Free chapter 路 Read without an account

Nadama page 12

by Fatima Isah 路 NADAMAR DA NA YI

  NADAMAR DA NA YI馃檰馃徏

             Fatima Isah

 

           

  

Edit.....2026

Love story 2015馃グ

***

  Page 蓷in yau naki ne 茩awar arziki tun ta yarinta Tabara Muhammad Kabir ha茩ika komi nada lokaci ubangiji Allah ya baku zaman lafiya dake da mijinki Allah yasa wannan aure an yishi a sa'a Ameen.

                  *******

                 PAGE 12

Duk wani abu da ya kamata ayiwa Amarya Pendo Ummi tayiwa Fatima, irin abubuwansu na Fulani da dai sauransu ita kanta Fatima takanji sauyi a jikinta takanyi tunanin inama wannan gyara da akayi mata duk na Musaddik ne.

Bayan an gama komi da misalin 茩arfe 8:00pm Dad ya 蓷auki 'yarsa da kansa zai kaita har gidanta kuma ya hana ko wace mace binsu uwa uba harda Pendo Ummi ya hana ya ce sai dai su tafi daga baya.

Fatima tanaji tana ganin yau zatayi ban kwana da 'yan uwanta za'a kaita gidan wanda tafi tsana a duniya, tana tafe tana kuka har ta isa mota Dad shida kansa yasa hannu ya bu蓷e mata sannan ya kamata ya zaunar da ita a kujerar baya, driver ne yazo da sauri Dad ya daga mashi hannu ya ce.

"A'a barshi Suleiman na hutar da kai yau ni zanja da kaina nakai 'yata har 蓷akinta sannan na saka mata albarka."

Suleiman yana murmushi ya bu蓷ewa Dad mota yana fa蓷in.

"Gaskiya ne Alhaji ai dama haka ya kamata duk uban 茩ir茩i ya dinga yiwa ya'yansa duk ranar da aka 蓷aurawa yarinya aure to ya 蓷auketa da kansa ya kaita har 蓷akinta yayi mata addu'a domin kuwa matan da za'a tara su kaita wata ko murna maybe batayi da aure balle ta samu damar yiwa ma'auratan addu'a gaskiya wannan halin naka Alhaji ya kamata duk uba na gari ya yi koyi da kai, Allah ya tsare Allah yasa wannan aure an yishi a sa'a, in shaa Allahu wannan aure anyi shi kenan har abada."

Tunda Suleiman ya fara magana Dad ya tsaya yana kallonshi cike da jin da蓷i kalamansa yayi murmushi ya ce

"Suleiman nagode da wannan adduar taka sannan ina mai yi maka albishir daga yau ka tashi daga driver gidan nan zaka koma kana cikin kashin kanka na baka 茩yautar million goma da gida kaje kaja jari."

"Alhaji ne? Ko dai mafarki nake?"

"Suleiman ba mafarki kake ba da gaske ne wannan yana 蓷aya daga cikin 茩yaututukan dana tana darwa wannan auran ga duk wanda ya taya ni murna cika wannan burin nawa."

Suleiman 茩asa ya fa蓷i yana mai cigaba dayiwa Dad godiya ita ko Fatima a zuciyarta ciwa ta yi.

'Humm Dad kenan ai kam kana dab da asarar dukiyarka danko ni wallahi banga mijin aure ba'

Check Dad ya 蓷auko ya rubutawa Suleiman har naira million goma kamar yanda ya fa蓷a mashi tare da makullin gida.

Hannun Suleiman na rawa yasa hannu ya amsa yana godiya hawaye na fita a idonsa ya ce.

  "Alhaji nagode Allah ubangiji yasa ka gama da duniya lafiya a kan yanda kake taimakon talakawa insha Allahu wannan auran ainyishi kenan mutu karaba"

"Allah yasa Suleiman dan Allah sai aje a kama sana'a."

"Insha Allahu Alhaji na gode."

"Haba is ok godiya ta isa haka."

Har Dad ya tayar da mota ya fita Suleiman ya kasa tashi daga inda yake tsugunne.

Dad na cikin mota yana driving a hankali cikin 茩wanciyar hankali yana kallo 'yar tashi ta madubin mota, yana kallon yanda hawaye ke fita a fuskarta.

A haka har suka isa makeken gidanta dayasha ado na kece raini, bayan sun isa mai gadi yayi sauri ya bu蓷e mashi get ya shiga yayi parking ya fito ya bu蓷e mata yasa hannu ya kama mata hannu suna tafiya har suka isa bakin wata 茩ofa wanda ake danna mata wasu numbers ta bu蓷e, itama 茩ofar tasha ado da irin fentin zamani, a hankali Dad ya furta.

"To Fatima gashi Allah ya kawo ki gidanki kiyi addu'a kafin mushiga kuma ki shiga da kafar dama."

Kai ta 蓷aga mashi alamar to tayi kamar yanda ya umarceta, wani katafaran parlour ne suka isa wanda yake 蓷auke da kujeru iri daban-daban.

Kai gidan ya ha蓷u fa iya ha蓷uwa, saida Dad ya shiga ko ina ya nuna mata duk yanda gidan yake kafin suka dawo parlour suka zauna ya ci gaba da yi mata nasiha mai shiga jiki kamar haka.

"Fatima dan Allah kiyi hakuri ki zauna da mijinki lafiya, ki guji fishin mijinki kiyi masa biyayya kada ki biyewa son zuciyarki ya kaiki ga dana sani, wallahi Fatima idan kika zauna da mijinki lafiya zan maki duk abinda bakiyi tunani ba.

Fatima mahaifiyarki ta baki tarbiya iya bakin gwargwado dan haka idan naga akasin haka bazanyi kuka da ita ba, wallahi Fatima duk ranar da kika kashe auranki daga ranar babu ni babu ke sai dai ki naimi wasu iyayen amma bamu ba.

Fatima doni mo yidi ma pat yeccatama,to a nani gam hore mada, to a nanai ma gam hore mada dan Allah kiji abinda muka fa蓷a maki."

Kullum Dad maganarshi 蓷aya kenan, saida Dad ya yi mata nasiha mai ratsa jiki kafin ya barta ya fita.

Motar Dad ta fita kenan tasu Ikram na danno kai

Ikram ita da 茩awarta Meena su kansu gidan ya baso sha'awa sun tabbatar da 茩awarsu tayi dacen gida bayan sunyi parking suka shiga gidan dama sun 茩ira Faruok ya fa蓷a musu code number 茩ofar, inda Dad ya barta a nan suka isketa ta kasa tashi sai hawaye da taketa aikin fitarwa.

"Gaskiya teema am bazan boye maki ba you have a big problem haba sai kace ba ful蓳e ba, fulani an sansu da kunya da kauda ido da abinda suke so amma ke naki ko irin alkunyar nan babu haba Fatima don't kill ur self."

Murmushi Fatima tayi mai 蓷auke da takaici ta girgiza kai ta ce

"Ikram, I know nobody will understand my feelings, ko ke bazaki fahimce ni ba har sai kin fa蓷a cikin irin halin dana fa蓷a."

"Allahumma ajirni fi masibati, dan wannan musiba ce Fatima ina naiman tsari tun yanzu."

Dariya Meena ta 茩washe da ita dan jin abinda Ikram ta ce.

A hankali  Ikram ta zauna inda take ta dafa kafa蓷arta ta fara magana cikin rarrashi.

"Please Fatima ki farka daga mummunan mafarkin da kike dan idan baki wasa ba kina dab da rasa  tunaninki dan wannan mafarki ne, Fatima wallahi Allah duk macen data samu miji kamar Faruok tayi sa'ar miji nakece reni meye Faruok baidashi da har kika likewa wannan makahon?"

"NAGARTA Musaddik yafi Faruok komi a wajena zan iya rabuwa da kowa saboda Musaddik dan haka kada ki kuskura ki muzanta abin sona.

Ikram kenan Allah hautuma be irin yide mi yidi musaddiq do ni."

Murmushi Ikram tayi ta koma ta jingina da kujera tana dariya, saida ta 蓷auki lokaci tana kallon Fatima kafin ta ce.

"Fatima dan Allah bakiji kunyar fa蓷in Musaddik yafi Faruok NAGARTA ba kin sanko abinda ake nufi da NAGARTA? Anyways mubar maganar haka tunda naga har yanzu ba茩ya son gaskiya, amma Fatima bari na tambaye ki taya kuka fara soyayya da Musaddik bayan barina 茩asar nan?"

Murmushi Fatima tayi ta lumshe idonta kamar bazatayi magana ba ta bu蓷e ido ta kalli Ikram ta ce.

"Hmm long story Ikram soyayyata da Musaddik daga Allah ne."

"Naji amma ya kamata ki dan ban labarin ha蓷uwarku, amma ba nan ba, mushiga daga cikin bedroom dinki dan nasan yanzu ana dab da rako ango."

Ikram ta kama hannun Fatima suka haura saman, masha Allah suna shiga suka dinga bin 蓷akin da kallo komi na 蓷akin pink ne dama sunsan best colour nata kenan, ita kanta 蓷akin ya yi mata kyau iya kyau ya tafi da imaninta.

Bakin gado suka zauna dukansu kafin Ikram ta ce.

"Teema ke naki sauraro da labarin wannan soyayyar taku."

"Hmm wata ranar Monday da mis.."

Kas maganarta ta tsaya ne sakamakon sallamar dasu Faruok sukayi tare da abokansa su uku.

Da sauri Fatima amarya ta rife fuskarta Faruok dai-dai inda take ya nufa ya zauna har suna gogar juna ya ce.

To

"Haba Amaryata daga zuwanmu kuma sai a rufe fuska?"

"Kai bama son iskanci kadai bari mu tafi."

Cewar Major Bilal.

Murmushi Faruok ya yi wanda ke 茩ara masa 茩yau a koda yaushe, 蓷aya daga cikin abokan nasa ne ya ce.

"Kaga Bilal gara muyi mutafi tun kafin ya kore mu gara mu tafi cikin arziki."

"Haka maganarka take Anwar dan haka sai muyi addu'a ko."

Sunyi addu'a kafin 茩awayen amarya su Ikram sukace masu sai sun bada ku蓷in siyan baki kafin su tafi cikin wasa da dariya Bilal ya basu da hannunsa tunda sukazo Bilal yake kallon Ikram.

Bayan sun gama Faruok ya ce.

"To ai sai a tashi a tafi haka ladar ta isa."

"Au korarmu kake tun yanzu."

Dariya ya yi ya 蓷auki hannunsa ya 蓷aura kan kafa蓷ar Fatima ita ko nan mutuwar zaune tayi kirjinta sai dukan uku-uku yake.

Dariya sukayi gabaki 蓷ayansu suka tashi zasu fita har sunkai bakin 茩ofa Bilal ya ce.

  "Kai bama son iskanci kana nufin bazaka rakamu ba?"

"Kai kuna da matsala kunsan bana son nayi nisa da amaryata"

Yana maganar ne yana tashi a hankali ya 蓷an sunkuyo da kai ya ra蓷a mata.

"Please kafin na dawo kiyi wanka ki 蓷auro alwala dan godiya ga Allah."

"Kai wai kai wane irin dan iska ne da baza kazo ka rakamu ba."

Dariya Faruok ya fashe da ita sannan ya juya suka fita saida ya rakasu har wajan motocinsu suka fita mai gadi ya rufe sannan ya dawo, 蓷akinshi ya wuce direct, bayan ya shiga bedroom ya 蓷auki farin jallabiyarshi ya shiga badroom, bai wani juma ba a ciki ya fito da jallabiyar jikinshi yana goge ruwan da ke kanshi da towel.

Bayan ya aje towel 蓷in ne ya juya ya fita, direct 蓷akin gimbiya ya nufa yasa hannu ya tura 茩ofa ya jita a rufe da key, cak Faruok yayi mutuwar tsaye dan yasan da gangan ta rufe 茩ofar, 茩arfin hali yayi irin jarumta nan ta mazan fama ya fara knocking amma a banza bama tasan yanayi ba cikin sanyi murya ya ce.

"Please Fatima ki bu蓷e kofar kizo muyi sallah muyi addu'a idan yaso da mun gama sai ki rufe 茩ofar please Fatima."

Tsaki tayi kawai ta gyara 茩wanciya, Faruok ya da蓷e a tsaye bata bu蓷e 茩ofar ba saida yaga da gaske take kafin ya juya ya koma 蓷akinshi.

Faruok da Fatima haka suka 茩wana ko wanansu da abinda yake tunani su duka sai dai irin barawon barcin nan ya 茩washe su.

Da asuba Faruok ya tashi yayi alwala ya tafi masallaci dake kusa da gidansu wanda kana jin lokacin da ake 茩iran sallah.

Bayan Faruok ya dawo ya nufi 蓷akinta yayi knocking ya ce.

"Fatima ki tashi lokacin sallah yayi idan yaso idan kika gama sallah sai ki koma ki 茩wanta."

Yana rufe baki ya juya ya koma 蓷akinshi dan ya tabbatar da tajishi.

************

Da misalin 12:30pm

茦wance take sai juyi take da alamu yunwa takeji dan bazata iya tuna ranar data zauna ta natsu taci abinci ba, raban da tasa wani abu a bakinta tun jiya da zasu taho Pendo Ummi ta bata wani abu a cup ta sha, amma tayi wanka ta sauya kayan dake jikinta tasaka riga da wando irin fashion ne masu 茩yau sun 蓷an kamata.

Fatima da taga babu sarki sai Allah yunwa na shirin kasheta yasa tatashi tun safe Faruok ke fama da ita ta bu蓷e 茩ofa tazo suyi breakfast amma ta kiya, a hankali ta bu蓷e 茩ofa ta fara tafiya kamar marar gaskiya, ajiyar zuciya ta sauke dan ganin babu kowa har parlour dake 茩asa kitchen ta nufa ta fara dube-dube taga duk ga komi nan na abinci babu abinda babu.

Gas ta kunna ta shiga fira arish potato.

Nan dai ta shiga girka abinda zata saka a bakinta, sauri-sauri take dan kada Faruok ya kamata.

Kafin ace maka me ko ina ya ba蓷e da kamshin girkinta.

Tsaye yake yana kallon duk wani bangare na jinta yana murmushi a hankali ya tako har inda take ya wani rungumuta ta baya ihu ta fasa ciki da tsoron shigowarshi.

"Please yaya Faruok meye haka?"

"Matata na kama ko na yi laifmeye

Ya furta cikin wata irin murya mai wuyar fasarawa..

Kash!!! kudaiyi hakuri muje zuwa..

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.