Free chapter 路 Read without an account

Chapter 32

by MARYAM STAR 路 茒AURIN ZUCI

***

***

饾樋饾樇饾檺饾檷饾檮饾檳 饾檿饾檺饾樉饾檮馃攼
         饾樈饾檾
饾檲饾樇饾檷饾檾饾樇饾檲 饾檸饾檹饾樇R



Chapter 32.
JUNAID
     Yana iya jin yanda numfashin shi ya soma dawowa sannu a hankali, har ya daidai zuwa lokacin ne kuma ya dawo hayyacinsa, sannu a hankali ya soma bu蓷e idanuwan shi da yake jin sun yi ma shi nauyi sosai, ya sauke shi akan ya sauke su akan  fankar sama da ke jujjuyawa tana bada iska, iskar da yake ji tana shigar har cikin 茩ofofin gashin jikin shi, tana saukar da sanyi.
    "Sannu Junaid, mike maka ciwo ne, bara in inje in kira Doctor ya 茩ara dubaka." Uncle ya fa蓷i yana juyawa ya fice da sauri.
   "Sannu Brother."
Fahad ya fa蓷a tausayin halin da yake ciki kwance akan fuskar shi.
    Kallon shi Junaid yayi da idanuwansa da suka 蓷an shige ciki, a hankali cikin sassanyan sauti ya ce.
    "Fahad wa kuka baro wajen Abeey naga kai da Uncle a nan??." Ya fa蓷a yana kafe Fahad 蓷in da idanuwansa da suka yi rauni sosai.

    "Ai Mommy ta dawo gida jiya, and ta tabbatar min da zata kwana biyu bata fita ba,  kuma a wajen Daddyn na barta kafin infito." sai kuma ya 茩ara da fa蓷in "Yanzu na zo babu jimawa dama ina son duba yanayin da kake ciki, amma yanzu zan koma gidan in sha Allah."
     Junaid nan take gaban shi ya fa蓷i jin Fahad ya ambaci Mommy, laluben dalilin da zaisaka abarota ita ka蓷ai wajen Abeey 蓷in shi ba, kai tsaye ya ce da Fahad.
    "Fahad tashi ka koma gida please nima yanzun zan taho."
   Babu musu Fahad ya mi茩e tare da fa蓷in.
   "Get well soon bro, bye." ya fa蓷a tare da mi茩ewa ya ture kujerar baya ya doshi 茩ofar fita.
     Kusan karo suka ci da Uncle daya sanyo kai biye da shi Doctor ne.
   "Yauwa Fahad gida zaka koma ko?."  Unle ya tambaye shi yana shigowa ciki.
    "Ih Uncle yanzu zan koma, Allah ya bashi lafiya."
   Ya fa蓷a a ta茩aice tare da ficewa.
    Motar da yazo ya ita ya kunna ya shiga, sai ga 蓷ora kan shi a kan setiyari ya yana jin zuciyar shi na 茩unci akan abin da Junaid da Uncle ke yi na rashin yadda da Mommy, kai tsaye basa nunawa amma yanda sam basu yarda da ita ba abin na sosa zuciyar shi kuma yana jin babu da蓷i sosai, koba komi ai mahaifiyar shi ce kodan yanda yake son su tsakani da Allah  bai dace ace sun ri茩e abin da ta yi shekara da shekaru ba, wanda zuwa yanzun ya kamata ace ya wuce.
   Tada motar yayi ya fice daga asibitin, tun kafin ya isa gida ta soma nuna ma shi alamun babu wadatacen mai, hakan ya saka ya rage gudu sosai ya dinga tu茩i a slow har ya iso 茩ofar get 蓷in gida, kasheta yayi tare da yi mata key ya durfafi get 蓷in yana rayawa a ran shi dole yayiwa Uncle magana akan 茩arewar da mai yake da wuri yanzu kuma ba'a cika lura ba wannan shi ne karo na biyu daya fita da mota mai ya 茩are ma shi a hanya.
   Da mamaki ya ke knocking amma still 茩ofogin duka da 茩arama da get 蓷in a  kulle, ganin zai 蓳atawa kan shi lokaci sai ya janyo waya ya dannan kiran layi security 蓷in da ke gadi, a ran shi yana mitar yanda Junaid ya tarkato su suka dawo Katsina, Katsinar da tsarin gidajenta sam basu yi ma shi ba.
     Wani tsaki ya doka sanda me gadin ya tabbatar ma shi ai Mommy ce ta aike shi, shi da driver, a fili ya ce.
    "Kai Mom ko problem daga dawowarta zata sa a fara issue tafi kowa cika ciki wallahi."
    Ya fa蓷a yana lalibo key 蓷in daya amsa tare dana mota a hannun Uncle, cikin sa'a ya samu Extra key wanda Uncle 蓷in baya rabo da su, ya bu蓷e 茩aramar 茩ofar yana jinjina nauyin da take da shi da kuma 茩o茩arin da Security ke yi wajen bu蓷ewa da kullewa.

    Lokacin daya kama handle 蓷in gami da bu蓷ewa sannu a hankali cikin nutsuwar da ta kasance adu wani aiki na shi, sam baya da hayanida da kwaramniya barshi dai da surutu amma ko wajen magana baya da 蓷aga sauti, komi na shi a sau茩a茩e kuma asanyaye ya ke, da ace yasan abin da zai gani kenan da tun farko ya fasa shigowa nan 蓷in ya haura sama ya watsa ruwa, saboda abin da yake ji na saka ma shi tashin zuciya wato warin asibiti warin Izal da sam baya so.
      Ba iya jinin jikin shi ba hatta da 蓳argon dake tsakiyar 茩ashin shi yana jin yanda yake daskarewa da tsananin tashin hankalin abin da ya gani, Mommy, Mommyn shi daya rasa dalilin Junaid na tsanarta bayan babu abin da ta aika ma shi, idan ma abin da ya faru ne a baya ai ba laifinta bane ita ka蓷ai kuma ai kuskure ne aka samu.
     A yanzun da yake kallonta tana aikata mummunan abu sai ya tsinci zuciyar shi da fatan ba wannan bane dalili, kar wannan abin ya zama dalilin tsanarta da Junaid yayi.
   Zai iya rantsewa da ba akan 茩afaguwan shi yake takawa ba, saboda sam baijin wani abu na motsi a jikin shi, kawai de ya tsinci kan shi yana tafiya kamar akan iska tsabar ru蓷ani da tashin hankalin daya shiga.
    Duka hannayensa biyu ya saka, ya ture    kwalbar glashin da take zu茩ar jinin shi tana zubawa a ciki, nan take kwalbar ta fa蓷i 茩asa  ta tarwatse  jinin cikinta ya soma malalewa yana sauya siffa daga kalar shi ta jah zuwa ba茩in haya茩i ya soma tashi yana sama, yayinda kwalbar ta shiga narkewa a 茩asan wajen.

    Da wata iriyar razana Mommy ta saki allurar hannunta sanda ta juyo da nittar 蓷ura jinin data zu茩o na 茩arshe, sai ta yi tozali da Fahad tsaye a bayanta cikin wani kalar yanayi me wutar fassarawa....
   Baya ka蓷an.

Yau tun asubahi Mommy ta dawo daga tafiyar kasuwancin da tayi, lokacinne kuma Fahad ya fito da zummar fita masallaci anan suka yi clash shi da ita, da tsananin mamaki ya ke kallonta tare da fa蓷in. "Mommy saukar yaushe, karde kice min yanzu kika iso?." ya fa蓷a da mamaki yana kallon motarta dake fake a harabar.
   "Ih Son yanzun nan na sauka wallahi kwanan hanya muka yi ai, ina sauran 拼an uwan naka ne?." ta fa蓷a tana le茩en bayan shi kamar tana neman su a wajen.
   A ta茩aice ya ce da ita, "Ya Jay ba lafiya yana hospital Uncle yaje ya kwana da shi nima dana dawo sallah zanje na dubo shi kafin Daddy ya tashi tun jiya naso zuwa amma Uncle ya hana ni saboda Daddy." ya fa蓷a a gaggauce jin an haramar tada sallah.
    "Okay yanzu ai zaka iya zuwa ni sai in kula da Daddyn naku tunda na dawo Allah ya bashi lafiya." Ta ga蓷a wani yanayi na gilmawa ta cikin idanuwanta.
     Bin bayan Fahad ta yi da kallo har sai da ya fice sannan ta koma motarta da sauri ta 蓷auko wata jaka ranta 茩al zata aiwatar da aikinta cikin sau茩i ba tare da zullumi ba.
    
Sai da ta tabbatar da Fahad ya 蓷auki mota ya fice daga gidan sannan ta 蓷auki kayan aikinta ta shige 蓷akin Saminaka ta taradda shi kamar yanda aka haska mata shi, hankali kwance ta soma gudanar da aikinta kiran wayarta da aka yi ne ya tsaida ita, ko kusa bata tsammaci dawowar Fahad nan kusa ba bare da aka ce Junaid ne ba lafiya, kuma sai da ta 蓷auke hankullan duka 拼an gida bayan ta aiki driver da security saboda bata son kowa ya shigo gidan sai ta gama aikinta....
    Cigaba.

Wata iriyar jijjiga Saminaka ya soma yi ba茩in haya茩i na fita daga bakin  da hancin shi, lamarin da ya 蓷auke hankalin Fahad kenan daga kan Mommy ya koma wajen Daddynshi da ke fizge-fizge yana wani irin nishi da gurnani me tsoratarwa.
   Da wannan damar    Mommy ta yi amfani taja jakarta ta fice ba tare da saninta ba tayi mantuwa, mantuwar da zata kawo 茩arshen wani abu, abu abu me muhimmanci a rayuwarta.
    Kuka Fahad ya fashe da shi tare da 蓷aga Daddy ya rungume shi yana kuka kamar ran shi zai fice zuciyar shi na matse a ir茩in shi, yayinda kwanyar shi ke hasko ma shi yanayin da yaga Mommy 蓷in da kuma zarginta daya 蓷arsu a ran shi.
    'Sanye ta ke da jajayen kaya, gaba 蓷aya jikinta inka cire hannuwanta da suka fito ta cikin faffa蓷an hannuwan rigar, hatta da fuskarta a rufe take sai bayan da ta juyo zata zuba jinin sannan ya ganta gaba 蓷ayanta.

Ba wanna bane babban abin da ya firgita shi, kalaman da ya ji tana ambatar kamar me karanto wani abu, kalamanda lokaci 蓷aya suka tayar da tsigar jikon shi, wannan kalaman nata sune suka 茩arfafa zargin shi, sannan kuma 蓷ibar jinin da take ba abisa 茩a'ida ba taya zata 蓷ibi jinin Daddyn da yawa har hakan bayan jiya Doctor ya ce jinin jikin shi ya 茩one da yawa gana bu茩atar a dinga 茩ara ma shi jini after two days, kuma a lokacin sai da ya kirata ya sanar da ita kawaide besan zata dawo ba a yau.'
     Kukw ya ci gaba da yi cikin kullewar kai babu abin da yake sai sake matse kan Daddy a 茩irjin shi akamr zai maida shi cikin shi, sam bai damu da amai me warin da Daddyn ke zazzaga ma shi ba.

     Sannu a hankali yake takawa bayan sun sauka daga motar, juyawa baya yayi tare da yi ma matar alama akan ta shiga gaban.
    Cikin tafiyarta a hankali ta 蓷an matsa kusa da su amma bata shiga gabansun ba kamar yanda ya so.
    Lumshe ido Junaid  yayi, sannan ya bu蓷e suka cigaba da tafiya shi da Uncle, a main parlor Uncle ya yi mata alama data zauna, shi kuma yabi bayan Jay daya nufi 蓷akin Saminaka.

    Cak su duka biyun suka tsaya ganin abin da ke faruwa a wajen, kafin suka zabura lokaci 蓷aya zukatan su na harbawa suka doshi wajen su Fahad a zafafe.
    "Subahanallah." Jay ya furta tare da tsugunawa a wajen ya na kama 茩afar shi 蓷aya da yaji wata arniyar azaba na huda shi, 茩urrr ya bi 拼ar 茩aramar farar kwalbar data daki lallausar fatar tafin 茩afar shi, nan take ta soma narkewa tana 蓳acewa, ba茩in jini nayo tsartuwa daga wajen.
    Azabure ya mi茩e tare da sanne 茩afar ya 茩arasa wajen Abeey ya taimakawa Uncle suka 蓳an蓳are kan shi da 茩yar daga  茦irjim Fahad, suna raba su Fahad yayi  luuuu baya tare da fa蓷uwa kamar marar rai.
    "Ruwa please Uncle." Junaid ya fa蓷a tare da kallon Fushar Saminaka da wani ba茩in jini keta fitowa ta hancin ci, wani haya茩i kuma na fita daga bakin shi.
     A ki蓷ime Uncle ya 蓷auko goran ruwan zamzam wanda aka tofe da ayyatush shifa ya kawowa Jay a rikice.
     Da bisimillah Junaid ya kafawa Samminaka goran ruwan a baki wannan duda wannan ba茩in haya茩in bai daina fitowa ba.
    Caraf saminaka ya soma ha蓷iyar ruwa domin kuwa a yahayin zafin da yake ji a cikin jikin shi babu abin da yake da bu茩ata irin ruwa wata茩ila ya sassauta ma shi azabar data addabi gangar jiki da ruhin shi.
    Da janye robar ruwan da Junad ya yi da kuma tahowar wani 茩a茩茩arfan amai da Saminaka ya yi, bai wuce 茩yastawar ido ba.
    Ri茩e a cikin hannayen Junaid ya dinga kwarara wani irin ba茩i 茩irin 蓷in amai me tsananin wari, kuma marar kyawun gani.
    Idasa rikicewa Uncle ya yi du dauriya irin ta shi ya gagara ri茩e kukan daya taho ma shi sai kawai ya du茩e a wajen tare da  soma rera kukan shi da dukanin 茩arfin sautin shi.

     Lumshe ido Junaid ya yi tare da jingina Saminaka da jikin shi yana jin yanda hucin da naman jikin shi ke yi ke dakar fatar shi da sam bata son zafi.
    "Its okay Uncle, finaly ya amayar da komi by now he is fine."
    Ya fa蓷a cike da comfidance.

   Yun茩urowa Uncle yayi da azama yana zare idanuwan shi tubarikallah ya ce. "Are you sure, stop ...."

MARYAM STAR...

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.