Free chapter 路 Read without an account
43
馃挄 NUFIN ALLAH 馃挄
By
Anisa Muhammad yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page 4锔忊儯3锔忊儯
Har suka fito ba wanda kema wani magana in ba Radion da yake ta faman zuba ba
Wayar ta kawai take danna wa, gashi su biyu ne kawai a motar, duk a takure take jin ta
Gani tayi ya karya kwana ya bar kan titin, a Valentino taga yayi parking, kallon shi tayi tana son tambayar shi amma ba dama
Ko kallon ta beyi ba, duk da yaji tana kallon shi, 茩ara ha蓷e rai yayi dan baya son ma tamai magana, dan bai san shima dalilin da zuciyar sa ya janyo shi nan ba,
So yake ya fara gwada abin da Abba yace Mai, so shi yasa ya fara da haka
Fita yayi daga motan bayan ya kashe, ita dai da kallo ta bishi, har ta kama handle din ya rigata bu蓷ewa yana kallon ta
Itama kallon shi tayi bata ce komai ba ta fito a hankali kamar bata so, motar ya rufe suka jera suka fara tafiya
Dan tsayawa tayi saida ya 蓷an yi gaba sai ta fara binshi a baya, dan juyawa yayi ya kalle ta bece komai ba har suka shiga
"Wani flavour kike so" ya tambaye ta yana kallon different varieties na ice creams 蓷in
"Ni na 茩oshi"
"Like how, karki 蓳ata mun rai"
Ganin ya 茩ara ha蓷e ranshi ba kamar sanda suka shigo bane yasa ta pointing chocolate one din
Scooping mata akayi, shima shi yace abashi, zama sukayi a gurin
Cup 蓷in ta tusa a gaba da kallo shima ta 蓷ago ta kalle shi, shan abun shi yake hankalinsa kwance
"Ki sha mu tafi"
茒an spoon din ice cream 蓷in ta 蓷auka tana juyawa amma ta kasa sha
Itafa ba gwanar shan ice cream 蓳ace dan ba tama so, banda tayar mata da zuciya ba abinda yake in ta sha sai taji kamar zatayi amai
Kallon ta ya 茩arayi yace "so kike in 茩ara mai maita miki"
"Yahh Allah na 茩oshi" ta fa蓷a idonta fal hawaye
Kallon ta yayi yace "abinci ne da zaki ce kin 茩oshi"
"Bana shan ice cream fah"
Irin kallon are you serious ya mata yace
"To yau zaki fara, come on sha"
Kamar zata yi kuka ta 蓷auka spoon 蓷in takai baki wani kwalla na cika idonta, ita tana ganin ikon Allah, mutum baya son abu amma za'a mai dole, ita tace sai ya siya mata ne da zai saka ta a gaba dole sai ta sha
Tana kaiwa ta ha蓷uye da kyar ,wani spoon 蓷in ta 茩ara kaiwa shima kamar ance ta sha flagyl, a spoon na uku ne taji wani amai ya taho mata ai da sauri ta ijje spoon 蓷in tayi waje
Saurin tashi yayi shima ya biyo bayanta, tun kafin ta karasa inda sukai parking ta tsugunna a wajen tana kakari, wani me saida pure water ya samu ya bata ta wanke bakinta
Sai duk yaji be kyauta ba, ta nuna mai bata so amma ya tilasta mata gashi ai ya sakata amai bata shirya ba ba gaira ba dalili, sai sannu yake mata, amma tayi banza ta kyale shi, hankalin sa duk ya tashi amma bazaka ce haka a kan face din shi ba, sannun da yake mata ma kamar wanda aka wa dole amma a ransa kuwa ji yake kamar ya daki kansa
wani haushi haushin shi take ji ya sakata yin amai a public,
Suna nufa ya bu蓷e mata ta shiga tana wani ha蓷e rai, shima ya bu蓷e side din shi ya shiga
"Sannu"
Ji tayi kamar ta gwabe bakin dake mata sannun, se kace bashi ya ja tayi ba hmm
Kanta ta kwantar kan kujerar ta juya mai baya tana kallon glass din motan ta rufe ido
Ahaka har bacci ya 蓷auke ta, duk bayan mintina sai ya juyo ya kalle ta, yanayin na mai da蓷i a hakan dan yama rage gudun motar, ahankali yake tafiya dan kar su 茩arasa da wuri
