Free chapter 路 Read without an account
Chapter 29
by MARYAM STAR 路 茒AURIN ZUCI
***
饾樋饾樇饾檺饾檷饾檮饾檳 饾檿饾檺饾樉饾檮馃攼
饾樈饾檾
饾檲饾樇饾檷饾檾饾樇饾檲 饾檸饾檹饾樇饾檷
Chapter 29
Da taimakon wasu samari biyu dake wajen aka sakata a mota, kuma kamar 蓷aya daga cikinsu yasan bazai iya tu茩in ba sai ya kalle shi tare da fa蓷in.
"Oga naga kamar a rikice kake kawo inyi driving 蓷in akwai wata 茩aramar privet asibiti anan sabon layi SAHEL CLINIC sai muje can kawai." Babu musu ya sauka tare da yiwa matashin godiya ya koma mazaunin me zaman banza ya dafe kan shi da hannuwa bibbiyu.
Emergency aka nufa da ita direct tare da soma bata taimakon gaugawa har aka samu aka cetota ta farfa蓷o daga suman da tayi.
Waya Junaid ya 蓷auka tare da turawa Uncle guntun massage.
'Karkujini shiru ina hospital na ka蓷e wata and nima bana jin da蓷i.'
Bayan ya tura ya nemi ganin likita jiri na kwasar shi, yasan de ya zauna akan kujera bayan wanda ya tu茩o shi ya taimaka ma shi ya ri茩e hanun shi gani kamar yana jin jiri, daga nan bai sake sanin inda yake ba.
UNCLE
"Wallahi Fahad na soma gajiya da halin Junaid ana tausaya ma shi amma sam shi baya tausayawa kan shi, ka duba ka gani sarai yasan halin da muke ciki shi ne yake 茩o茩ari 茩ara jefamu a wani yanayi." Ya fa蓷a 蓳acin rai na bayyana a muryar shi.
Nisawa Fahad ya yi tare da jinjina al'amarin Junaid sannan cike da son fahimtar da Uncle ya ce.
"Dani da kai duka munsan waye Junaid, baya ta蓳a yadda yayi abin da yake kuskure ko cutarwa ba tare da wani babban dalilina.
Mi yasa idonka zai rufe akan abin da kasan gaskiya ne, ka fi kowa sanin waye shi, kamar yanda kafi kowa sanin hali da 蓷abi'ar shi, kasan ba zaka goya ma shi bayaba akan abin da ya saka gaba mi yasa zaka saka ya dawo 茩asar nan, 茩asarda yayiwa kan shi al茩awari akan bazai sake waiwayarta ba, 茩asardata zama silar 蓷aure zuciyar shi da tarin raunuka, ya kamata ka dinga waiwayen abubuwan da suka faru a baya, shin ka mance tarin abubuwa da muhimman aiyukan daya baro acan Dubai yazo nan duda yayiwa kan shi al茩awarin bazai sake takowa Nigeria ba???."
Fahad ya fa蓷a shu蓷a蓷蓷un lamurran da suka faru a baya suna dawowa dalla-dallah a kwanyar shi.
"Lock Fahad wannan ba hujja bace da zai yi amfani da ita wajen cusa kan shi a abinda ya kasance hatsari ga rayuwar shi, shin kasan maganar wa yake, kasan shirin shi ana tunkarar azzalumin mutumin can ne, ko kasan har yanzu bai cire Muhammad daga ran shi ba."
Ya fa蓷a a 蓷an hasale.
"Wane mutumi ne zai tunkara?
Sannan akan wane muhammad kake magana, and minene shirin shi na gaba da ni ban saniba?."
Fahad ya fa蓷a a蓷an rikice yana 茩o茩arin daidaita nutsuwar shi waje 蓷aya ta hanyar hana kan shi yarda da tunanin da ke yawo a kwanyar shi.
