Free chapter 路 Read without an account

Chapter 4

by Sayyada barrister 路 BIYU A 茒AYA

BIYU A 茒AYA 


***
  YOTA 13 
Team of FIVE INK legends 

Dedicated to you my Apple 馃崕 Na'ima SARAUTA 馃懜馃徎

Page 4


          GHANA 

Ta iso gida cikin tashin hankali, da 茩yar ta kawo kanta gida, shiru farfajiyar gidan nasu babu kowa, duk suna cikin 蓷akunansu ta wuce 蓳angarensu ta turo 茩ofar ta shiga bakinta 蓷auke da sallama, ta ajiye jakarta a madaidaicin palourn su da babu komai a ciki sai shimfi蓷a蓷蓷iyar leda carpet, ta zauna tana sauke numfashi tare da jinginawa jikin garu, ta runtse idanunta, tana sake tunawa da abin da Alaja ta fa蓷a mata a restaurant da kuma abin da yake 茩o茩arin faruwa da ita...

"Kin dawo"

Ta 蓷ago da idanunta da suka sauya kala ta kalli mahaifiyarta dake tsaye ta ce

"Eh Mama"

"Ya kika dawo da wuri? Ina Majada da Jummai da kuma Alaja?"

"Mama na gaji ba zan sake zuwa restaurant ba, na daina wannan aikin"

Samun wajen zama Mamanta tayi, cike da mamaki take duban Bilqees ta ce

"Bisa wane dalili?"

"Mama kawai bana son aiki"

"Bilkisu kenan, yanzu har kin yi girman da za ki za蓳a wa kan ki rayuwa? har kin kai lokacin da za ki dinga jayayya da mahaifiyarki? To ki sani wannan aikin shine rayuwar mu, in ki ka bari to kin kuwa kashe mu"

"Zan nemi wani aikin Mama wannan aikin na Alaja bai dace damu ba, da kuma rayuwar mu"

"Bilkisu!"

Mamarta ta daka mata tsawa tare da kiran sunanta, duk da bata jin da蓷in jikinta amma ta sami 茩arfin halin yin magana cikin 蓷aga murya 

"Alaja da kike gani ita ce silar da kike takama dashi, ita ce ta tsaya tsayin daka ta baki rayuwa me kyau, au yanzu shine za ki ja da ita, lallai Bilkisu wuyar ki ta isa yanka"

"Mama tun dana taso nake yiwa Alaja biyayya, nasan tana 茩o茩ari sosai akan inganta rayuwata, to me yasa zata tura ni hotel wajen namiji"

Ras gaban Mamanta ya bada, tasan wannan ba 茩aramin aikin Alaja bane, to ta manta alkawarin da ta 蓷aukar mata ne? ko kuma akan maganar da su kayi ne yasa take 茩o茩arin yin hakan? Amma mamarta ta dake tare da cewa 

"Kul kada na sake jin wannan maganar a bakin ki, kuma aiki yanzu kika fara"

Mi茩ewa Bilqees tayi ta 蓷auro alwala saboda gabatar da sallah la'asar, tana alwala tana tunanin zuci, wai shin me yasa Mama take tsoron Alaja ne? Shin wacce iriyar ala茩a ne dake sakanin Mama da Alaja? Ya aka yi ma mamanta ta dam茩a amanarta a hannun Alaja....

"Omoo see fine girl"

Taji murya daga gefenta kuma ta shaida muryar.
Ko kallonsa bata yi ba, ta san daga 蓷akin da ya fito don haka tana idar da alwala ta shigo ta gabatar da sallah, Mamanta ma ta fito ta 蓷aura alwala ta shigo ta idar da sallah, ta ce Bilqees ta 蓷aura tukunyar dare. 

Bilqees ta mik'e ta hura wuta, ta 蓷aura abinci nan da nan ta kammala har dare Mama bata sake mata fuska ba, don haka ita ma bata sake cewa komai ba har suka ci abinci, sun kwanta kenan Alaja suka shigo gida saboda hayaniyar da suke yi, daga baya kuma su kayi shiru. Bacci ya 蓷auke Bilqees ganin haka yasa Mama ta lalla蓳a ta shiga 蓷akin Alaja ta tadda ta zaune tana shan kankana Mama ta zauna tare da cewa 

"Sannu Alaja"

Alaja sai da ta ha蓷iye sauran kankanan dake bakinta ta amsa da 

"Yauwa Maman Bilqees"

Sauke numfashi Maman Bilqees tayi sannan ta ce

"Alaja yau ko tsayawa ba ki yi mun gaisa ba? ai ko 蓷an sannu da dawowan nan nayi miki ai da da蓷i"

"Maman Bilqees are you teasing me? You know everything, amma ki ke nunawa ba abin da kika sani"

"Uhm Alaja ban fahimci abin da kike nufi ba, me kuma na sani?"

"Bilqees ta fa蓷a miki abin da ya faru a restaurant yau, shin so kike na maimaita miki ki ji daga bakina ne?"

"A'a Alaja cire ni cikin wannan abin, ni ai ba zan shiga tsakanin ku ba, kun fi kusa, ke da 拼arki ni na isa, wane yaro"

"Hehehe Maman Bilqees kina da wayo sosai, nayi tunanin kin manta ne, to amma ita Bilqees ta manta wacece ni?"

"Kin san yaro da kuruciya anma ba zata ta蓳a manta wa dake ba"

"Tayi min rashin kunya, don haka kada ta sake zuwar min restaurant"

"A'a Alaja ki yi hakuri nawa Bilqees take har yanzu dai yarinya take, zan yi mata fa蓷a ba za ta sake yi ba"

"Ai gani take ta girma wuyanta ya kai yanka..

"Haba Alaja ki yi hakuri mana, Bilqees fah 拼ar kice tun da mahaifinta ya rasu kike 蓷awainiya da ita, nononki ne kawai bata sha ba"

"To na ji amma ta kiyaye ni ba a min iskanci"

"To zan ja mata kunne, amma Alaja ina neman wata alfarma"

"I don't have money woo"

A tunanin Alaja ku蓷i Maman Bilqees take so ta ran ta mata, murmushi Maman Bilqees tayi ganin cikin sauri Alaja ta fassara maganar ta da neman rancen ku蓷i, kai Alaja da ku蓷i sai a hankali, ta sauke numfashi tare da cewa 

"A'a ba ku蓷i zan tambaya ba"

"Ina jinki to"

"Nayi wa Baban  Bilqees alkawari zan kula da Bilqees ko da bayan ransa ne, zan bata tarbiyya kamar yana raye, zan tsare mutuncin ta kamar yana raye, ba zan bari ta zubda 茩walla ba"

Tayi shiru tana jin 蓷aji cikin zuciyarta, ji take dama ace ba a ta蓳a halittar ta ba, ji take ina ma wannan rayuwar duk mafarki ne...

"Ina sauraron ki Maman Bilqees"

"Alaja ina so ki rufa min asiri ki bari na cika wannan burin na mahaifinta, na sani kin yi mata abin da ko mahaifinta iyakarsa kenan, amma ina so Bilqees takai budurcinta 蓷akin mijinta, ina so Bilqees tayi rayuwa cikin daraja da mutunci"

"Any way, za mu yi magana akai amma ba yanzu ba"

"To na gode sosai Alaja"

Ta mik'e tana 茩o茩arin fita, Alaja ta ce

"Maman Bilqees da fatan baki manta yarjejeniyar da mu kayi ba?"

"Eh ban manta ba"

"lokacin yana dab da 茩arasowa"

"Na sani amma akwai Allah"

"Daman akwai shi, kuma shi ya bamu tsawon rai har muka iski shekarar, to ki sani lokacin yana yi ba zan ji tausayinki ba, ba zan saurari magiyar ki ba, zan 蓷auki Bilqees na har abada!"

Tana gama fa蓷in hakan ta shige ciki, Maman Bilqees dake tsaye kamar ta 茩wala ihu haka take ji, ta juyo da 茩yar ta nufo hanyar fitowa...

Bilqees dake ma茩ale tana sauraron duk abin da suke tattaunawa, tun da taji fitar Mamanta tasan wajen Alaja za ta je, don haka ta lalla蓳o ta fito, don tasan a tunanin Mamanta tayi nesa a bacci. Taji duk abin da suka tattauna kuma wannan abin ba sabo bane duk lokacin da Alaja da Mamanta suke tare to shi suke tattaunawa akai, sai dai maganar su ta 茩arshe ce ta 蓷aga mata hankali..

"Yarjejeniya?"

Ta furta a hankali, jin alamun motsin fitowar Mamanta ne yasa tayi sauri ta lalu蓳o ta dawo 蓷akinsu ta kwanta....

