Free chapter 路 Read without an account

16

by Anisa Muhammad Yahaya 路 NUFIN ALLAH


馃挄 NUFIN ALLAH 馃挄 
By
Anisa Muhammad yahaya 


Page 1锔忊儯6锔忊儯

Neman su aka fara yi dan bada kyauta.
Tashi sukayi suka tafi inda sauran students din suke

Amba nabila award na punctual and obedient student and best in biology 

Ita Kuma Jalila na neatest student and best in chemistry 

Anisa Kuma best student in all calculation subjects and the most nicest and obedient student 

" Uhmmm kaga nicest student, ga neatest a kusa da ita"
Yayi maganar yana kashewa da dariya ya 茩ara cewa

"Allah basu san award din me suka baku ba ke Anisa ke din ce nice, duk wannan shegen tsiwar taki, ke Kuma neat su neat anji jiki, daman ita nabila i know she's obedient ta cancanci award 蓷inta"

Yafa蓷a yana kashe wa nabila ido, ita dai sunkuyar da kanta tayi tana murmushi dan harga Allah ya Ahmad na bata dariya a times

Ita dai Anisa hararar shi tayi bata ce komai ba dan jinta take duk a takure, saboda tana jin idon shi na yawo akan ta Amman ta茩i ta kalli inda yake

Jalila ce ta ce
"To ya Ahmad me kake nufi am not neat Ko me" ta fa蓷a tana wani murgu蓷a baki 

"Matar da se ki fi kwana 2 da the same kaya shine wani neat"
Ammah ta fa蓷a tana 蓷an dariya

"Kaiii Ammah pickles din tawa" fa蓷in Anisa tana supporting Jalila 

"To meye banbancin daga ke har itan ai duk kanwar ja ce" fadin Ammi 
"Ai duk haka suke sedai shiriya kuma"

Ahmad ne ya kalli nabila yace 
"Kema haka"
Kunya ya bata kawai ta ja hannun Anisa tace kuzo muje wajen su Maryam 

Duk tashi sukai suka bar gurin, 
shidai Umar ko uppan bece ba saidai ido daya kure Anisa dashi Amman ta茩i ta juyo ma ta kalle shi, kuma yasan tana jin kallon nashi tunda ga alamar ta takura Amman ta茩i kallon nashi,

Shifa gaba 蓷aya ji yake kamar yayi hauka a gurin, kawai maintaining yake yana composing kanshi kar yayi wani abun, saboda ganin wannan na kusa dashi din ya kureta da ido har yanzu

Har sun 蓷an yi nisa ka蓷an daga inda su Ammah suke Amman suna iya hago su wannan wanda ya zauna kusa da ya Umar ya 蓷an sha gaban su

"Heyyy dear, sunana Habib kefah"
Ya kalli Anisa Yana maganar 

Ita dai ko kallon shi batayi ba ta fara jan hannun nabila dake kusa da ita

"Ki tsaya mana, ki samun phone numbern ki mana ko gaisawa ne mu ringa yi" yayi maganar yana mi茩a mata wayar shi, bata amsa ba ya kara cewa
'' wallahi beautiful kina da kyau sosai fah, irin na mind blowing 蓷innan''
茦o茩arin kara shigewa sukayi ba tare da ko kallon shi tayi ba amma 蓷an anacin ki ya kara tare gabanta
'' tun kuna stage nagan ki kuma gaskiya kin tafi da imanin Habib ki taimaka ki saka mun numbern Please !!!!!!'' ya ja kalmar Please 蓷in yana marairaice fuska cike da barikanci, cikin za茩uwa da 蓷an hasale dan gaba 蓷aya yanayin shi be mata kama da kamilallen mutum ba tace
 
"Malam plea.."
 Bata karasa maganar ba taga an kwace wayar dake hannun shi anyi jifa daita wani gefen
Juyowa tayi taga waye yayi jifan suka ha蓷a ido da Ya Faruq 

"Kun bar gurin nan ko sai na 蓳alla ku, dan rashin sanin ciwon kai ne zaki wani tsaya kina ma irin wa'anan mazan magana, wallahi na 茩ara ganin ki kina ma wani magana a gurin nan sai na karya ki, ku wuce ku bani guri, nonsense tsabar baku san ciwon kanku ba wuce ki bar idona in dai na ganin ki kafin inyi 茩asa 茩asa dake yanzu"

