maryam ce ta dakatar da Amarya, ta amsa mata sannan ta shigo.

"Iya ina wuni"

"Lafiya lau Maryam ya maigidan naki da yara"

"Duk lafiya"

Zama tayi kusa da Sumayya tana fa蓷in "Jiya fa sai dana miki nasiha wato ba za ki bar kukan nan ba ko"

"Wata茩ila taji naki maganar amma ni ta茩i jin tawa" Amarya ta fa蓷a tana mi茩ewa "Tunda kin shigo bari in fita in 茩arasa aiki"

"Laaa Iya bari nazo na kama miki"

"Haba kisha zamanki Maryam, gata nan ki rarrasheta"

"Atika bata nan?"

"Suna can islamiyya hadda ake yanzu"

"Masha Allah, Allah ya taimaka"

"Amin."

Amarya na fita Maryam ta kalli Sumayya "Ya kamata ki daina kukan nan, dan ba shi ne mafita ba"

"Maryam ba za ki gane, har yanzu ina tunani akan wanda ya yi min ciki, cikin jikina ya zubar da martabar gidan nan, duk sauran da suke da tarbiyya yanzu duk zaginmu ake, Maryam wai ba ayi min fya蓷e ba sai da nayi aure, auren dama 蓷an 蓷osane nake saboda Kamal sam baya 茩aunata to kuma ga wannan abin daya faru"

"Gaskiya akwai 蓷aure kai abin, taya haka ta faru? Amma ko a musulunci fa 蓷a na mijinki ne"

"Taya? Bamu ta蓳a ha蓷a shimfi蓷a ba tunda muka yi aure"

"To waye zai shigo ya miki fya蓷e? Cikin aljani dai ba zai bayyana a jikinki ba"

"Shiyasa mutane da dama gani suke 茩arya na fa蓷a, ni nayi iskanci na samu ciki, Maryam wallahi ko 茩arfe 蓷aya na dare Kamal zai kai bai dawo ba bana ta蓳a kwanciya idan bai dawo ba, saboda ni tsoro ma nake duk da ana barin wuta, tunda aka kaini ban ta蓳a ganin an 蓷auke wuta ba. Akwai ranar da sai asuba ya dawo wallahi haka na kwana zaune. Kuma ko ya dawo sai na rufe 蓷akina da mukulli nake bacci"

"Cab, dama mai fitar dake sai Allah, tunda yana fita yawonsa haka zai ce in ya fita kema fita kike"

Hannu ta saka ta goge hawaye.

"Gaskiya dole akwai ranar da aka samu wani ya shigo baki sani ba ya gusar miki da hankali tare da amfani dake."

Kai ta girgiza tare da fa蓷in "Ni dai na san haka bata ta蓳a faruwa dani ba, dan yawanci ma baccin rana ne ban rufe 蓷aki kuma shima sai na tabbatar yana nan nake baccin saboda tsoro, sannan ba shigowa 蓷akina yake ba kuma kin san dai bani da nauyin bacci."

"Yanzu dai mene mafita?"

"Maryam na fi so cikin nan ya zube ko na samu salama, amma bana so kowa ya sani dan na san ba za a barni ba"

"Kin san ana cin ku蓷i wajen zubar da ciki"

"Ina tunanin akwai dubu ashirin a gurina"

"To yanzu ki shirya gobe muje asibiti"

"Gaskiya ba gobe ba, kin san kafin na fita wani aiki ne, amma ranar juma'a Baffa da wuri yake fita sai muje"

"To shi kenan Allah ya kaimu"

"Amin ya rabbi"

Sumayya ta 蓷an samu sau茩i sosai ganin sun samowa kansu mafita.

#Share fi sabilillah

SaNaz_deeyah馃尭

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.