Free chapter 路 Read without an account

39

by Anisa Muhammad Yahaya 路 NUFIN ALLAH


馃挄 NUFIN ALLAH 馃挄 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA


Page 3锔忊儯9锔忊儯

Dining 蓷in ta nufa ta zauna daga 蓷an nisa da shi 

Tuwon ta kalla sai kuma ta fara ci, har lokacin tana iya jin idanun shi akanta

Shima warmers din dake gaban shi ya janyo ya saka tuwo 蓷aya ya zuba miyan dan duk zaman da yayi a wurin har su Ammi suka gama suka koma parlour beci ba

 Ammi ce ma tace"ahah Babban yaya kai baza ka ci abincin ba"

"Zanci Ammi bana jin yunwa ne yanzu"
 Shima Ahmad da ya gama sallama ya musu dan ana neman shi

Spoon ya 蓷auka ya fara cin tuwon dashi, 蓷agowa tayi ganin ya ja spoon taga yana ci da shi,
"ikon rabbi tuwo da spoon iyayi dai kawai" ta fa蓷a a ranta

Tana 茩o茩arin kauda kanta ne suka ha蓷a ido, sai ya 蓷aga mata gira yana kai tuwo bakin shi, kai ta juyar tana 蓷an ta蓳e baki

Itafa har yanzu bata gama yarda wannan ya Umar din dai da tasani shi ke sonta ba bama ha蓷i ta ina zata ma far yarda da wannan batun, ita fa bata ga wani alama ba,anya ba iyaye ke ki蓷ar su suna rawansu ba, ba suke son kawai ha蓷a wannan al'amarin ba kuwa

Kallon shi ta 蓷an 茩ara yi, so take taga ko da wata karamar alama ne da zai sa ta yarda shi 蓷in ne 

Rai ya 蓷an ha蓷e jin tana ta kallon shi ya 蓷ago kanshi daga danna wayar da yake daidai yanda ita ka蓷ai zata ji yace

"Nifa ban cika son kallo ba in ba haka ba Tom" ya jijjiga kai yana cigaba da kallon ta ranshi a 蓷an ha蓷e 

Tun suka ha蓷a ido tayi saurin janye wa, jin wai yana cewa baya son kallo yasa ta 茩ara 蓷agowa ta kalle shi, kasa kasa tace

"Amma kai ai ka iya kallo harda na haramun, mutum sai shegen kallon tsiya amman shi wai kar akalle shi'' ta fa蓷a harda wani murgu蓷a baki

Murmushi yaso yayi amman ya maze dan yaji abinda ta fa蓷a ga tana maganar tana wani cuno 茩aramin bakinta gaba

"To ya za'ayi dani, ai mallakina nike kallo ba na wani ba"

Da sauri ta 蓷ago tana kallon shi ya wani maze kamar ba daga bakin shi maganar ta fito ba, idan ba dan tasan Muryar shi ba kuma tasan su biyu ke zaune a gurin sai ta musa shi ya fa蓷a

Dan yanda ya wani 茩ara ha蓷e rai yana danna wayar shi kamar ma besan tana existing a gurin ba sai ta iya rantsewa besan me take ba

"Nace miki bana son kallo koh" ya 蓷ago idanunsa ya saka anata, kauda kanta tayi, ji tayi ma zaman dining din ya ishe ta sai kawai ta mi茩e da plate 蓷in abincin ta tayi kitchen 

Murmushin gefen baki yayi dan shi kansa yasan ba tayi expecting Jin hakan ba, wani tunanin ne ya dawo cikin kanshi,

 Ahmad yafa蓷a mai yanda suka yi da Abba, tunani da fargaba take ya dirar mai karfa ace ta ce bata sonshi,yasan shikenan ya gama, tun jiya yake wannan fargaban amma azahiri in ka ganshi ba zaka ce wani abu na damun shi ba 

Ko 蓷azu daya ganta yayi tunanin ko gudowa tayi dan kar Abba ya 茩ara tambayar ta opinion 蓷inta, shifa besan ta yanda zai Fara bane shiyasa, da ya dade da Kama wannan zuciyar dake wahalar dashi

Karasa cin abincin nashi yayi dan 蓷azu ba wani ci yake ba sai akin kallon ta da yake 

Saida ta gama cin abincin, tana cikin wanke plate 蓷in harta gama zata kife ya shigo, nashi plate 蓷in ya ajje mata a sink 蓷in ya 蓷auki cold water a fridge ya fita bece da ita komai ba, itama bata ce masa komai ba ta 茩ara wanke nashin 

Fitowa tayi ta nufi 蓷akin ta ta kwanta ta rufe idon ta, tana tunanin yanzu koda ta yarda wane irin zama za tayi da shi 

Ganin tunanukan bazasu kai mata bane yasa ta lalubo wayar ta ta cigaba da kallon da take, amman ina ba ma ta fahimtar me take yi se su da take hasaso wa a cikin wayar, kifa wayar tayi akan gadon ta kama kanta tana fa蓷in 
''na banina nikam, banga ta yanda wannan al'amari ze yu ba anya zan iya kuwa, zan iya amincewa kuwa??..''


Follow and like my account on arewapen ba dan halin wannan marubuciyar ba dan Allah 馃ス馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹

______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 馃尯 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol