Free chapter · Read without an account
Unspoken
by ZAHRAA · Zumar Hamada 🍯 🏜️
Zumar Hamada
Page 19
Tun bayan daren nan a club…Nawaf bai sake zuwa ba, ba saboda aiki ya yi yawa ba, kuma ba saboda ya manta da ita ba ,Sai dai duk lokacin da ya yi niyyar fita sai fuskar Farida ta faɗo masa Baya son sata a ransa it’s not healthy Gara ya nisance ta shine mafi alkairi ,sau biyu yana ɗauki key ɗin mota da niyyar fita Sai ya fasa
Gashi Ramadan ya shigo no more club Sai dai abin mamaki…Duk lokacin da ya yi shiru, sai ya tuna murmushinta
Tuno Kalamanta yayi Murmushi yana maka kyau sosai… kamar na ɗauki picture
ƙaramin murmushi ya Saki yana girgiza kai
Nadira ta lura mijinta ya fi zama a gida a kwanakin nan , ta gane cewa barazana ko Hauka bazai taba canza Nawaf ba ,dan Bayan zagin da ta masa a waya sai da tayi kwana 4 bata gansa ba yaki dawowa gidan .
sai da tayi blackmailing dinsa da Ayla kana ya dawo
Sai gashi idan tayi girki yana ci ,har amsa hirar ta yake time to time ,kawai ta fara samun wani sabon fata ko dai…Mijinta ya dawo gare ta?ganin haka ita ma ta sake dagewa, ta Kara kula da shi ,ta fara magana cikin natsuwa
Bayan an sha ruwa ta same shi a balcony Ta miƙa masa cup na coffee ,Na yi maka ba sugar sosai Na san haka kake so
Ya ɗaga kai Ya kalle ta ya karɓa ,Thank you nadira ,Kalmar ta yi mata daɗi fiye da yadda ya zata Saboda shekarun nan…Har “thank you” ɗin ma ya yi mata wuya ta ji daga gare shi
Bayan kwana biyu…Nadira ta same shi ɗakinsa yana ta aiki a laptop ,ta zauna kusa dashi ,Uhmm Zauji na biya mana Umrah
Oh nice Allah ya kaiku lafiya ,ta dan yi jim kadan kana tace ba fa iya ni da Ayla ba ne harda Kai ,Allah kaimu Sannu da kokari
Nadira ta zaro ido Da gaske?zaka ?Wani irin farin ciki ya mamaye zuciyarta,kiss ta manna masa ta goshi ,nawaf ya runtsa ido
Bari na fara hada mana kaya ta fice zuwa dakin ta cikin murna,Tana fita ya dauki waya ya mata transfer din kudin umrar data kashe
Shiru ya ratsa tsakaninsu Khalifa ya kalli wayar da ke hannun mahaifinsa Sannan ya sake kallon fuskarsa Everything okay, Dad?Eh. Komai lafiya ya fada yana dan kawar da fuskar sa gefe ,Khalifa ya jinjina kai
Amma bai motsa daga inda yake ba
Daddy ya lura da wani Kallo da khalifa ke masa ,ya dan daure fuska me ya kawo ka nan?khalifa ya ɗan yi murmushi ,na fito ne Shan iska sai na tarar kana waya
Daddy ya zuba masa ido ya kasa magana
Tadala ce ko?muryar Kalifa ta katse shirun
Wani abu ya motsa a fuskar Daddy yayi sauri ya danne shi
Eh Ita ce
Khalifa ya jinjina kai Ta ce tana Jin tsoro ne ?
Daddy bai ce komai ba A lokacin ne ya tabbatar Yaron nan Ya ji komai
Daddy Gidanmu yana da girma sosai Ni ma da farko ina tsoron zama ni kaɗai a ciki ,Poor girl har yanzu dady be tanka ba to me zai ce ?
Dad…
Na’am?Kana kula da Tadala sosai
Sabida Baƙuwarmu ce khalifa shiyasa
Is that all? Daddy ya zuba masa ido Kamar mai son karanta Abu a fuskar dan nasa
Khalifa ya ɗaga hannuwansa kaɗan
Okay… okay na dame ka questions mu koma ciki
suka fara tafiya jikin dady a sanyaye daf da zasu shiga khalifa ya koma juyo wa by the way…I don’t think she’s an outsider yar gida ce itama ya shige Cikin restaurant din
Alhaji Kamal ya tsaya a wurin Idanunsa suna kan bayan ɗansa A karon farko Ya ji kamar wani ya kama shi da wani sirri da bai ma san yana ƙoƙarin ɓoyewa ba
Ramadan ya yi nisa Yanzu sun kai kusan azumi ashirin da ɗaya Gaba ɗaya mansion din Gidadon Katsina ya canza Hayaniyar gidan ta ragu, kowa ya dukufa da ibada
A ɓangaren Tadala kuwa, rayuwa ta ɗan yi mata sauƙi. Makaranta ta tsaya saboda hutun semester, kuma tana samun damar yin karatu da ibada cikin natsuwa
A wannan ranar, tana zaune a ɗakinta tana karanta Al-Qur’ani wayarta ta yi ƙara
Anty Zaheera ce ,cikin zumudi ta daga Assalamu alaikum, Anty ina yini,
Wa alaikumus salam folawar mu Mi kike yi ne?ba komai fa Ina zaune ne kawai
To, ki shirya Yau a gidana zakiyi buɗa-baki
Na Kira sadiya na fada mata ,Wayyo Antyna Nagode can’t wait to see you
Bayan ta kashe wayar, wani irin farin ciki ya mamaye zuciyarta Ta dade ba ta fita ko’ina ba tana shirin tafiya Sadiya ta shigo ɗakin
Kin shirya ne? Eh Mami Sadiya ta jinjina kai.
To, ki gaishe ta.
daddy ma ya fadawa matan sa,zaheera ta gayyace shi bude baki dama duk shekara tana gayyatar dady ,shiyasa ma da suka ga tadala ma tafi basu kawo komai ba
Tana isa gidan ganin falon ba kowa kai tsaye ta nufi sama main bedroom din zaheera ,zaheeran ta rungume tadala
“na yi missing ɗinki fulawar mu ,Tadala ta yi dariya Ni ma haka Antyna
By the way, Kamal ma zai zo buɗa-baki nan
Tadala ta ɗago kai da sauri Daddy?”
Eh mana gani nayi kuna bukatar zantawa
Daga nan dakin mardiya ta Nufa Wajan azahar Kitchen suka shiga gaba dayansu inda aka shirya Kayan Shan ruwa
Suna gamawa duk suka shige daki dan Watsa ruwa Sabida saukin gajiya
Horn sukaji ,Zaheera ta yi murmushi Ga twin brother ɗina nan gandoki bazai Bari ma magrib tayi ba
Ba da jimawa ba ya shigo Sanye yake da farar shadda,hularsa a hannunsa
Ya fara gaishe da Zaheera idanunsa suka sauka kan Tadala Tsaye Sanye da abaya mai launin ruwan kasa
Mi…dahlia ba magana ?
Ta yi murmushi ina yini Daddy?Lafiya Lou babyna ya ibada ?Zaheera ta bi su da kallo
Na ware muku waje Ni zan kawo muku abin buɗa-baki da kaina kuma gaskiya alhaji kamal ka rage tsaurin ido a gaban nawa ?
Daddy ya dafe kai ,Kina da matsala twin
Ba wata matsala nida ja fulawar ka ku wuce guest parlor Kafin yara su shigo
Guest palour …
Shiru ne ya ɗan mamaye falon kasan carpet Tadala ta zauna Azumi nawa kika sha?ta jiyo Muryarsa a gefenta ,ban sha ko daya ba ta amsa cikin kunya ,Uhmm ban yarda ba mi dahlia ,yanzu that aside ya naga kin rame ?
Azumi ne Dama kam dan ramewa amma Bayan sallah Zan dan ciko zaiyi magana kenan aka Kira sallah ,dabino ya Mika mata ta dauki daya tare da Adduar bude baki Shima yayi daga nan ya nufi main falo dan tafiya masjid dasu junior ,itama daki ta nufa tayi alwala ,mardiya na kwance Wai period dinta yazo cikin ta na ciwo ,brush tadala tayi ta koma guest falon ,har ya dawo ya fara zuba abinci ,a plate daya serving dinsu A wannan lokacin…baya tuna komai daga shi sai mi dahliar sa daf da zaa Kira isha ya miƙe To, zan tafi mi dahlia zaheera tace kwana zakiyi Muje ki raka ni suka jera suna tafiya Chan kuma ya juyo
Mi dahlia …
Na’am?
Za ki iya haɗa ni da iyayenki?
Ta zaro ido Papa da Uma?
Eh su
Gabanta ya faɗi Lalle…Da gaske yake Ba wasa yake yi ba suka karasa harabar gidan
Hannu na rawa Tadala ta Kira Moussa Bayan Sun gaisa da Yaren su ta fadawa moussa zasu gaisa da mijin Anty sadiya …Ta ba Daddy wayar
Assalamu alaikum Moussa ya amsa da sauri jin dawa yake waya Daga nan aka haɗa shi da papa da uma Daddy ya yi musu barka da shan ruwa Ya yi musu gaisuwa cikin girmamawa suka dinga mamakin rashin girman kan sa
Kafin su rabu, ya ce
Moussa Zan amsa number yanzu ,ka turo mini account number ɗinka A saya wa autanmu lemo
Autanmu ? Kalmar ta bugi zuciyar Tadala ,har zata raka shi parking lot yace ta koma
Tana shiga falon taga zaheera ta baje kaya ,zo nan fulawar mu
Ga sako daga twin Wai Kayan sallar kine
Anty?
Zaheera ta yi murmushi bude su mana
Lace uku , Super uku Bazin uku,Designer shoes Matching veils ,Anty…Duk nawa ne ?
Buɗe ƙaramin box ɗin ki gani mana
Tana buɗewa taga Gold set Yan kunne da Sarka
Ta buɗe baki ta kasa magana Nan take…Maganar Farida ta dawo mata
An ce a Gidadon Katsina, kullum cikin sayen wa matansa gold yake…
Ta sake kallon kallon Kayan A’a, Anty Kayan sun yi yawa Wallahi sun yi yawa Ina Zan kaisu ?Ta ɗauki ɗaya daga cikin laces ɗin
Wannan kaɗai ma ya isa
Mi Dahlia, ai ba ki ga komai ba Indai kamal ne Tadala ta zaro ido Ban ga komai ba?a hakan ? Gobe ma za a kai miki dinki zaheera ta canza hirar dan ta Lura har yanzu Tadala bata San waye gidadon katsina a dukiya ba
Tadala ta zuba mata ido kamar wacce aka yi wa sabon harshe
Anty…Dan Allah a rage Kinga ….Zaheera ta katse ta ,ki bar maganar nace
Jiki a sanyaye Tadala ta jinjina kai To Anty
Ki gode wa Allah kawai
Tadala ta sauke numfashi.
Toh Anty Allah ya karawa daddy budi
Ameen ya Allah ,tatttara ki kai daki haka ta fara tattara Kayan Ta kasa yarda cewa duk wannan nata ne.
Ta shiga guest room ɗin da ta saba sauka idan ta zo gidan ,ta zauna a bakin gado, wayarta ta yi ƙara Moussa.
Yaya Moussa
Tadala!
Na’am.
Ke, kin san nawa mijin Sadiya ya turo min?
Ta ɗan yi shiru A’a.”
Million biyu fa
Tadala ta miƙe zaune
Me?
Million biyu fa! Wallahi, million biyu cif!
Moussa ya ci gaba da magana cikin farin ciki ,Wallahi wannan mutumi ɗan aljanna ne! Yanzu zan kira Sadiya na yi mata godiya
Da sauri Tadala ta ce,A’a! Yaya, don Allah kar ka kira ta Moussa ya yi shiru Kar na kira ta?Eh Saboda me?Bata san da ya bayar ba.”
Kamar ya ?Don Allah kawai, kar ku mata maganar.
Ashe Wayar a speaker take Can ta ji muryar Uma Moussa, bani wayar
Tadala?Na’am, Uma.”
An ina kuka haɗu da Alhaji Kamal har ya ce ki haɗa shi da mu?
Uhmm…”Dama ….Na je gidan yar uwarsa ne… Anty Zaheera, wacce nake baki labarinta Shi ma ya zo ,a nan muka haɗu
To, idan haka ne, me ya sa kika ce kar a yi wa Sadiya godiya?
Da sauri Tadala ta ce,A’a Uma… ai Mami ba ta son Alhaji yana yawan kyauta ne Shi ya sa yake yi a boye Ta faɗi cikin rawar murya.
Ba ta san dalilin da ya sa ta yi ƙaryar ba.
Sai dai…Ta ji ba za ta iya bayyana musu gaskiyar lamarin ba Can Uma ta sauke numfashi Allah ya saka masa da alheri.”
Moussa, ka Ka ba Fiza wani abu daga cikin kuɗin nan Tunda mijinta har yanzu ba wani ci gaba ya samu a rayuwa ba
To Uma Kuma ku yi wa Alhaji Kamal addu’a. Allah Ya ƙara masa arziki da lafiya.
Tadala ta lumshe Idonta
Amin.
Bayan ta kashe wayar Ta zauna shiru.
Idanunta suka sauka kan ledodin kayan da ke gaban ta
ta tuna kalmar da Daddy ya faɗa dazu saya wa autanmu lemo
Ta dafe ƙirjinta a hankali A karon farko…
Ta fara jin tsoron yadda wannan mutumin yake kula da ita. 💔
A can waje…Daddy ya fito zai shiga mota kawai ya yi karo da mutum
khalifa ne Tsaye Hannayensa cikin aljihun wando Yana kallonsa
Gaban Daddy ya faɗi
Khalifa? Me ka zo yi nan? Khalifa ya yi shiru na ɗan lokaci Na zo ne in ƙara tabbatar da abin da nake zargi.
Daddy ya ɗan tsuke fuska me kake nufi?Khalifa ya kalli gidan Sannan ya sake kallon mahaifinsa.
Daddy… did You really love her this much.”
Ko motsi Daddy bai yi ba
Khalifa ya ci gaba
Na ga fuskarka yau ,Na ga yadda ka ke kallonta ,Na ga yadda ka ke farin ciki idan tana magana Wallahi, Dad… ban taɓa ganin ka haka ba ,Lokaci ya yi kamar ya tsaya
Alhaji Kamal ya zuba wa ɗansa ido
Domin a karon farko…Wani ya furta abin da shi kansa yake tsoron furta wa