Free chapter 路 Read without an account

33

by Anisa Muhammad Yahaya 路 NUFIN ALLAH

https://www.arewapen.com/book?id=6aa58fbdf7af357fd59c9f87

***

馃挄 NUFIN ALLAH 馃挄 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA

Under team yota's amazing pen

Page 3锔忊儯3锔忊儯


Bayan auren malam Ali da rukayya papi ya bashi gida da aiki a Company 蓷in shi saboda yana da diploma a computer engineering 

Wannan lamarin sai da ya haifar da 茩aramar fitina tsakanin papi da sahura, da kyar ya iya yiwa idon shi kwalli ya tsaya kan 茩afarshi baza'a kar蓳a gidan ba, dan ita aikin da ya bashi ne kai gidan daya bashi tayar mata da hankali ba, koda tace ayi auren nan ba wai dan rukayya ta ji dadi bane, so take taje ta cigaba da shan wahalar rayuwa a gidan ma ba wai so take taje taji da蓷i ba

lamarin da har gurin hajja Saida yaje, ita ce ta tsawatar wa abun dan badan tsufa ya cinye ta ba da ta da蓷e da ma lamarin sahura tufka, dan itama ba daga nan ba, ba ta 蓷aukar shirme da shiritita ko ka蓷an, rashin lafiyar da take fama dashi ga hawan jini ga kuma ciwon 茩afa, 茩aramin hauka ne sahura kawai bata ma papi ba akan wannan lamarin, kuma ba yanda ta iya dan tana bala'in tsoron 拼ar tsohuwar nan, shiyasa tana ji tana gani, Ahaka dai zancen ya lafa,

Bayan shekara biyar da auren su, abubuwa na tafiya daidai, sun samu daidaito da fahimtar juna da sha茩uwa tsakanin ta da mijinta,

Rayuwa suke cike da jin da蓷i da walwala,suna son junar su, Amman har lokacin Allah bai basu haihuwa ba 

A lokacin juwaira ta gama secondary ta fara zuwa kasu, tana level 4 sauran 1 year ta gama

Suma su muneefa da muneef suna level 2 

Adam da hafeez kamar wasa suka cike wani scholarship na studying a Cairo university, Kuma duk su biyun sun samu tare da wani abokin su shima, su kusan bakwai suka yi applying Amman su uku suka samu, dan suma dai basuyi tunanin zasu samu ba

architecture Adam yayi applying Kuma shi ya samu, shi kuma hafeez mechanical engineering, duk course 蓷in nasu 4yrs course ne 

Yanzu sun ci 2 yrs da 拼an kai baifi 1 and a half ya rage su gama su dawo ba

Suna zuwa gidan uncle abdallah idan suna free anan Adam ya saba da jannat 拼ar gidan uncle abdallah Wanda itace ta biyu a gurin shi bayan Yusuf babban 蓷an shi, su biyu ne yaran shi kawai 

Wani rana ne sunje gidan gaida umma da Ganin sauran 拼anuwanta dan tun sukayi aure baifi sau hu蓷u taje ba saidai ko idan sun zo

Suna zuwa tayi sama hanyar parlourn umma , maganganu take ji da alamar shashshe茩ar kuka kuma Muryar shaheeda ne umma ita kuma nata balai 

shiga tayi, taga shahida zaune kan kujera jikinta du shatin duka, umma na kanta sai masifa take kamar ta auri baki ita kuma sai kuka take zubawa

"Ai wallahi Bazan yarda Ba ai ba cewa nayi bana sonki ba da zasu jibgeki kamar jaka ba ko wata mara gata, wallahi bazata sa蓳u ba, kuma wallahi sai ya sake ki tunda shi bai da ta ido baida daraja, bai.."

Ganin zancen nata ba 茩arewa zai yi ba yasa ta 茩ara yin sallama tana cewa

"Umma ina wuni, meya faru haka, shaheeda meya faru"

"Wannan laanannen mijin nata ne mana, dukanta yayi kamar wanda ya aike jaka da ta kai 茩ara itama uwar shi da 茩annen shi suka ha蓷u suka mata duka wai tana musu rashin kunya, jaka suka samu da zasu dakar mun 拼a, ko saboda ba su suka haifar mun ita ba basu san ciwon rasa ta ba, idan suka kashe mun ita zasu iya mun madadin ta ne"

Duk zuban nan da take wa rukayya ta manta ita wani hali ta saka yaran wasu abaya Amma yanzu tazo tana tada jijiyar wuya dayake nata ne

Akace ranar naka se naka, duk abinda shahida da umma suka mata abaya Saida taji tausayin shahidar Dan ta ko蓷e ta rame ga fuskarta wurin gefen idonta ya loma alamar naushinta akayi ga bakinta ya kumbura

Kamar ba wannan 拼arkwalisa masifaffiyar yayarta ba, itama zama tayi tana 茩ara bata hakuri umma tace

"Daman fa ba tun yau ya fara ba, ashe 蓷an giya ne sai yayi ma茩il yazo ya mata zagin 茩are dangi wai dan kudin shi kawai ta aure shi da sauran su, yanzu kuma harta kai 拼anuwansa ma su daketa, dan ban ta蓳a magana ba, to wallahi bazai yuba"

Mamaki da tsoron Allah ne suka cika ran rukayya dan wannan abinda ta shuka ne ta fara girba akan 拼arta ka蓷an da ka蓷an....

follow and like for more update 馃グ


______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 馃尯
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol