Free chapter 路 Read without an account

Page 01

by Ummu~Fadeela 路 MARYAMA

馃挮MARYAMA馃挮
BY
Ummu Fadeela
Typing... 馃摬
EPISODE 01
Bismillahi Rahmani-Raheem. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin sammai da 茩assai. Tsira da aminci su 茩ara tabbata ga shugaba, jagaba Annabi Muhammad (S.A.W), da iyalan gidansa da sahabbansa baki 蓷aya.
KHALEEFA BIN ZAYED AL NAHYAN STREET, ABU DHABI CITY (UAE).
Katafariyar unguwa ce da ke cikin babban birnin Ha蓷a蓷蓷iyar Daular Larabawa wanda aka fi sani da Abu Dhabi. Unguwa ce mai 蓷auke da rukunin gidaje masu kama da aljannar duniya...
Lumshe kyawawan fararen idanuna na yi. Na da蓷e ina jin yadda ake yabon kyawun zubin halittar idanuna; mutane da dama idan sun tashi yabon kyan halitta ta, sukan kira ni da "mai idon madara" tsabar irin hasken da kyawun da Allah ya ba ni. Amma a halin da nake ciki yanzu, sabanin kasancewar su launin madara, idanun sun yi jajur kai kace attaruhu aka 蓷aka aka watsa a cikinsu, ko kuma na kwana uku ina kuka ba tare da tsagaitawa ba. Sai dai ba ko 蓷aya daga ciki; tsabar tashin hankalin da nake ciki ne ya haddasa mini canzawar launin idon.
A hankali na juya na kuma kallon shi, zuciyata na bugawa da 茩arfi da 茩arfi, yayin da nauyin da kaina ya yi ya haddasa mini ganin dishi-dishi... Yana dur茩ushe gaban gadon da nake zaune ya ba ni baya, yana ta daddaure hodar iblis (C0C@!NE) cikin wasu 茩ananan ledojin nylon. Cikin sauri-sauri yake aikin, wanda duk bayan da茩i茩a 蓷aya sai ya 蓷aga kai ya kalli 茩ofa.
Runtse idanuna na kuma yi, zuciyata na tsananta bugu yayin da nake tuna cewa wai ni ce zan ha蓷iye gaba 蓷aya wannan hodar iblis 蓷in a cikin cikina, in yi safararta zuwa Nigeria. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, na furta cikin raina, kana na bi dogayen 茩afafuna farare sol da kallo. 茒aure suke cikin sar茩o茩i (chains) sakamakon yunkurin guduwar da na yi, hakan ya sa suka 蓷aure ni. Zuwa yanzu na tabbatar ro茩o da magiya ba za su yi mini amfani ba.
"You have to be brave," zuciyata ta fa蓷a mini. Tabbas dabara ce kawai zan yi da taimakon Ubangiji in bar wurin nan; idan ba haka ba, rayuwata ta 茩are. Safarar cocaine ba 茩aramin ha蓷ari (risky) ba ne ga rayuwata. Cikina ne ya hautsine gami da ba da sautin kululululu sakamakon tunawa da na yi wai ha蓷iyar wa蓷annan ledodin zan yi a cikina. Duk da ya sanar da ni hanyoyin da za a bi a fitar da su idan mun isa Nigeria, hakan bai rage ko da 茩aso 蓷aya cikin 蓷ari na irin tsoratar da na yi ba.
A hankali na fara bin 蓷akin da kallo ko zan dace. Aiko idanuna suka sauka kan bedside lamp dake kusa da ni, ga kuma wani tangaran mai 蓷auke da furen rose duk a wuri 蓷aya. Cikin dabara na kai hannuna duk biyun na 蓷auki lamp 蓷in da kuma furen (flower vase) 蓷in... Ya du茩ufa sai aiki yake a gaggauce, hakan ya sa bai maida hankali kaina ba.
Runtse idanu na yi ina tabbatar wa kaina abin da zan aikata shi ne daidai. Bai yi aune ba ya ji saukar tangaran a 茩eyarsa, ji kake garammm! Cikin azama ya juyo jin abin da bai yi tsammani ba (unexpected). Yana juyowa na kuma rota masa bedside lamp 蓷in a daidai gurin. Take ya yi baya-baya, ya 茩wala wani irin ihun kiran sunana: "MARYAMAAAA!" Ya fa蓷i 茩asa, jini ya fara malala a wurin.
Da gaggawa na fara 茩o茩arin kwance sar茩o茩in da ya 蓷aure mini a 茩afata. Sai a lokacin na kula da cewa tunda ya fa蓷i bai 茩ara motsi ba, ga jini dake tsartuwa ta 茩eyarsa, baki, har da hanci. Zuciyata ce ta kuma bugawa da 茩arfi. 茒an matsawa na yi kusa da shi, a hankali na ce, "ABDALLAH?" Amma shiru, ko motsi bai yi ba. Na 蓷aga hannunshi ina sakewa, hannun ya dawo matacce.
Mikewa na yi ina ja da baya-baya yayin da wani irin jiri ke kwasata. "Ya mutu!" na furta da 茩arfi. A lokaci 蓷aya kuma wani irin 茩arrawa ya yi ruri cikin 茩wakwalwata: na kashe shi! Idan aka kama ni shikenan, ba mai 茩ara jin labarina a duniyar nan...
Ba tare da wani dogon tunani ba, na janyo bedside drawer, na cire fasfo (passport) nawa da kuma credit card, sai wayoyina guda biyu da kuma tablet tawa. Cikin sauri-sauri na kuma zuge wata doguwar drowar mai 蓷auke da kayayyakina jere reras; ba tare da na bi ta kansu ba, na janyo wata 'yar akwati na bu蓷e. American dollars ne shimfi蓷e 蓷auri-蓷auri. Duk 茩aunata ga ku蓷i, duk irin wuyar da na sha da irin ha蓷arurrukan da na shiga wurin tara su, amma na kasa 蓷aukarsu. Tabbas wani tashin hankalin ya fi gaban wani.
茒auri biyu kawai na 蓷auka, na sa su tare da wayoyina da na riga na sa su a flight mode. Na yafa gyalen ba茩ar abayana cikin hanzari, kana na bi gefen Abdallah na fice daga 蓷akin.
"Act smart Maryama, this is Dubai, not Abuja, Nigeria," zuciyata ke ba ni shawara. Sai dai duk yadda na so bin shawarar zuciyata, na kasa; jikina sai rawa yake, yayin da launin idanuna ke 茩ara sauyawa saboda tsananin tashin hankali. Cikin sa'a na fita daga gidan ba tare da mai gadi ya tuhume ni ba, sanin matsayina da ya yi a gun mai gidan. Taksi (cab) na tsayar na shige, ha蓷e da ce masa: "Airport."
Ina daidaita zamana cikin taksin, wani irin kuka mai masifun 茩arfi ya taho mini, amma haka na dinga dannewa, wanda ya haddasa mini rawar jiki ha蓷i da takurewar fuska.
ABU DHABI INTERNATIONAL AIRPORT, UAE.
"I need a ticket to Nigeria," na fa蓷a muryata na rawa.
茒ago kai mutumin ya yi yana kallona jin yanayin muryata, sannan ya mayar da kanshi yace, "Your passport, ma'am."
Ciro 蓷an 茩aramin fasfo 蓷ina na yi jikina na rawa, na mi茩a mishi. Ya kar蓳a ya 蓷an dudduba, kana ya miko min yace, "Okay, give me a moment to check, ma'am."
Ya maida hankali kan kwamfutar dake gabansa, ya 蓷an yi danne-danne na 蓷an lokaci, kana ya 蓷ago yace, "The earliest flight is Emirates Airlines, but the economy is full. Would you like to opt for business class? Ko kuma in yi scheduling naki zuwa gobe?"
"Gobe?" na maimaita. A'a, babu yadda za a yi in kai gobe a 茩asar nan, wannan ba mai yiwuwa ba ne. Cikin ro茩o na ce, "Please sir, ka 茩ara duba mini economy 蓷in, maybe a dace."
Kafin ya ba ni amsa, kamar ance in juya, na hango su suna ta baza ido cikin filin jirgin (airport 蓷in). Sun kai su biyar; 茩atti ne sosai marasa kyan gani, idan sun dam茩e ka sai dai uwarka ta haifi wani ba dai kai ba. Yara (boys) na Abdallah ne, mun kwashe lokaci sosai muna aiki tare da su.
Zaro ido na yi yayin da wani irin gumi ya 茩aryo mini har yana 蓷iga a 茩asa. Jikina na rawa na zaro credit card nawa na mi茩a masa na ce, "A ba ni business class 蓷in."
Kallona ya yi da mamaki ganin yadda nake ta jan mayafina don ya rufe mini fuska, yayin da nake jin rawar da 茩afafuna ke yi tana gab da kayar da ni 茩asa... Kaina a sunkuye nake tafiya bayan na gama da batun tikiti. Mutumin ya sanar da ni na je na duba information panel domin sanin ainihin lokacin da zamu tashi da kuma lambar kujerata (seat no).
茒an 蓷ago kai na yi ka蓷an na kalli gefen da na hango su 蓷azu. Aiko 茩araf muka ha蓷a ido da John, wanda shi ne babban yaron Abdallah. Muna ha蓷a ido naga ya tunkaro inda nake. Na san ba zai yi gigin da za a kama shi ba ganin a airport muke, hakan ya sa nima na 蓷an saita nutsuwata, amma can cikin zuciyata saura 茩adan ta shige cikin cikina. Tafiya nake amma gaba 蓷aya hankalina yana kansu, ganin bina suke bil-haqqi.
Ba tare da tunani na biyu ba, na 茩wasa a guje. Domin duk 茩o茩arina na ganin ban yi gudu ba, kasawa na yi, ga uban gumin da ya gama mini wanka. Gudu na dinga yi irin na ceton rai. Cikin ikon Allah ban ha蓷u da jami'an tsaro (security) ba...
茦araf na ji na bu茩i wani abu mai 茩auri kuma mai laushi, kana mai sanyayyen 茩amshi. A lokaci 蓷aya kuma wani irin zafi ya ziyarci hannuna ha蓷e da watsewar wasu takardu a 茩asa. Jikina na mazari na sunkuya da sauri-sauri na shiga tattare takardun da suka zube a 茩asa. Cikin da茩i茩a 蓷aya na mi茩e, na kamo tafin hannunshi ba tare da na 蓷aga kai na ganshi ba, na dam茩a mishi takardun ha蓷i da furta: "Sorry, sorry, it is not intentional." Ban yarda na ha蓷a ido da shi ba, na ci gaba da gudu na.
Juyawa ya yi yana kallona da madaukakin mamaki kafin ya bi tsadadden kwat (suit) nashi da na 蓳ata masa da kofin shayi (coffee) dake hannunsa... Wani 蓷an lungu na bi, na ga wani babban jikin juji (dustbin). Ba tare da dogon tunani ba na shige cikin dustbin 蓷in mai cike da tarkacen datti, ina sauke numfashi da zare idanu kamar 蓳era cikin bokitin gari, tare da addu'ar Allah ya tseratar da ni.
Wani lokaci can baya
GOMBI L.G.A, ADAMAWA STATE.
Wasu kyawawan 'yan mata ne su biyu sanye da kakin makaranta (uniform); riga da wando da kuma hijabi. Wandon kore mai duhu (dark green), yayin da riga da hijab 蓷in ya kasance farare tas. 茦afafunsu sanye cikin takalman sawu-ciki ba茩a茩e 茩irar Toms. Hannunsu ri茩e da wasu dogayen takardu wa蓷anda suka fi kama da takardar jarabawa (question paper).
Fuskar 蓷ayar cike take da murmushi da annuri, yayin da 蓷ayar kuma duk tsiyarka ba za ka fahimci yanayin da ke saman fuskarta ba. Tafiya suke cike da nutsuwa irin ta 'yan matan da suka san kansu, yayin da mai fara'ar take 蓷an magana ka蓷an-ka蓷an, 蓷ayar kuma amsarta ba ta wuce "Uhum" ko "Um-um".
A haka suke 茩etara hanyar da suka shigo, kasancewar wurin kasuwa ce sosai irin dai kasuwar bakin hanyar nan; babu abun da zaka nema a wurin na siyarwa ka rasa. Saboda haka, wurin cike yake da jama'a ana ta harka. Wasu cikin shaguna, wasu kuwa tebura suka kakkafa, wasu kuma tantuna (tampol). Don haka ko da yaushe wurin cike yake. Mutanen unguwar ba su da kewa ko ka蓷an. Unguwar KASUWAN BUTU ke nan dake garin Gombi na jihar Adamawa.
Tsallake kwaltar da ta raba kasuwar da kuma cikin unguwar suka yi, suna ci gaba da tafiya suna ratsa gidajen dake cikin unguwar, wa蓷anda galibinsu tsofaffin gidaje ne irin na masu 茩aramin 茩arfi... 茒an ta蓳a ta mai maganar ta yi, ta ce, "Pretty, kinga mutumin ki tunda ga wurin fulani masu sayar da nonon can nake hango shi ya kafe ki da idanu, sai murmushi yake zabgawa kamar mai tallan Closeup. Ni tsorona ma kar ya yanke hannunshi da zarton nan mu shiga uku," ta fa蓷a cikin sigar zolaya.
Wacce aka kira da Pretty ta 茩ara 蓷aure fuska tamau kamar ba ta san me dariya ba. Cikin muryarta mai da蓷in sauraro ta ce, "Kinga UMAIMAH, raba ni da jarabarki. Ba na son tashin hankali da tsakar ranar nan. Ki bar ni in ji da abun da ke damuna, please..."
Hakan kuwa ya yi daidai da isowarsu kusa da wani wuri da ake aikin 茩era gado da kujeru da dai sauran kayan katako. Wani saurayi ne tsaye ri茩e da zarto, yana 茩o茩arin tsaga katako. 茦akka茩fa ne sosai, a 茩alla zai yi shekara 27 zuwa 28 a duniya. Kallon fari zaka 蓷auka shi 蓷in ba茩i ne, amma a zahiri fari ne sol; tsabar tsayuwa cikin rana ne ya 茩odar da shi. Dogo ne mai kiran mazantaka, sai dai kallo 蓷aya zaka masa ka fahimci talauci ya samu lasisi a jikinsa. Duban wacce aka ambata da Pretty kawai yake yi ba tare da 茩iftawa ba (without blinking), yana 蓷an murmushi ka蓷an-ka蓷an, wanda zahiri daga can cikin zuciyarshi murmushin ke fitowa.
茒an rusunawa Umaimah ta yi ta ce, "Barka da aiki, HAMMA JABEER."
Murmushinsa ya kuma fa蓷a蓷a, yana kallon cikin idanun Pretty, ya ce, "Barkanku dai. Ya jarabawar? Hope dai bai ba gimbiyata wahala ba?"
Ko uffan ba ta ce ba. Sai Umaimah ce ta kuma cewa, "Alhamdulillah, final exam ya yi da蓷i Hamma Jabeer. Sai ku taya mu da addu'a kawai." Kafin ta 茩arasa maganar, ta hango Pretty ta yi nisa, da 蓷an sassarfa ta bi bayanta.
Murmushi Jabeer ya yi ya ce, "My drama queen."
Umaimah ta ce, "Wani irin busasshen walakanci ne wannan Maryama? Ya zaki yi tafiyarki ki barshi ko gaisuwa ba kiyi mishi ba, bayan kinsan domin ki yake tsaye a wannan uban ranar? Haba mana Maryama, at least you should show some concern mana."
Tsaki Maryama (Pretty) ta ja, amma ba ta ce komai ba.
Umaimah ta kuma cewa, "Wannan dai ba halin 茩warai ba ne wallahi, ki gyara. Gidanshi zaki je a matsayin mata. Ko ba ma wannan ba, yayanki ne jini 蓷aya, ai ba wasa ba. Maybe ma yanzu haka gadon aurenki yake ta fafutukar 茩erawa, amma ko sannu kin gaza ce masa."
茒um! 茒um! 茒um! 茦irjin Maryama ya ba da sauti jin furucin Umaimah na 茩arshe: "Maybe ma gadon aurenki yake fafutukar 茩erawa." Ta 茩ara maimata maganar a zuciyarta.
Da sauri ta ce, "Impossible! Ni na fi 茩arfin a mere 茩afinta ya 茩era mini gadon aurena. Kamar ni?" ta fa蓷a tana nuna kanta. "Impossible wallahi!"
Bu蓷e baki Umaimah ta yi da nufin yin magana, Maryama ta yi saurin katse ta ta hanyar 蓷ago dara-daran idanunta ta zuba mata ha蓷i da fadin, "Look Umaimah, dan girman Allah ki 茩yale ni in samu sau茩i. Rayuwata daban, taki daban. Don kina matsayin aminiyata ba shi zai sa rayuwarmu ta zama 蓷aya ba. You know me, and you know all my dreams and my desires, so leave me alone, please."
Ta juya ha蓷i da shigewa 蓷an tsurkukin gidansu wanda ya fi kowane lalacewa a unguwar. Girgiza kai Umaimah ta yi, kana ita ma ta shiga gidansu wanda yake katanga 蓷aya da na su Maryama.
Wani irin takaici ne ya turnu茩e zuciyarta lokacin da ta shiga cikin 蓷an matsakaicin gidan na su, sakamakon arba da ta yi da wani 茩atoton bokiti cike taf da ruwan da aka wanke 茩alwar yin daddawa, ga 茩udaje sai yawo suke yi a kai. Gefe guda kuma, innarta ce ke ta faman kir蓳a 茩alwa a wani 茩atoton turmi.
Yami蓷a fuska ta yi ta ce, "Kai Innarmu! Yanzu ba zaki daina wannan abun ba? Duk gida ya cika da 茩auri ta ko'ina. Ni shi yasa fa ba na son kawo 茩awayena gidan nan, don kada su raina ni."
Dakawa Inna ta yi mata ta ce, "Ungo naki Maryama! Ja'ira da idanu kamar 蓷an farin alade. Wannan shi ne sallama ko haka aka koya miki?"
Turo baki ta yi ta ce, "Kai Innarmu! Don kawai na fa蓷i gaskiya? Duk sana'ar duniyar nan ki rasa wadda zaki yi sai daddawa? Allah, duk sanda na yi ku蓷i zaki huta da wannan wahalar."
Tana fadin haka, ta 蓷aga labulen 蓷akinsu ta shige ciki tana kunkuni... Dafe kumatu Inna ta yi, sannan ta ce, "Allahu ya shirya mini ke, Maryama." Kana ta ci gaba da kir蓳a daddawarta.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol