Free chapter · Read without an account
Chapter 7
WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha
@umsar Arewapen
Wattpad: Umma Mustapha
PAGE 7
Kwanaki suka ja, lokaci yana tafiya a hankali, yayin da rayuwar Nihla ke ci gaba da sauya salo.
Yaya babbah,ya samo mata mai lesson domin ya taimaka mata wajen shirya jarabawar JAMB da take gab da rubutawa.
Saboda haka, Nihla ba ta samun hutu sosai.
Kullum cikin karatu take.
Da safe karatu.
Da rana karatu.
Da dare ma, idan ta samu dama, sai ta sake komawa kan litattafanta.
Babban abin da yake ƙara mata ƙwarin gwiwa shi ne burinta na shiga jami'a Zai cika.
Tana son taji me ake ji a cikin jami'ar.
Hafiz da Fa'iz za su daina samun damar tsokanarta da cika mata Baki akan jami'a, Basu da aiki kullum sai labarin school , to itama yanzu zataje taga me akeyi a jami'ar.
"Allah ya sa na samu admission kawai," takan faɗa a ranta.
Amma abin da Nihla ba ta sani ba shi ne...
wata sabuwar rayuwa ce take gab da buɗe mata ƙofa.
Rayuwar da ba ta san za ta zo da farin ciki ko da hawaye ba.
Burin shiga jami'a ya zama kamar wata ƙofa da take gabanta, amma har yanzu ba ta san abin da ke bayan ƙofar ba.
A haka dai aka ci gaba da tafiya har lokacin rubuta JAMB ya yi.
Ranar jarabawar ta zo.
Nihla ta shiga da fargaba, zuciyarta cike da addu'a da kuma tunanin zata ci ko zata fadi, a haka dai ta rubuta jarabawar.
Tun daga wannan ranar, jira ya fara.
Kullum tana jiran a saki sakamako.
Kullum tana addu'a.
"Ya Allah, Ka sa na samu."
Wannan ce addu'ar da ta fi yawan maimaitawa.
Sai ranar da aka saki sakamakon ta zo.
Nihla tana zaune ne lokacin da Jafar ya kira ta a waya.
"Yar baka, ki turo min email address ɗinki da password ɗinki."
Ta tura masa ba tare da wata magana mai yawa ba.
Daga nan ta zauna tana jiran tsammani.
Mintuna suka ja.
Sai kusan rabin awa ya wuce.
Wayarta ta sake ƙara.
Jafar ne.
Ta ɗaga.
"Hello?"
"Albishirinki, Yar baka!"
Nan take zuciyar Nihla ta yi wani irin tsalle.
Cikin ɗoki da son jin abin da zai ce, ta amsa:
"Goro!"
Jafar ya yi dariya.
"Goro kawai? Sai kin bani tukuici kafin na faɗa miki."
Nihla ta tabe baki.
"Yaya Jafar, don Allah ka faɗa min."
"Ke dai kina da sauri. Sai kin yi min godiya tukuna."
"Na gode mana!"
"Wannan godiyar ce?"
"Yaya Jafar!"
Dariya ya yi.
Sai da ya gama zolayarta, sannan ya ce:
"Ki kwantar da hankalinki. Sakamakon JAMB ɗinki ya fito, kuma ya yi kyau sosai."
Nihla ta yi shiru.
"Na samu nawa?"
"270."
Na ɗan lokaci Nihla ta kasa magana.
Kamar ba ta yarda da abin da kunnenta suka ji ba.
"270?"
"Eh, 270. Yarinyar nan kin yi abin kirki."
"Alhamdulillah!"
Muryarta cike take da farin ciki.
Ta ɗaga hannayenta sama.
"Alhamdulillah, Ya Allah!"
Ba ta tsaya a ɗakin ba. Nan take ta miƙe ta fito da sauri tana neman Hajiya Mama.
"Hajiya Mama!"
Muryarta ta cika gidan.
Hajiya Mama da Baba Jummai suka juyo suka kalleta.
"Me ya faru kuma?" Hajiya Mama ta tambaya cikin ɗan firgici.
Nihla ta tsaya gabansu, fuskarta cike da farin ciki.
"Na samu!"
Hajiya Mama ta kalleta.
"Kin samu me?"
"JAMB!"
Hajiya Mama ta yi murmushi.
"Da gaske?"
Nihla ta gyada kai.
"270!"
"Alhamdulillah!"
Hajiya Mama ta cika da farin ciki.
"Na tayaki murna, yarinya. Allah Ya taimaka. Allah Ya dafa. Allah Ya sa ki zama abin alfahari."
"Ameen, Hajjajuna," Nihla ta amsa cikin murmushi.
Farin cikin Nihla ya kasa ɓoyuwa.
Baki ya ƙi rufuwa.
A ranta kawai take:
"Zata zama 'yar jami'a!"
Sai dai...
rashin sani ya fi dare duhu.
Nihla ba ta san abin da ke jiranta a bayan wannan farin cikin ba.
Ba ta san cewa wannan admission ɗin da take murna da shi zai zama farkon wani babi da zai sauya rayuwarta gaba ɗaya ba.
Da ta san abin da ke tunkararta, da watakila ba murna za ta yi ba...
sai dai ta zauna ta yi kuka.
Dare ya yi.
'Yan mazan gidan suka dawo, suka hallara a falon kamar yadda suka saba.
Hayaniya ta cika gidan.
Hirar tasu ta karkata kan jarabawar JAMB da Nihla ta yi.
Kowa sai tsokanarta yake.
"270? Wannan ba Nihla ba ce fa!"
"Wallahi mai lesson ɗin nan ya cancanci a ba shi kyauta."
"Yarinyar nan za ta bar mu ta zama 'yar jami'a kenan!"
Dariya ta tashi.
Hafiz kuwa bai bar damar ta wuce shi ba.yace
"Yanzu fa Yar Jami'a zaki zama saura kizo ki damemu da iyayi."
Nihla ta yi masa harara.
"an fada maka kowa irinkane."
"Ku ji ta!"
Dariya ta sake tashi.
Har Fa'iz da ba ya ƙasar ma sai Hafiz ya kirashi ta video call.
sai hirar ta ƙara armashi.
"Fa'iz, ka ji result ɗin Nihla?"
"Na ji mana. 270."
"Yarinyar nan kina wuta fa!"
Fa'iz ya yi dariya.
"sai ki dage kar kije ki kwaso kaya."
Nihla tace, " bani da lokacinka ".
Dariya ta barke a falon.
Suna cikin wannan hirar ne Yaya Babbah ya shigo.
Nan take wasu suka rage muryoyinsu.
Jafar ya ɗauko takardun Nihla ya miƙa masa.
"Ga result ɗinta."
Yaya Babbah ya karɓa.
Bai ce komai ba.
Ya zauna ya fara nazarin takardun.
Idanuwansa suna bin rubutun ɗaya bayan ɗaya.
Sai ya tsaya.
SULE LAMIDO UNIVERSITY, JIGAWA.
Ya sake karantawa.
Jigawa?
Fuskarsa ta ɗan sauya.
Ba wai baya son Nihla ta yi karatu ba ne.
Akasin hakane.
Yana son ta yi karatu, ta samu ilimi, ta zama abin alfahari ga iyalinta.
Amma abin da yake damunsa shi ne nisan wurin.
Bai taɓa son Nihla ta yi karatu a wani gari mai nisa da gida ba.
A matsayinta na mace, yana ganin gwara ta kasance kusa da su.
Ta je makaranta.
Ta dawo.
Su san inda take.
Su san waɗanda suke tare da ita.
Amma yanzu babu yadda zai yi.
Ta nemi admission a Kano, ba ta samu ba.
Ga shi kuma wannan ce makarantar da ta samu.
Yaya Babbah ya sake kallon sunan jami'ar.
Sule Lamido University, Jigawa.
Abin da ya fi damunsa shi ne...
Ba su da wani dangi a Jigawa.
Babu gidan wani da zai ce ta je ta zauna.
Wannan yana nufin Nihla za ta zauna a hostel.
Kuma wannan tunanin shi ne ya fi damunsa.
Ya san Nihla.
Ba ta da rawar kai.
Ba ta cika shiga cikin mutane ba.
Ba ta da yawan ƙawayen da za suke zuwa nemanta.
A gaskiya, idan aka tambaye shi yawan ƙawayen Nihla, zai yi wuya ya iya ƙirga su.
Sai dai jami'a ba gida ba ce.
Sabuwar muhalli ce.
Sabbin mutane.
Sabbin ƙawaye.
Sabbin abubuwan da bai san yadda za su kasance ba.
Yaya Babbah ya sauke ajiyar zuciya.
Babu abin da zai iya yi yanzu face ya bar ta ta tafi.
Ya bita da addu'a.
Sannan kuma yana da wasu abokai a makarantar.
Zai tuntube su.
Ya roƙe su su riƙa kula da ita.
Ya tabbatar da cewa ba a bar ta ita kaɗai ba.
Da wannan tunanin ya miƙe.
Takardun Nihla har yanzu suna hannunsa.
Ya kalli yaran gidan na ɗan lokaci, sannan ya ce:
"Ku ci gaba da zama lafiya."
Daga nan ya yi musu sallama ya fita.
Sai dai babu wanda ya lura da irin kallon da ya yi wa takardun da Kuma sauyawar yanayinsa kafin ya tafi.
Nihla kuwa tana ganin wannan admission ɗin a matsayin mafarkin da ya kusa cika.
Ba ta san cewa akwai wani abu da ƙaddara ta riga ta shirya mata ba.
Ba ta san cewa tafiyarta zuwa Jigawa, ba tafiyarce da za ta kasance ta neman ilimi kawai ba.
A can ne rayuwarta za ta fara ɗaukar wani sabon salo.
A can ne za ta haɗu da mutanen da ba ta taɓa tsammanin za ta sani ba.
A can ne wani sabon babi zai buɗe a rayuwarta...
Babin da zai zo da farin ciki, da ƙalubale, da sirrika da ba za su tonu da sauƙi ba.
Amma a wannan lokacin, Nihla ba ta san komai ba.
Abin da ta sani kawai shi ne-
ta samu admission.
Kuma a zuciyarta, farin ciki kawai take ji.
Sabuwar rayuwa ta kusa farawa.
Umsar ✍️
***