Free chapter 路 Read without an account

36

by Anisa Muhammad Yahaya 路 NUFIN ALLAH


馃挄 NUFIN ALLAH 馃挄 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA


Page 3锔忊儯6锔忊儯


Bayan sun dawo gida ne Uncle Munir ya zaunar da ita ya fara mata nasiha sosai 

"Kiyi hakuri Rukayya kiyi hakuri, nasan ke macece mai juriya da hakuri, kiyi tawakkali karkiyi tunanin dan kin rasa mijin ki da mahaifin ki lokaci 蓷aya Allah baya sonki ne, ko baya ganin halin da kike ciki, duk son da kike musu ya fiki sonsu, lokacin da zasu zauna dake a duniya ne ya 茩are, ke ma wata rana haka lokacin da wasu zasu zauna dake zai 茩are, bazance ki daina kuka ba dan kuka rahama ne idan kika yi zai sau茩a茩a Miki zuciya, zai rage Miki wani miki, Allah ya amshe mijin ki amman ya bar miki 蓷a ko 拼ar da zaki ringa tunawa dashi, inda yaso zai iya ha蓷awa gaba 蓷aya, ya 蓷auke miki mijin da kuma a binda ke cikin naki amman se ya bar miki wanda zaki ringa kalla kina jin sanyi a ranki, ya dauke miki mahaifi amman ki na da 拼an uwanki, wanda suma kika gansu zaki tuna shi har ki mai addu'a, kina da wasu iyayen duk da ba'a maye gurbin uwa da uba amman muna tare daku a kowani lokaci, kiyi hakuri ki 茩ara hakuri kinji Rukayya ba abinda zai faru a rayuwa batare da wani nufi na Allah ba, sai kiga wani wuyan 茩arshen shi yayi da蓷i, kagama shan wahala amman sai kiga duk ya koma labari, ko a Yanzu ke kanki misali ce, danAllah kiyi hakuri kiyi tawakkali, karki sawa ran ki damuwa da yawan da zai cutar da lafiyar ki ko 蓷an dake cikin ki"

Kuka take yi sosai so take ta yi juriyar da Abba Munir ke fa蓷a amman takasa, hannunta takai cikin ta tana tunanin da ace Abhie yana raye sai yafi Kowa farin ciki da haka

Ada itace me damuwa, shi ke kwantar mata da hankali yace da ita 

"Indai muna da rabon ganin jinin mu Rukayya zamu gani, ki daina damuwa Allah na sane da mu bayinsa a koda yaushe"

Bayan rasuwar da Wata biyu ne su Juwaira suka dawo Kano da zama dan cema Baba tayi bazata iya zama a wani 茩asar 拼ar uwarta na wani waje daban ba

Tunda yanzu ba wanda ta ke da ya茩inin zai kula mata da ita yanda ya dace

Da farko Baba so yayi Ammi ta dawo gurin su da zama amman ta ce bazata koma gidan 茩anwarta da zama ba itama tana da gidan mijinta 

Yanda Amma ta tada mai hankali yasa shi dawowa Kano saboda akwai branch dinsu acan

Koda suka dawo juyin duniya Amma tayi ta dawo su zauna gida 蓷aya amman ta茩i lokacin Ammah na goyon Jalila da bata wuci 10 months ba 

Itama lokacin Anty Muneefa nada Nabila ita kuma kusan 7 months 

Ran Ammah ne ya 蓳aci jin yanda Ammi ta茩i yarda, ta kira Daddy ta fa蓷a mai shine ya nemi gida a Kano kusa da inda Ammah take ya siya

Shima dai da kyar ta koma Kanon dan da cewa tayi tafison ta zauna Kaduna gidan da mijinta yake 

Saida suka nuna mata 蓳acin ran su har Anty Zuhura suka ha蓷a ta da Abba Munir tukuna kafin ta amince ta koma 

Ammah na zuwa dubata akai akai dan kusan kullum tana gidan, shi yasa Ahmad sukayi sabo da Ammi sosai dan duk weekend Yana gidan anan yake ma zuwa tahfeez, Ammah tana hakan ne saboda kar a ringa Barin ta ita ka蓷ai a wannan halin 

A haka wani ziyara da su Daddy suka kawo ne bayan sun je Kano ya siya wani fili dake kusa da gidan Ammi ya ha蓷a da gidan da ya zama shine ya shiga tsakanin filin da gidan Ammin ya gyara gidan yace idan sun zo hutu sai su ri茩a sauka a gidan 

Da suka zo tafiya ne Umar ya sa kukan ba zai je ko ina ba, shi so yake ya zauna a wajen Ammi, kuma daman sun sha茩u da abokin sa Ahmad dan shine babban abokin shi tun kafin su bar Egypt 

Itama Ammi rokon su tayi subar mata shi dan Umar yana da shiga rai

Mommy ce tace ta ri茩e shi har sai ta gaji dan itama a lokacin tana fama da kanta tanada tsohon ciki kusan 6 to 7 months

Bayan ta haihu akasa ma jaririyar suna Anisa Wanda Umar ne ya za蓳a mata sunan

Saboda yanda tun sanda aka haife yarinyar yake sonta kullum tana 茩an茩ame a hannun shi duk rashin son shi da yara, banda ita yanda yake hade rai kuwa idan za'a amshe ta se kayi mamaki, bacci ko cin abincin kawai ke rabashi da yarinyar, ko abincin zata ci yana zaune har tagama a dawo mai da ita

Shine da ake tambayar Ammi wani suna takeson a sa mata tace ya za蓳ar mata suna

Kallon jaririyar yayi duk da ba fara bace amma black beauty ce, be ta蓳a Ganin black Jaririya ba, sai akanta ya saba da ganin yaran Larabawa farare, amma ita wannan ba茩a ce, gata kuma kyakkyawa, yana son abu mai kyau kuma special, kuma tun lokacin yaji ta shiga ranshi

A hankali sanyayyar Muryar shi ta furta Anisa!! ya kalla Ammi yace 

"Ammi a saka mata Anisa"
"Kasan meaning din sunan" Ammi ta fa蓷a tana kallon shi dan itama sunan ya mata

Kai ya jinjina mata alamar eh yace
"Yana nufin friendly and affectionate"
 "Are you feeling so affectionate to her"
Anty ta tambaye shi tana 蓷an dariya 

"Ehmana Anty shiyasa naga ta dace da abunda nike ji akanta sunan yaje da ita"

Dariya sukayi duka Amma tace 

"Anisa ba nickname bane"
"Aa suna ne me zaman kanshi buh mutane suna sakawa a nickname amman suna ne na gaskiya"

Fa蓷in Mommy wadda duk tare suke harda su Momma Zuhura, suma su Usman na zaune gefen shi ya hana su jaririyar ko su Antyn ma suna 蓷auka ba jimawa zai je ya amshe ta kamar shi ka蓷ai aka haifa mawa

Ko da yaushe yarinyar na hannun shi, da mutum ya 蓷auke ta ze koma kusa da kai ya zauna ya kafe ka da idanu har se ka gaji ka bashi idan kuma ya ga baka da niyyar bashi ita se ya kai hannu ya amshe ta, shima idan baka bashi ba yayi ta 茩unci kenan yana ha蓷e rai, ko kula shi akayi baze tanka mutum ba ranar, in ko tana hannun shi ai ko su Ahmad 蓷in ma baya biye mawa suyi wasa, har ta fara wayo kodayaushe suna tare, duk rashin son yara na zuwa inda yake wai shi a lallai babba banda ita 

Amman wani abun mamakin duk yanda yake sake mata ita kuma tsoron shi take, kuma hakan ya samo asali ne da tun sanda sukayi wani taro suka ha蓷u yaran suka je suna ta蓳a mai kayan shi, suka mai 蓳ar na sosai, gashi suka shigar mai 蓷aki abinda ya tsana, sun mai kaca kaca da ko ina,
Kowannen su seda ya bi ya zane yasa su punishment ranan yaran ba karamin wahala suka ci ba gashi iya sune a part din ba me ceton su, amman da ita, jalila, fareedah da nabila suka gudu suka buya 茩asan gado shi

Da ya gansu kuwa yace sai sun koma kasan gadon kuma ba zasu ci koda abinci ba sai sanda yaga dama sannan zasu fito, yana ji ana neman su amma yayi biris seda suka kusan awa 3 a kasan gado sannan yace su fito, sun wahala sun gama kukan sauro, ga duhu ga zafi har 蓷an baccin wahala sukayi,
Tun sannan ta fara tsoron shi dan sun wahala a 茩asan gadon nan ba ka蓷an ba, kuma dalilin da yasa suka ha蓷e kansu su hudu kenan suna kiran kansu the P quadruplets, lokacin suka ba kansu suna, ita Anisa pixie, Jalila pickles, Nabila pebbles, se Fareedah pookie 

Shiyasa da taji ance ga babban yayan ku zata nemi guri ta 蓳oye daman gashi Allah ya mata shegen tsoro to balle da ya ha蓷u da yaci zalinta 
Shi kuma gudun da take mai ba 茩aramin harzi茩a shi yake ba, dan duk cikin 茩ananan shi yana ji da ita amma take mai haka shiyasa shima yake share ta

Shekaru sun ja, Faruq ya samu soja ya fara daga rank din lieutenant yanzu currently Yana rank din Major General (MAJ GEN UMAR ADAM BAFFAYO), and Yana aiki a Companyn Daddy dake kaduna dan kafin ma ya samu aikin soja a Company 蓷in yake aiki kuma har yanzu yana aiki a Company 蓷in kawai dai dan yafi son aikin sojan ne ma yafi karkata hankalinsa a can

Usman ke kula da Company 蓷in tunda she ke zaune a Kaduna kuma architecture shima ya karanta, sai dai ko idan Daddy yazo ya ke zuwa 蓷an duba wa, 

Shi kuma Ahmad medicine ya karanta, kuma yana 蓷an ta蓳a business, yanzu ne ma da baba ya bu蓷e nashi a Kano yake kula dashi amman da shi duk wani business be dame shi ba akan aikin shi kawai yayi forcusing




Jama'a baku tambaye ni ya shaheeda, abida da Umma sahura suka 茩are ba,
Se mun ha蓷u a page na gaba idan naga comment 

Follow and like my account on arewapen ba dan halin wannan marubuciyar ba dan Allah 馃ス馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹

______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 馃尯 
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.