Har suka isa bata tashi ba, ido ya zuba mata yana jingina kanshi shima akan kujerar sa, yanzu ta juyo tana facing din side din da yake
Face 蓷in nata yake bi da kallo, aranshi yace
"You look more innocent and sweet in kina bacci,that baby face of yours, ina son wa蓷anda tiny lips din da kullum suke ga蓳a, dan rigima ayita cuno su" murmushi ya 蓷anyi sannan a fili yace
"Matsoraciya, kullum bakida aiki se tsoro kamar wadda za'a sace, farar kura kawai"
Idon ta da ya 蓷anyi ja ta bude, bacci take amman tana iya jin yanda idonsa suka hanata sukuni, yana ganin haka yayi saurin kauda kanshi ya zauna daidai kamar ba kallon ta yake ba
Tashi tayi zaune sosai tana salati, ta kalle shi ta kalli kofar gidan, wayar ta da ta fa蓷ar kasa ta dauko dan dama iya abinda ta dauka kenan ba ko jaka a hannun ta
Handle din ta bu蓷e zata fita ya rufe, bata ce komai ba ta saki handle din, fita yayi ya zagaya ya bu蓷e mata, kallon shi tayi, sai kuma ta fito ya rufe suka nufi gidan
A bakin 茩ofa suka ha蓷u da su Nabila da Anty ta aike su suna dawowa, gaishe shi sukayi suna mata kallon Allah yasa mu ha蓷e zakiyi mana bayani
Binsu tayi suka yi gaba,shima yana biye dasu a baya
Ba kowa a parlourn, Anty na sama, zama yayi su kuma suka yi hanyar stairs Nabila na Jan hannun ta
"Keee ki sake ni ko se kin 蓳alla ni tukuna"
Kin sakin ta tayi saida suka je 蓷aki sannan tace
"Kaiii kun tafi dani kalla wani match kun wani jero kamar wasu newly Weds"
"To ai sun kusa zama newly Weds din"
"Kin san dan kawai muna gaban sune ba damar yin hoto ai dana 蓷an yi capturing moment 蓷in nan"
"Keee ashe muna 蓷aya nima fa abinda yazo zuciya ta kenan"
Ita dai bata tanka su ba dan tasan so suke su kunna ta, itama dai Fareedah bata ce musu komai ba
"Kee ba mu kira Anty ba, Anisa kije ki kira anty ai tare kuke" fa蓷in Jalila
"To dan tare muk.., ni nasan inda take ne"
Ta gyara zancen ganin kamar har yanzu Fareedah na ciki da ita
"Tana 蓷akin ta"
Bata ce komai ba ta fita, tunda dai har tasa aranta zata yarda be kamata ko su ta ringa nuna musu kamar baso take ba dan yanzu ta gane me suke fada mata, ba da蓷i taringa hakan a gaban fareedah
Knocking tayi a kofar tace ta shigo, tsaye ta same ta gaban wardrobe tana gyara kaya
"Anisa kin dawo,yasu Ammi"
"Anty ina wuni, duk suna lafiya sun ce in gaida ke"
"Madallah ya jikin naki"
"Lapiya kalau amm daman tare muke da ya Umar yana parlour"
"Kice Babban yaya ne a gidan, ki fa蓷a mai gani nan zuwa kar ya jini shiru"
Da Tom ta amsa ta fita tayi 茩asa
Tun ta fara saukowa daga stairs 蓷in yake bin ta da kallo, har kusan har蓷ewa tayi dan daman da sauri take sakkowa
"Yah tace wai gata nan zuwa tana 蓷an abu ne"
Kai ya jinjina mata, ta juya zata tafi yace
"Ke zauna kafin ta sakko"
Kallon shi tayi ta 蓷an kwa蓳e fuska tace
"Yah ni kuma??"
bayi mata reply ba,sai kallon ta da yake
"Yahh abu nike yi"
Gira 蓷aya ya 蓷aga mata yana 蓷an ha蓷e rai
Zama tayi a dan nisa dashi tana cuccuno baki, to ita idan ta zauna me zata mai
Follow and like my account on arewapen ba dan halin wannan marubuciyar ba dan Allah 馃ス馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹
______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 馃尯
***