Free chapter 路 Read without an account
38
馃挄 NUFIN ALLAH 馃挄
By
Anisa Muhammad yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page 3锔忊儯8锔忊儯
Kallon bedside drawer tayi taga abincin da ta 蓷ibo tun 蓷azu bata ci ba tace
"Ki ci abincin ki kinji Babyn Ammahn ta, kuma ki bar kukan ko so kike Ammi taga idanuwan ki a suntume ta shiga damuwa"
Kai ta girgiza mata
"To share hawayen kinji bar kukan, indai ba alkhairi aciki zaki ga hakan be faru ba in akwai alkhairi ki sama ranki ruwan sanyi dan za蓳in Allah yafi son ran bawa kinji"
Hawayen ta share tace
"In sha Allah Ammah na, Nagode in Sha Allah zanyi hakan dan faranta ran Ammi, dan nasan bazaku ta蓳a mun za蓳in da zai cutar da ni ba"
"Yauwa to 蓷auka abincin ki kici har ya huce ma"
"Bana jin yunwa yanzu Bara dai inje in rufe"
Kafin Amma tayi magana mommy ta shigo da茩in, jin Amma shiru ne ya saka ta bin bayanta kuma taga itama Anisa yau ta茩i zaman parlour tazo ta duba me take yi kuma ta ga inda Ammah take dan akwai abinda take son tambayar ta
"Au ashe kema kina nan, ahah me ya faru take kuka"
"Wallahi kam ina nan, shigowa nayi in duba ta dan naga har tagama girkin bata fito ba sai na same ta tana kukan ciwon kai, banda abin Anisa ma wai ciwo take ma kuka madadin ta nemi magani"
"Kayya ni dai wannan 拼a tawa Allah ya kyauta miki yanzu ciwon kai kike wa kuka to ai madadin ya rake miki sai dai ya 茩ara miki wani ciwon"
Ita dai bata ce komai ba sai kanta da ta sunkuyar 茩asa dan da farko tayi tunanin Amma fa蓷awa Mommy zatayi jin tace kuka take
"To fito muje maybe ma ba kici abincin ba sai aukin kuka da kika zauna yi"
"Aiko kamar kin sani ba abinda taci ai shiyasa na tsaya ina mata fa蓷an"
"To nidai duk ku fito mu je, ban son zaman dakin nan da kuke"
"To Anty Babba"
Fa蓷in Amma jin yanda take magana, dariya Mommy tayi tace
"Ai kin san dai na girme ki daidai kika fa蓷a"
"Koba kin girme ni ba"
"Nidai ku fito muje" ta bu蓷e kofar dakin tana musu nuni da hannu
Plate 蓷in abincinta ta dauko tana ri茩e hannun Amma dan har yanzu zuciyar ta da 蓷an nauyi kuma ha蓷i da jin yanda mahaifiyarta ta rayu abaya, bata ta蓳a sanin haka Ammi ta wahala ba ta dai san idan rashin mutuncin Mamee Abida ya tashi
Sai tayi ta mata gorin ta茩i aure ta zauna zaman kai, ko kuma ta ringa cewa itace silar war gajewar rayuwar farin cikinta, ta zama silar auren talaka da tayi, maganganu kala kala, Ita dai Ammi ba biye mata take ba, saidai idan kuma tayi a gaban Amma sai itama ta mayar mata
Ita kam daman Mama shahida tun sanda Ammi ta ba mijinta ku蓷i ya nemi sana'a dan kudin shi ya kare a shegen shaye-shayen bin mata da caca da yake, a ganin sa yana da ku蓷i dan haka lokacin fantamawar sa ne, gwara yaci duniyar sa da tsinke,
daga baya kuwa da ya samu karayar arziki, ya daina samun na shan giyar ta shi daman bawai sigari yake sha ba, idan yayo cacar tasa idan ya fa蓷i ko bashi da kudi se yazo ya fanshe a jikin ta ta hanyar duka da cin mutunci, ya ha蓷a ta ita da Umma ya zage tass kuma bata da bakin magana
Tun lokacin ya fara Ganin mutuncin Ammi ya rage dukan ta, daman ya 蓷an rage shan giyar tashi, dan ma Allah yasa lokacin Amra da Amina ne dan lokacin ita saudat din bata da wani wayo, Allah ya taimake ta ya dena shan komai, amma ko a yanzu ka ganshi zaka san yana shaye shaye ko ya ta蓳a yi dan duk ya lalace
Kuma Ammi harma da Amma suna yawan taimaka musu, suna 茩o茩arin ganin kan gidansu bai tarwatse ba duk da halin su barin ma Abida dan ita Shahida ta iya makirci da danne abu a rai ko bata so
Duk da abinda suke musu gani suke ai zasu iya musu abinda ya fi haka amma dan mugunta suke basu iya ka蓷an, ga mugun tsana da hassada da suka cusa wa ransu da 拼a拼an su da ba shida amfani sai ma 茩untatawa kan su da suke
Dan shi hassada ga me rabo taki ne, idan kana wa wani 蓷an Adam hassada baza ka tashi ka nemi naka ba saidai kaga ka raba mutum da nashi ko kuma ya ci baya saidai kaga yayi gaba kai kuwa banda baya da lalacewa ba abinda zakayi
Shi yasa bawa ka ringa neman tsari da sharrin hassada dan mugun abune, Allah ya sa mu dace
Parlourn suka fito, hanyar kitchen ta nufa da abincin Mommy tace
"Idan kin maida wannan ki 蓷ibo wani kizo kici dan baza dai kice zaki zauna da yunwa ba"
To tace ta wuce kitchen 蓷in, tana tafiya kamar zata fa蓷i dan har 蓷an har蓷ewa tayi jin yanda ido mai kaifi ke bin ta da kallo har ya shige
Kasa daina kallon ta yayi yana tunanin me yasa ka ta kuka gashi tana tafiyar ma kamar mara lafiya, ji yayi Mommy na cewa Ammi
"Wai yanzu kin san kukan ciwon kai 拼ar nan ta zauna yi madadin ta nemi magani ta sha sai ta zauna yin kuka"
"Ai wani kayan takaicin sai Anisa wani lokacin, abinda bema Kai ya kawo ba zata fara mai kuka kamar wata karamar yarinya, Allah dai ya kyauta" Ammi tayi maganar cikin takaici
Hanyar cikin 蓷in ya 茩ara bi da kallo, 蓷an murmushin gefen baki yayi dan wannan ma na daga cikin abinda yake kara sa yana jin sonta
Abincin ta zuba ta dawo parlourn dan ta ganshi a kan dining kamar ma baida niyyar barin wajen
"Ina kuma zaki je"fadin Amma
"茒aki zan koma"
"A'a kije dining ki ci ina ganin ki kafin ki 茩ara barin abincin baki ci ba"
Fa蓷in Mommy
"Hmm wannan yarinyar da abinci kuma karki wani wahalar da kanki dan ita da abinci ko ka蓷an zata ci har ramuwa take"
Dariya sukayi jin maganar Ammi, ita kam kunya taji ta sunkuyar da kanta 茩asa
Mommy ce tace
"Haba Ammi ramuwa dai, kamar wani azumi"
"Hmm idan fa bata ci da daddare ba ta kwanta da safe wai sai tace ai ta rama na daren da bata ci ba"
Shima kallon ta yayi duk cin abincin shi baya rama wani in be ci ba, gashi dai ba wai 茩iba ta keda shi ba, ko cikin ta ma shafe yake kamar wanda ze ha蓷e da bayan ta, kamar ma wata mara cin abinci, indai ba ka sani ba sai kace bai fi irin masu cin spoon uku ba dan kar a mutu
Amman ace wai itace ke irin cin da Ammi ta fa蓷a, dan dariya ya 蓷an yi me 蓷an sauti yace
"Ci ba 茩iba" baisan a fili ya fa蓷a ba
Sai da yaga ta 蓷ago tana kallon shi tana cuno dan bakin nan nata agurin
Suma su Amma kallon shi suka yi, ganin suna kallon shi ne ya maze ya cigaba da abinda yake kamar ma besan abinda ke faruwa ba balle kace shi ya fa蓷a
Ganin yanda yayi kicinkicin da fuska yasa Amma kama ha蓳a a ranta tace "jimin 蓷a oh ni Juwaira sai yayi abu ya wani maze kamar besan me ake ba, ina ganin abinda ya fi 茩arfi na"
Itama ganin ya wani maze yasa ta 蓷an ta蓳e baki a ranta tana fadin
"Ai dama sai dai idan kuma bashi din bane, mutum yayi abu amman ya wani maze kamar ma baisan anyi ba ko kuma akwai iskar ku ma a wajen"
Please follow and like my account on arewapen ba dan halin wannan marubuciyar ba 馃ス 馃檹 馃檹 馃檹
______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 馃尯
007059822449