Maman Bilqees da 茩yar ta kawo kanta 蓷akinsu, ta kwanta, cikin tashin hankali, ya za tayi da ranta abin da take tsoro shi yake shirin faruwa, ya za tayi ta hana faruwar abin, ya Allah ya kawo mata 蓷auki...

Tana saka da wannan tunani bacci ya 蓷auke ta.

Bilqees tun da ta saka kanta a kan pillow bacci ya gagareta, ta rasa dalilin da yasa Mamanta ke lalla蓳a Alaja, ko da laifin Alaja ne sai tayi ta bata hakuri, tun tana 茩arama take fuskantar wannan al'amarin. Wai shin ma, menene ha蓷in su da Alaja? wacce iriyar alaqa ce a sakaninsu da ita? Wacece Alaja a rayuwarsu? To in ba Alaja kenan ba za su rayu ba? saboda yadda take jin Mamanta ke fa蓷in Alaja ita ce gatansu. Wai shin ma, wacce yarjejeniya ce sakanin Mamanta da Alaja da take cewa lokacin wannan yarjejeniyar ya kusa cika.....

Da wannan zancen zuci bacci ya saci Bilqees ba tare da ta samo amshoshin tambayoyin ta ba...

Washegari 

Kamar yadda Bilqees take yi in ta tashi a bacci haka tayi, ta kammala aikinta sannan ta shigo palour ta zauna, ta 蓷auko wayarta da sai tayi kwana biyu bata yi amfani da ita ba, ta hau buga game, shiru Mamanta bata tashi ba, tun da ta idar da sallah. Bilqees ta ci gaba da game har 8:00am taji alamun motsin fitowar Mamanta daga 蓷aki ta 蓷ago tare da gaida ta

"Bonjour Maa"

Ta ce da Mamanta ina kwana da yaren French, Mamanta ta maida mata da yaren.

"Comment ca va?"

Take tambayar ta, how are you? Ya ya take? Ta amsa cikin siririyar muryarta da 

"Ca va Bien?"

I'm good, ta bata amsa da lafiya kalau, ta kalleta a hankali Mama ta ce

"Ya kike zaune, ba za ki je wajen aiki bane?"

"Umm ... Daman... Uhm akan abin da ya faru jiya ne.. na ce..

"Bilqees ki tashi ki shirya ki tafi wajen aiki nayi magana da Alaja a daren jiya, ta ce ba komai, ya wuce"

Sauke numfashi Bilqees tayi, tsam bata son tayi mutsu ko jayayya ta tashi ta fito ta shige toilet ta rage kayan jikinta ta watsa ruwa sannan ta fito ta shirya cikin uniform na wajen aiki, a lokacin Mamanta ta zuba musu abinci a plate suka ci tare sannan ta yi wa Mamanta sai an jima ta fito tsakar gidan babu kowa, tayi saurin fitowa bakin gate ta samu mashin ya kawo ta Alaja special restaurant......


******************************

Nigeria, Maiduguri KIRAWA'S FAMILY 

Horn yayi a 茩ofar gida, Baba Musa ya bu蓷e masa, ya shigo kai tsaye parking space ya wuce yayi parking, ya fito ya nufi 蓷akin sa. A gajiye ya dawo ya ajiye side bag nasa da wayarsa a kan tabur sannan ya rage kayan jikinsa ya fa蓷a toilet ya watsa ruwa, ya fito ya ji jikinsa wasai ya shirya cikin kayan wasan 茩wallon hannu sannan ya fito ya wuce side inda suke motsa jiki....

Da isowarsa ya tadda 茩annensa da suke wasan 茩wallon 茩afa har sun fara, bai bi ta inda suke ba, ya iso inda shi yake buga 茩wallon hannu, a hankali yake motsa jiki yana zaga wajen, ya 蓷an tsaya yana sauke numfashi sannan ya fara twisting a hankali yake motsa hannayensa, cen kuma ya fara stretching yana mimmi茩a hannayensa...

"Likita bokan Turai"

Ya dakata tare da yin murmushin gefen la蓳蓳e, ya ce

"Sa'eed how fah? Sai yanzu?"

Sa'eed ya sosa keyarsa tare da cewa 

"Bacci ne ya sake ni bayan sallah asuba"

"Oh ka kwana chatting ko?"

