Free chapter 路 Read without an account

40

by Anisa Muhammad Yahaya 路 NUFIN ALLAH



馃挄 NUFIN ALLAH 馃挄 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA


Page 4锔忊儯0锔忊儯

Ammi ce bayan magarib lokacin Ammah ta tafi ita kuma Mommy ta koma part din su ta shigo ta sami Anisan

Dan daman tun sanda ta zo gidan take jin kamar wani abu na damun ta, abinda ya sa bata tambaye ta ba saboda yanda su amma suka nuna nasu kulawar shiyasa tayi kawaici ta share kamar bata gani ba

Kuma taga alamar tana son ta fa蓷a mata wani abu 蓷azu shiyasa tun lokacin hankalin ta na kanta, zuciyar ta Allah Allah take ta 茩ebe da 蓷iyar tata taji meke damun ta

Zama tayi kusa da ita, ta dafa ta tace
"Me kike son ki fa蓷a mun 蓷azu ne"

Jin abinda tace ne yasa ka ta fara tunanin me zata ce mata dan bata ta蓳a boyewa Ammi komai da ya shafeta ba amman yau zata fara dan ba zata so abun da zai sosa mata ranta ba, bata son abinda ze karya wa mahaifiyarta farin cikin ta hayatyn ta rai

"Amm daman fa Ammi na kasa Bama Abba amsa ne da ya tambaye ni, kuma nasan ko gobe ko jibi zai nemi jin ra'ayina amman ni kunya nake ji shine nake son fa ke ki fa蓷a mai da kan ki na amince"

Fadar kalamar ta amincen ma sai da yasa ta jin wani abu a cikin ranta kamar ta 茩aryata kanta

Dan sauke ajiyar zuciya Ammi tayi, tana jin farin ciki aranta, amman haka kawai take jin ba iya shikenan ba

"Iya shikenan kawai ba abinda yake damunki"
"Me kika gani hayatyna?"

"Gani nayi kamar ba iya maganar dake bakin ki ba kenan"

"A'a Babu komai hayaty na" ta fa蓷a tana rungume Ammin, ita ma rungume ta tayi tana mata adduo'i a ranta

"Ammi na ina sonki sosai, You have gone through alot, Allah ya biya kida Aljanna Ammi na, Allah ya ji茩an Abhie"

Kanta ta shafa hawaye na cikowa idonta tace
"Ameen ameen Anisa ameen, Kuma Allah ya muku albarka yasa ku cigaba da ha蓷a kanku fiye da yanzu, ya baku zuri'a 蓷ayyiba"

Kanta ta kwantar kan kafa蓷ar Ammi tana sauke ajiyar zuciya, ta tabar wannan shine abinda ya dace tayi tana da ya茩inin in Sha Allah wannan ne mafi alkhairin decision da ta yanke ko dan faranta wa Ammin ta rai Allah itama zai duba ta

Zata Fara 茩o茩ari taga ta sanya koda 茩an茩ani ne na son shi kodan Ammin ta, zata rage tsoron da take mai ta kalle shi a matsayin mutum kuma matsayin 蓷anuwanta, yayanta, kuma me 茩o茩arin taka matsayin mi..... Kasa 茩arasawa wa tayi ta lumshe idon ta wani tsoron na 茩ara shigar ta

Wani nannauyar ajiyar zuciyar ta sake saukewa ta lumshe idanunta tana kara rungume Ammi n

Sun 蓷an jima a haka sannan Ammi tace
"An kira isha let's go and pray"

Tom tace tana zame jikinta ta yi toilet, da kallo Ammi ta bi bayanta tana tuna mahaifinta da bai ta蓳a ganin jinin shi ba a doran duniya, itama bata ta蓳a ganin fuskar mahaifinta ba saidai hoto 

Koda suka zo kwanciya Ammi zata tafi Anisa tace so take su kwana tare

"Yau kuma keda idan nace kizo mu kwana kike guduwa idan ba wani tsoron naki ya kawo ki ba"

"To Ammi ai lokacin da ban yau daban, ni dake nike son kwana"

Ko bayan da zasu kwanta, alarm ta saka na 茩arfe 2 na dare, dan ta tashi tayi addu'a kamar yanda tama Amma al茩awari

Da kyar ta tashi wajen 2 din abunka da ba'a saba ba, sallah tayi raka'a 6 tayi adduo'i tayi istikara 

Ammi ce jin motsin ta ta tashi ta ga tana sallah, wani sanyi taji a ranta dan koda akwai dalili, hakan ya nuna mata 拼arta ta fara girma da hankali, ta fara sanin muhimmancin kai wa Allah lamari ba shiritita da shirme da take ba ko zaman kuka

Ko a 蓷azu taji tane kawai da tace ba komai amman ita tasan dole da akwai wani abun, bata tursasa mata ba ne saboda tasan tayi hakan ne dole dan wata 茩ila abin in ta fada mata zai dame ta, shiyasa bata tursasa mata ba karma memakon ta fa蓷a mata gaskiya ta mata 茩arya 

A gurin ta zauna ta cigaba da addu'a daga baya ta 蓷auko Qur'ani ta fara karantawa ba ita ta bar gurin ba sai bayan da tayi sallahn asuba

Tun kafin ta koma bacci taji nauyin da zuciyar ta tayi da fargabar da take akan auren ta da ya Umar na 蓷an yayewa tana jin wani kwanciyar hankali tun bayan ta gama karatun quranin

'' in Sha Allah zanyi zan iya zan cika wa ammina farin cikin ta '' ta fa蓷a a ranta tana kallon Ammi dake zaune kan dadduma 



Follow and like my account on arewapen ba dan halin wannan marubuciyar ba dan Allah 馃ス馃檹馃檹馃檹馃檹



______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 馃尯 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol