Free chapter 路 Read without an account

Page 27/28

by Ummu~Fadeela 路 MARYAMA

馃挮MARYAMA馃挮

                            BY 

                   Ummu Fadeela

Typing馃摬

Episode 27/28.....


Yatsar shi manuniya ya 蓷aura saman le蓳ena idanunshi a lumshe ya furta, "Shhhsshhshttt, bacci pretty".

Daga haka bai 茩ara bani damar yin magana ko kuka ba ya rufe idanunshi gam ha蓷i da matse ni sosai tamkar dai zai maida ni ciki ko mai tsoron kar wani ya kwace masa ni. da haka bacci mai cike da nisha蓷i da annashuwa ya 蓷auki Jabeer yayin da ni kuma kamshin turarensa na oud essential ya cika min hanci ya hanani nutsuwa gefe guda kuma irin ri茩on da ya min da ko numfashin kirki bana iyawa.tunani ne suka min rubdugu nima bansan sanda bacci ya 蓷auke ni ba.....

Sau茩ar numfashinta a hankali ne ya tabbatarwa Jay cewa ta yi bacci, a hankali ya 蓷an sassauta ri茩on da ya mata yana gyara mata kwanciya yadda zata zama comfortable, still kanta yana saman damtsen hannunsa suna fuskantan juna, addu'a ya yi masu su duka sannan ya gyara masu duvet 蓷in kana ya cigaba da shafar gashin kanta wanda yana cikin abin da ke burgeshi a gun 蓷iya mace, balle na Maryama da ya kasance na musamman,da haka bacci na gaske mai cike da mafarkai barkatai ya 蓷aukeshi....

A hankali ya fara bu蓷e idanunshi sakamakon hasken rana da ya 蓷an shigo ta window 蓷in dakin,da sauri ya gama bu蓷e idanun yana mai tasbihi da tsarkake sunan Ubangiji ganin karfe shida ta yi, Jabeer zai iya cewa tunda ya mallaki hankalin kanshi sallar asuba bata ta蓳a kubce masa ba matu茩ar yana halin lafiya sai yau...idanunshi ya sau茩ar a kanta, tana kwance a jikinshi kamar yadda ya sakata tun jiya bai jin ko motsi ta yi,hannu ya sa ya shafa saman fuskanta yana 蓷an murmushi ka蓷an ka蓷an,a can kasan ma茩oshi ya ce, "Pretty!"

Mar mar ta farayi da idanu, tun kiran sallar farko idanunta ke bu蓷e sakamakon sabo da tayi na tashin asuba suyi sallah a gida da kuma baccin rashin sukunin da tayi, sai dai yadda zata tashi daga jikinsa ne ya zame mata matsala dan wani irin masifaffen kunyar shi takeji.

Zare hannunshi ya yi daga kanta a hankali ya fara kokarin mi茩ewa,jin ya sake ta Maryama tayi wani irin juyi sai gata a karshen gadon,kamar rufe ido ta mi茩e da sauri ta sau茩a saman gadon ta ma茩ure jikin gini tana ta zare ido kamar tayiwa sarki 茩arya, dogayen laps nata farare sol Jabeer ya bi da kallo dariyan abin da tayi na cinsa amma ya danne, bin inda yake kallo na yi da ido....zaro ido nayi gami da kwalla 茩ara da karfi na durkushe a wajen ina ha蓷e jikina waje 蓷aya....Jabeer could'nt help it sai da ya yi dariya,sannan ya mi茩e ya fita 蓷akin ganin matu茩ar ya ci gaba da zama sai 8 zaiyi sallah.

A gaggauce ya cika bokiti da ruwa da kuma babban buta ya shiga bayi. Sai da ya gabatar da uzurinsa sannan ya yi wanka kamar yadda ya saba safe da dare kana ya janyo butar ya fara wankan tsarki baiyi niyyar kusantar ta ba har sai ta saba dashi kuma ta amince masa, amma yana son ya cire kunya a tsakaninsu dan samun happy home shiyasa yai mata abin da yai jiya,sai dai da 茩yar ya iya controlling kanshi....


Babban towel da ya shiga dashi ya 蓷auko gami da goge jikinsa ya saka wata boxer daban ya fito,yana shiga 蓷akin fittt ya ga gilmawarta ta fice a guje kamar wal茩iya shafa kanshi ya yi yana 蓷an murmushi,.....har Jabeer ya idar da Sallah Maryama bata shigo ba, ita ko tana ma茩ure bakin kofa ta 蓷auro alwala tun 蓷azu amma ta rasa yadda zata shigo dan wani irin kunyar shi da take ji mai ha蓷e da 蓷an tsoro tsoro.

Da hanzari jabeer ya cire jallabiyar da ya yi sallar ya rage daga shi sai singlet da boxer ya na 茩o茩arin fitowa ita kuma ta yi shahadar kutsa kanta cikin 蓷akin,karo suka yi ba tare da kowannensu ya kula ba da hanzari ya ri茩o ta ya bata wani irin hug yana sauke ajiyar zuciya, hannunshi ya 蓷aura saman gashinta duk da sanye take da hijab babba, ya na shafawa murya a sha茩e ya ce, "Morning my angel how was your nyt?hope you enjoy it?".

A hankali yake maganar kuma kusa da kunnena, ga ri茩on ba zatar da ya min hakan yasa jikina sakewa sai dai duk da mutuwar da jikina ya yi na Hamma Jay ya fi nawa dan yadda muryarsa ta koma da yadda kafafunsa ke rawa suna son kaimu 茩asa.

Da wannan raunin da ya samu na yi amfani yana gaf da 蓷ora bakinsa saman nawa na hanka蓷a shi na shige 蓷aki a guje na ma茩ala sakata dan na san ko na sa makulli a banza ne zai bu蓷e kamar dai jiya. Zama na yi a bakin gadon ina sau茩e numfashi sama sama tsakanin jiya da yau duk sadda hamma Jay ya ta蓳a jikina sai in ri茩a jin tamkar an jona mun electric shock haka kuma gabana ya dinga fa蓷uwa, the worst part of it kuwa shi ne I like the feeling da na ke ji duk sanda muka samu body contact 蓷in, ya Salam! na fa蓷a ina dafe goshi na.....

Jabeer dake jin kanshi yana yawo a sararin samaniya, baiyi aune ba yaji ta tureshi akayi dace kuma gaba 蓷aya karfin shi ya koma kanta hakan ya sa ya yi baya baya ya fa蓷a saman kujera mai zaman mutum 蓷aya dake gefensa da gudu ya ga shigewarta 蓷aki. Ba haka yake so ba so ya ke suyi zama mai aminci zama mai cike da sha茩uwa da soyayya. Bai son yadda take nuna ta na jin tsoron nan nashi ko ka蓷an. Amma ta ya zai cire mata tsoron? 蓷an murmushi ya yi yana shafa kanshi jin wani tunani ya fa蓷o mishi a hankali ya kwantar da kanshi jikin kujerar ha蓷i da lumshe idanu. Sauri ya ke dama yanason yin exercise ko ka蓷an ne amma gaba蓷aya Maryama ta kwance mashi notinan jikinsa bai jin zai iya ta蓳uka wani abin azo a gani ko da ya fita ma.

Jabeer na zaune a wajen doing nothing bai san iya adadin minutes da ya kwashe ba ya jiyo sallamar fatima, sai da ya maida jallabiyarsa sannan ya amsa labulen palon ta 蓷aga ha蓷i da shigowa bakinta 蓷auke da wata sallamar.

"Ina kwana Hammanmu,"

Cewar Fatima lokacin da ta ke du茩awa kasa.

"Lafiya lau Fati ya su Innarmu, ina baffa da su daada? Ya amsa ha蓷i da tambayarta fuskarshi 蓷auke da murmushi.

"Duk lafiyansu. Innarmu tace in kawo muku abin karyawa ta fa蓷a tana matso da kular da ta shigo dashi tare da tea flask....

Still smiling Jay ya ce, "ki ce da Innarmu mun gode mi茩ewa Fati ta yi har ta kai kofa sai kuma ta juyo ta ce, "Hamma Jabeer Ina antynmu?".

"Antinku ta na wani aiki ka蓷an a ciki idan ta fito zan fa蓷a mata kin zo".

Da "to" ta amsa kana ta ta koma gida...Bu蓷e food flask 蓷in ya yi yaga doya ce aka soya da kwai sai kamshin spices ke tashi tea flask 蓷in kuwa tea ne a ciki as he expect shima sai tashin 茩amshin su ginger ya ke yi. A gefe ya musu mazauni ya daga ledar jiya da dare da ba wanda ya ta蓳a ya fitar da kayan shayin suma ya ajiye a gefe ledar kazar kuma ya fita da ita zuwa kitchen. Girki ba ba茩on abu bane ga duk 蓷an talakan da ya je jami'a, dan haka Jay ya fara 茩o茩arin warming kazar luckily kuma da akwai stove mai cike da kerosine a cikin kitchen 蓷in da Innarmu ta siyawa Maryama komai yana zaune a muhallinshi dan haka kunnawa kawai ya yi ha蓷i da 蓷aukan karamar tukunya ya 蓷aurayeta sannan ya jefa kazar a ciki.....Bayan mintuna ka蓷an ya samu plate ya juye yasa wata ya rufe saman namar ya shigar 蓷aki ya kuma dawowa ya 蓷auki wata tukunyar madaidaici ya cika da ruwa ya mayar saman stove 蓷in ya rufe wasu plate din guda biyu, fork, knife, da kuma cup ya dauka suma ya shigar 蓷akin....anan tsakar 蓷akin ya jere komai yadda ya ke so sannan ya nufi bakin kofar murya 茩asa 茩asa ya ce.

"Pretty fito kiyi breakfast gashi nan Innarmu ta turo mana favourite food na ki" Ina zaune bakin gado bayan na gabatar da sallah counter ce a hannuna ina azkar duk abin da ya ke ina jinsa lokacin da Fati ta shigo ji nayi tamkar in fito in rungume ta amma na kasa saboda tsoro da kunyar hamma jay da nake,...sosai ya Jabeer ya ke ma ta magiya kan ta fito su karya amma ko gezau Maryama ba ta yi ba kasancewar yana son zuwa can gida kafin Baffanmu ya fita yasa shi dawowa kan breakfast 蓷in ya 蓷eba komai yadda zai iya ci ya ha蓷a shayi ya fara karyawa a ransa yana aminta da shawarar da zuciyar shi ke bashi wanda ya ke ganin ita ce hanya 蓷aya tilo da zai cire wannan tsoron a tsakaninsu. A gurguje ya gama ya maida kayanshi da ya cire jiya dan ba wasu kayan a nan dole sai ya je gida ya 蓷auko akwatinsa bakin kofar ya kuma dawowa pleadingly ya ce, "Plsss Pretty ki fito ki yi breakfast ni fita ma zanyi don Allah karki zauna da yunwa plsss wife ya 茩are da sassanyan muryar da wanda ya ta蓳a tsintan kanshi a irin wannan bahagon soyayyar ne kawai zai iya karantar abin da ke zuciyarsa.

Har ya juya xai fita sai kuma ya dawo cikin nutsuwa ya ce, "Da akwai ruwan wanka a kan stove na 蓷aura miki kar ki manta dashi kero ya 茩are, ki fito plssss ni zan fita yanzu, byeee take care of your selfff.

Tun da ya fara magana na ajiye counter 蓷in hannuna ina jinsa amma na kasa furta komai time da ya ce ya 蓷aura min ruwan wanka a take naji idanuna sun cika da hawayen da ban san dalilinsu ba, ba tare da na shirya ba hawayen suka fara sau茩a haka kuma banyi tunanin sharesu ba, inajin fitar shi kusan da minti ishirin still ina zaune ga wani irin yunwar da ke kwa茩ular yan hanjina ba dan na shirya ba na fito. Komai yana nan yadda ya barshi da sauri sauri na ha蓷a tea mai kauri na ajiye gefe na 蓷auki doya yanka biyu hannuna yana rawa na bude plate 蓷in kazar dake ta tashin kamshi. Duk da dai ta fara sanyi amma ban kula ba na fara mata cin yunwa ina bi da shayi Kamin in ankara sai kasusuwa na gani dan haka ban samu cin doyar ba na mayar cikin kula.

Kwanukan na tattara na fitar inda aka tanada musamman dan wanke wanke a gefen kitchen nan na ajiye su kular doya da ta shayin kuma na mayar kitchen na adana. 


Ganin ruwan da ya 蓷ora sai tafasa take yasa ni juyewa a babban flask na 茩ara 蓷ora wani. Baho na 蓷auka da kwando nazo na wanke yan kwanukan da sukayi datti na shigar na jere komai yadda ya kamata sannan na dawo 蓷akin duk da babu datti na 蓷an kakka蓳e sama sama na fesa freshner take ko ina ya 蓷auki kamshi. Ina turo baki gaba na 蓷aga farar jallabiyar shi dake tashin kamshin mayataccen oud dinnan na linke kana na sama mashi wajen zama a bedroom. 


Sai da na tabbatar komai ya min yadda na keso sannan na je na juye ruwan na shiga wanka,....lokacin da na fito har shabiyu ta kusa mai na shafa da 蓷an turare sama sama na shirya cikin riga da siket na wani atamfa blue black sosai farar fatata ta haska aciki, tunanin Sadeeq da Siyama na ma茩ale a raina kana gefe guda kuma tunanin inda hamma jay ya tafi nake yi.

A hankali na 蓷aga gefen katifata na 蓷auko wayar, ina 茩o茩arin kunnata dan kiran Sadeeq naji ana kwa蓷a sallama a waje da hanzari na 茩ara turata kasan gadon na fito ina amsawa wasu mata ne su biyu da yaransu kusan biyar suka shigo saida na isar dasu 蓷aki muka gaisa na fahimci ashe makwafta ne suka shigo ganin 蓷akin amarya. 

Kamar sun bu蓷e kofa ne, nan jama'a suka dinga 蓷i蓷蓷ikowa wai da sunan ganin 蓷aki tuni sun 蓳ata min sharar da nayi, har bayan azahar wasunsu na nan musamman yara. Kamar daga sama Allah ya turo min su Fati da Salima 蓷auke da wata kular ta abincin rana..Fati ce tayi karfin halin korar yaran bayan ta basu sauran doyar safe da ya rage da tea tare muka ci abinci da yan 茩annena da nake ji tamkar na shekara ne ban gansu ba. 

Bayan mun gama salima ta wanke kwanukan da muka 蓳ata fati kuma ta hau shara da mopping har da su kunna tiraren wuta a burner take gida ya 蓷au kamshi da walkiya sak na amarya, a bakin su fati na ke jin wai hamma jay sun fita da baffanmu wani waje tun da safe har fitansu basu dawo ba....sai maghrib su fati suka tafi suka barni cike da kewa Duk yadda na so su tsaya sai ya dawo 茩i suka yi da dabara ma suka gudu na shiga wanka lokacin a darare na shige 蓷aki da zan murza makulli naga wayam sakata ma an cireta, Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un na furta ina zare ido.

Wa ya ta蓳a kofar nan,? ko dai akwai aljanu a gidan nan. Zaro ido nayi na dawo palo da gudun gaske, sai dai bazan iya fita waje ba da kyar na gabatar da sallar maghrib wacce bansan ko abin da na karanta a ciki ba tsabar yadda nake tsorace ina cikin wannan halin aka kira isha shima na gabatar ba tare da ina cikin nutsuwa ba. 

Wani irin kuka ne ya kwace min na fara kukan a hankali hankali cike da tsoro na jima ina kuka har kaina ya fara ciwo sosai amma ba Hamma jay ba dalilinsa. Wajajen karfe takwas na dare ya nufo gidan hannunsa 蓷auke da ledar kazar da ya siyamata da kuma fresh milk, a ransa yana tunanin wane hali ta ke dan yasan Maryama da 蓷an karen tsoro kamar farar kura, ana sallar isha suka dawo daga inda sukaje da baffa tafiya mai cike da nasara cikin farin ciki ya shigo gidan dake mamaye da duhu dulum wayar hannunshi ya haska lokacin da ya iso bakon kofar palon, wani irin 茩amshi ne ya ziyar ci hancinshi gefe 蓷aya kuma ya na jin sheshshsekan kuka sama sama,da hanzari ya fa蓷a palon yana dallare tocin wayarshi,tana ma茩ure jikin kujera akan sallaya idanunta sunyi jawur tsabar kukan da ta ci,."Pretty" ya ambata da 蓷an sanyin murya ka蓷an, tun da ya haska toci ta kara dam茩e jikinta dake rawa waje 蓷aya tana ayyana shikenan tata ta茩are bataji shigowar shi ba sai hasken toci ta gani so ta 蓷auka wani abune daban, jin muryarshi yasa ta tasowa da gudu ba tare da tunanin komai ba ta rungumeshi gam gam tana sakin wani sabon kuka mai cike da shagwa蓳a.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.