Yaja tsaki yana wani watsa ma gayen mugun kallo,

Saurin barin gurin sukayi jikinta na 蓳ari ta ri茩e hannun nabila gam kamar zata karya ta dan duk saninta dashi ba abinda ke ha蓷a su bare akai ga irin wannan fa蓷an sedai ta hanga yanayi Amman be ta蓳a mata irinsa ba se yau da taji kamar ta sume a gurin ki ta saki fitsari dan yanda idon sa sukayi ja har jijiyar kansa na tashi

Tun sanda Habib ya tashi ya nufi inda suke zuciyar sa ce dukan uku uku, kasa daure wa yayi sanda yaga zasu tafi ya 茩ara shan gabanta har yana wani mi茩a mata banzar waya,shi idan ba idonsa ke mai gizo ba gani yayi kamar ma amsa zatayi tana washe ma sakaren baki

Su Anty basu Ankara ba sai sanda sukaga yana cilli da wayar wani
"Kai Ahmad yaushe Umar ya tashi daga nan" fa蓷ar Ammah 

Shima saida ya 茩ara juyawa ya kalli inda yake zaune da inda ya gan shi yanzu

"Wallahi ban sani ba Anty nima saida kika yi magana nayi noticing"

"Malam lafiya zaka jefar mun da waya"

"Last warning zan maka, she belongs to me and only me, karka bari musa 茩afar wando 蓷aya, dan bazaka ji da da蓷i ba, kabar wajen nan yanzu dan zan iya illata ka idan ina ganin banzan face dinka" ya fa蓷a yana wani huci kamar wani murucin zaki

Shima ganin yanayin face 蓷in ya Umar din ne yasa be biye mai ba bare ya mai nashi kalar haukan dan yasan a duke se Faruq ya jibgi ukun shi ba ma iya shi ka蓷ai ba dan a murde yake shiko gashi bushashshe a gurin kamar an daura wa mucciya zani dan dai kawai ba laifi yana da 蓷an kyau

 tafiya yayi ya barshi a gurin zuciyarsa na mugun ta fasa, wani jaki mara sense dashi zai so yana wani kure abinda yake mallakin sa da kallo, belonging dinshi fah, she is his and only his, baayi wani bayan shi ba, he even have the guts da zai yi mata magana

Ji yake kamar ya harbe shi ya huta ko zai 蓷an samu sassaucin abinda yake ji sedai duk abinda ze faru daga baya ya faru

Ammi ce tace ma ya Ahmad ya kira su jalila su zo su tafi

Bayan ya kira su ne suka fito zasu tafi, daman ya Umar ma da mota yazo 

Sudai sun san ko karen hauka ya cije su ba abinda zai shigar dasu motar shi barin ma yanda yake a fusacen nan

Hanyar motar Ya Ahmad suka nufa, har sun kai bakin kofa suka ji Muryar shi

 "ku shiga wancan, su Ammi sai su shiga wannan"

Hantar cikin Anisa ne ya ka蓷a, dan itafa a tsorace take bare ga yanda ya mata wannan fa蓷ar dazu kamar zai cinye ta, sai tayi dauriyan cewa

"Amm yah tunda sun riga da sun je bakin motan mu Bara mu shiga nan tare da Anty"

Wani mugun kallo ya watsa mata har zaiyi magana kawai ya fasa yayi kwafa

A fusace ya bude motar ya shiga suma su Ammah suka shiga ya ja motar

Gashi ba damar ya ja motar da gudu tunda su ammi ne aciki bare ya rage takaici da 蓷acin zuciyar da ta 茩unsa mai a yau dinnan, ai da ta shigo motar nan yau duk wani kwandon bala'i da rashin mutuncin dake cin shi seya juye mata shi tass 

Wani uban kwafa ya buga da seda amma dake zaune a side din shi ta kalli shi, kafin ma tayi magana Ammi ta rigata da fadin

'' wai babban yaya me aka maka ne yau gaba 蓷aya naga kamar ranka a 蓳ace, yanzu kuma kana ha蓷e mana rai harda buga kwafa..''


___________________
By
Anisa Muhammad yahaya 馃尯

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.