Dariya yayi yasan me Dr Waahab ke nufi ya ce

"A'a bros nayi baccin dare mah fah sosai"

"Ni ido biyu na kwana a hospital, gashi kuma na dawo gida ban koma bacci ba, har sai na idda motsa jiki kuma nayi breakfast sannan na kwanta na rama bacci"

茒auko 茩wallon Sa'eed yayi yana 蓷an buga shi da 茩asa yana bouncing ya ce

"Wa zai iya irin rayuwar ka, ni ban ta蓳a ganin wanda yake 茩in baccin dare irin ka ba"

"Nupe ba 茩i bane fah, wasu abubuwa ne nake yi, balle kuma yanzu da nake senor doctor kaga ni da baccin dare ai mun yi hannun riga"

"Lallai bros matar ka zata sha fama kam, let's play"

Suka soma wasan, sun jima suna yi yau ma Dr Waahab Waseem KIRAWA ne ya kwamushe wasan, suka zauna Sa'eed ya ce ba damuwa shima ko da watarana ne zai yi nasara suna hira suna dariya. Dr Waahab Waseem KIRAWA bai cika hira ko hayaniya sosai ba, in dai hira me tsawo ce to ko yana tare da Sa'eed ko mahaifinsa.....

"Barkan ku da safiya manyan mu"

Cewar 茩annensu da suka iso daga filin wasan buga 茩wallon 茩afa, suna share gumi, Ya Sa'eed ne ya amsa da 

"Barka dai footballers, kuma kun tashi a wasan kenan?"

Sageer Mustapha KIRAWA ne ya amsa da

"Eh fah me ya rage mun yi wining"

"To Abdullahi kai ko ya ka bari hakan ta faru?"

"Ya Sa'eed hariya ce amma ba komai ai ba a gama ba, gobe ma rana ce"

Dariya su kayi suna kallon Abdullahi Umar KIRAWA wanda ya gama kulewa sabar takaici ko kallon 拼an team nasa bayyi ba, yana huci"

"Little bro kada ka damu daman haka wasan ya gada, ko ka kada wani ko a kada ka"

Cewar Dr Waahab Waseem KIRAWA, a lokacin da yake ci gaba da goge gumin dake fuskar sa. Abdullahi Umar KIRAWA ya sauke numfashi tare da cewa 

"Kyale su gobe ma rana ce"

"Kada ka cika baki Abdul kawai ka bada gari ba za ka iya ja dani ba"

"Ba zan bada ba har sai nayi nasara"

Dr Waahab Waseem KIRAWA bai sake tofa baki ba, ya 蓷auki ruwan roba ya kwankwa蓷a sannan ya ajiye yana jinsu har Abdul yayi zuciya ya bar wajen, sauran ma suka tafi, Ya Sa'eed ya kalli Dr Waahab da ya kurawa gefe guda idanu da alama ya fa蓷a a kogin tunani, ya matsu ya 蓷an 蓷aura hannu akan kafa蓷ar sa tare da cewa 

"Ya dai Likita?"

A hankali ya sauke numfashi ya dubi Ya Sa'eed cikin kulawa yayi magana 

"Jikin Mommie ne yake damuna, har yanzu nake ganin kamar babu sauyi, kuma bana so a fitar da ita outside"

"Ban tari numfashinka ba Likita amma ina ganin a fitar da ita 茩asar wajen kawai shine mafita, kaga an kaita hospital a garin Kano jiki ya茩i sauki haka ma Abuja nan ma gidan jiya, kawai a fitar da ita ko za a dace"

Ya sauke numfashi yayi shiru na wani lokaci sannan yayi magana 

"Na 蓷aurata akan wasu magungunan, mu bari zuwa wani lokacin"

"To Allah ya bata lafiya"

"Amin"

Dr Waahab Waseem KIRAWA ya mik'e zuwa ciki ya bar Sa'eed a zaune yana amsa waya. 

A hankali ya tura 茩ofar 蓷akinsa ya shigo, da mamaki yabi ko'ina da kallo, ganin an gyara komai sai 茩amshi 蓷akin ke yi, gashi an ajiye masa basket na breakfast daga gefe. A hankali ya 茩araso ya tsugunna ya bu蓷e kulolin yaga farar doya ce sa egg sauce sai kuma kunun gya蓷a dake jug, ya rufe ya tashi ya rage kayan jikinsa ya fa蓷a toilet.....




Comments and share fisabilillah

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.