"No Fahad ka gazkaga tunani da zuciyarka abin da kake 茩o茩arin 蓳oyewa shi nike nufi shin har yanzun kana ganin laifin ko har yanun kana tunanin banyi ma shi adalci ba, shifa 蓷an uwanmu ne tare muka taso tun 茩uruci miyasa bazanji zafi ba idan 茩addara mummuna irin wacce ta auku a rayuwar shi, kana tunanin zai iya ha茩ura da bibiyar abin da ya faru tun shekarun baya, kana tunanin shiru da kuma nisan da yayi zasu tashi a banza, to tabbas kayi kuskure domin kuwa ni nasan waye Junaid kuma nasan abin da zai iya aikatawa, na tsani ala茩ar shi da wannan yaron Muhammad na tsani du wani abu da zai dangantasu da juna na tsani sha茩ar numfashin da yake yi a doron 茩asa shi蓷in annoba ne kuma fitina ne."
Uncle ya fad'a ran shi na kuma 'baci."
"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'um, Allah kai kad'ai muke da a wannan yanayin Allah ka karkatar da hankalin d'an uwanmu daga fuskantar abinda ya ke 'kalubale a rayuwar shi, Allah ka sau'ka'ka zuciyar shi ka sassauta ma shi rad'ad'i da azabar da ya kwashe shekaru a cikinta." Fahad ya fad'i hawaye na gangarowa daga idon shi saboda tuna mummunan abin da ya faru da su a shekarun da suka shud'e.
Hawaye ne suka 'ballewa Saminaka lokacin da yake jiyo firar su, tunda maganar shi ta d'auke bai ta'ba jin takaici da damuwar hakanba sai a yau da aka zo wajenda maganar shi keda muhimmanci amma kuma babu baki, da ace yana da ikon magana daya kirasu sun matso kusa da shi sannan ya ce musu.
"Muhammad da Fahad ku rabu da Junaid yayi abin da ya dace a lamarin nan, domin kuwa yafiku gaskiya da hangen nesa, shi zai iya hasashen abin da zai faru saboda yanada basira, ko babu komi yana fafukar neman warken maganin dam'bareren ciwon da ke zubda jini ba dare ba rana a zuciyar shi, ni da shi muna cikin wani yanayi da ba kowane zai gane hakan ba sai mu da abin ya shafa, ku daina shiga ralurran shi kuna yin kane-kane kawai kubi shi da addu'ar fatan alkairi da fatan nasara."
Amma yanzu ba hali babu yalin da zai yi musu bayanin da zai gamsar da su.
Tunanin sanda rayuwar shi ta fara ya soma yi da kuma yanda ta kai shi matakai mabanbanta har zuwa yanayin data dawo da shi a yanzun.
WANENE SAMINAKA?
MIYE ABINDA YA FARU DA RAYUWAR SHI CAN BAYA???.
ku cigaba da kasancewa tare da ni domin warware muku asalin zaren labarin.
****
Numfashi ha蓷e da huci 茦waro ke saukewa yana jin tsananin bu茩atuwar son kasancewa da abin da yake ba halilinsa ba.
Wata arniyar dariya ya saki tuna abin da zai iya faruwa da MAKAFA muddin ya tarwatsa wannan bangon sihirin, da hannun shi yayi amfani wajen yi tsafi ya hasko MAKAFA.
Kwance ya ke yanata faman tari wanda ke fita tare da ba茩in haya茩i, da alama ba iya shi ka蓷ai ba hatta da halittun kan shi suma sun ta蓳u wanda hakan ke nuni da tabbas akwai 茩alubale a lafiyar makafan.
Nisha蓷i ne ya bayyana a kan fuskar 茦waro yana ji a ran shi ankusa isa matakin da yake jiran a je, ya kusa nunawa MAKAFA har yanzu yana 茩asa da shi.
"Yanzun wasan zai Fara Abdullahi Makafa ganinka a haka na bani nisha蓷i tare da tunatar da ni yanda na shigo da kai rayuwata."
Ya fa蓷a hotunan abubuwan da suka shu蓷e na dawowa tar akan shi kamar yanzu ne abin ke wakana.
TUNA BAYA
WAYE 茦WARO
WAYE MAKAFA?
MADARASATUL TA'AZIMUL ISLAM.
Shahararriyar makaranta ce ta addini wacce tai fice da suna a cikin garin Katsina unguwar Malan Niga, makaranta ce data kafa tarihi me tsawo, domin kuwa anjima ana yin karatu a cikinta kasancewarta makarantar allo ta almajirai.
A wata ranar lahadi da marice wani ba茩i 茩irin 蓷in almajiri ne raku蓳e jikin bango yana share gwalla, yayinda 茩afar shi ke fitar da jini jikin shi kuma du 茩asa da alama fa蓷a suka yi.
Wata 茩erarriyar mota ce 茩irar golf da ake ji da ita a zamanin tayi parking kusa da rumfar makarantar da almajirai keta haramar shirin zama karatun bayan sallar azahar.
Cak wannan almajirin ya tsayar da kukan da yake yi tare da yin wani irin yun茩uri ya nufi wajen motar kan shi tsaye ya saka hannu ya bu蓷e jikin shi na 蓳ari.
Kallon daga sama har 茩asa Senator Mansur Ashiru yabi ba茩in matashin yaron da shi, zuciyar shi na 茩issima ma shi wani abu na daban game da matashin yaron.
"Ranka ya da蓷e dan girman Allah ina neman taimakonka, ko aikin kakka蓳e motocinka ne ka bani."
Almajirin ya fa蓷a idon shi kafeM akanMM Senator Mansur Ashiru.
Isowar malaminsu ne ya saka yaron tashi tare da ja da baya har lokacin bai daina kallon sanata ba.
Sun 蓷auki lokaci suna tattaunawa tsakanin malam da Sanata Mansur wanda suke magana yana hangen wannan yaron.
Almajirin da ake kira da Audu ya koma gefe ya raku蓳e yayinda ya kafe motar da ido ko 茩iftawa baya yi.
Kuma da Malaminsu yazo ma shi da wani batu wanda ya wanke zuciyar shi fes, saboda tsabar zumu蓷i ko jakar kayan shi bai tsaya 蓷aukaba kamar yanda Malam ya ce, duda yace ma shi aikin na蓷an lokaci ne zai dawo, amma ya saka a ran shi idan ya tafi ya tafi kenan yanda baya 茩aunar wannan karatun baiga abin da zaisa ya dawo makarantarba bayan ya samu fredom, shi ko baiyi aiki a gidan sanata ba indai har yabar makarantar nan tofa bu茩atar shi ta biya.
Ya so ya tsaya sanda wani daga cikin yaran sanatab ya fincike shi tare da janyo shi baya, amam sai tattaurar zuciyar shi ta茩i bashi ha蓷in kai sai ya bangaje matashin ya fa蓷a cikin motar yana zare 茩ananun jajayen idanuwan shi dakw 茩ara ma shi muni.
Nan matashin yahau zagin shi yana tada jijiyoyin wuya kamar zai kai ma shi mangari amaa sai Sanata ya hana ya tada motar tare da saita madubi a saitin Audu yana kallon shi time to time.
Koda suka isa gidan Sanata Audu ya sauko bai wani tsaya 茩arewa gidan kallo ba saboda hakan baya gaban shi, babban burin shi shine ya aiwatar da 茩usurin shi cikin gaugawa ya 茩arawa wandon shi isa, idan yana waje aka yi ajiya bai sata ba hannayen shi sun dinga 茩ai茩ayi kenan bai samun salama sai yayi dabara ya sace abun nan, inyaso daga baya bai damuba du irin hukuncin da za'ayi ma shi.....
Ka蓷an kenan daga cikin tarihin MAKAFA DA 茦WARO yanzu zamu soma asalin labarin kuci gaba da kasancewa tare da ni.
Wannan page 蓷in na masoya novel 蓷ina ne masu like da comnent harma da masu taya ni da share ina mayu茩ar godiya sannan ina alfahari da ku馃挭馃檹馃徎.
MARYAM STAR.