Free chapter · Read without an account

Page 38

by Ayshatou Galadima · MISHAL

MISHAL



By AYSHA GALADIMAđŸ€đŸż
***


BOOK 1 
Page 38

Hannayenta biyu tasa tana d’an tura kafad’an sa a hankali “ Uncle Moh please ka sauke ni
” cikin rawar murya tayi maganar , hawayen da suka cika idanuwanta suna saukowa akan kumatun ta. 

Baice mata komai ba sai finger d’insa, da yasa ya d’an goge hawayen , idanuwansa ga baki d’aya akan fuskarta.

“ Meyasa kike kuka ?” Yayi maganar cikin ‘kasan ma’koshi. 

Ji tayi wani kukan yanaso ya taho mata, amma sai iya ‘ko’karin mayar dashi take, ta hanyar sauke ajiyar zuciya, shiyasa ‘kirjinta yake sama , yana ‘kasa da sauri.

Ganin bashi da niyar sakinta ta d’an zabura da sauri zata mi’ke ya sake mayar da ita, fuskarsa babu fara’a ya furta “ Keeee?.” Take Moh ya dawo original Uncle Moh d’insa , babu fara’a kwata kwata.

Hakan yasa ta nutsu, ta dena ‘ko’karin ‘kwace kanta da take yi. 

“ Good , so now tell me , kukan me kike?”.

Shiru tayi tana tunani, sai maganar Zarah ya sake dawo mata cikin kai, d’an ta’be baki tayi kad’an tana girgiza masa kai, babu abunda akai mun..”

“Karki bari na sake maimaita maganar da nayi miki
.”


“ Dagaske Uncle Moh, babu abunda akai mun?”.

Hannunsa d’aya ya saka ya d’an ja hancinta, hakan yasa ta d’anyi murmushi kad’an tana san juyar da kanta amma ya’ki bata damar hakan. 

Sai ya saka hannunsa ya d’ora kanta akan kirjinsa, hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya me d’an ‘karfi a fili. 

Sai da ya bari tayi relax sosai tukunna ya d’an sunkuyo da kansa dai dai kunnenta , yadda ita kad’ai ce zata ji abunda yace “ Mimi if you’re angry , just say it

 so now tell me , me kike ‘boyewa a zuciyar ki?”. Yadda yayı magana so calm, yasa ta d’an d’ago ta kallesa , sai ya d’aga masa girarsa guda d’aya , sai ta koma yadda take tana fad’in “ Uncle Moh?”.

“ Uhmm 
” ya fad’a ba tare da ya kalleta ba.

“ Meyasa bakazo ka duba ni ba?”. 


“ Am not in town Mimi
”

Kanta ta sake jinjinawa, sai kuma ta sake fad’in “ Aunt Aya tace zaka kira ni, kuma baka kira ni ba.”

“ Ba gashi nazo ba , ai shine kiran , ko kinaso na kira miki itane?”.


“ Itama ai tunda ta tafi ban ‘kara ganinta ba, tace min zata dawo amma har yanzu bata dawo ba .”

Hannu yasa yaja hancinta, har sai da tace aushhh, hakan yasa ya d’anyi murmushi kad’an , ita kuma ta d’an turo lips d’inta . 

“ She’s back , gobe zaki ganta .”

Da mamaki ta furta “ Gobe ? Dagaske?.”


“ Ko bakyaso ki ganta?”.

“ Inaso , babu kowa fa yanzu Mamy sun tafiya, Aunt Shukura tana zuwa school sai ni kad’ai fa 
.. like an orphan
..”

“ Then you’re not
 you have a whole family and also here i’am 
”

Za tayi magana, ya mi’ke tsaye da ita , a hannunsa babu yadda ta iya sai dai ta sa’kala hannuwanta a wuyansa sabida kar ta fad’i. 

A haka suka cigaba da tafiya , har ya sauko ‘kasa da ita. 

Falon ‘kasan babu wani haske sosai, it’s so dummy haka, ya wuce da ita har wajan dinning. 

Kan dinning d’in kuma an shiryasa da different dishes , sai faman tashin ‘kanshi yake 
. 

Sakar baki tayi tana kallan dinning d’in, tana mamakin yadda akai dishes d’in sukazo, tunda tasan babu kowa a cikin part d’in. 

A kan kujera ya zaunar da ita , shima kuma ya zauna yana d’an nuna mata abincin da idanuwa. 

Sai a lokacin taji ta soma jin yunwa , dan tun kukan da tayi akan maganar su Zarah bata kuma ßaka komai a bakinta ba sai yanzu da taga abincin tsohuwar yunwar da take ji ya tashi. 

Da idanuwa ta soma bin dishes d’in, bata masan wanne za tayi serving ba , sabida duka high note dishes ne. 

Farfesun cowtail ta d’an zuba masa a bowl, tana tunanin mene ne next abunda za tayi serving d’insa , sabida akwai su fried rice , creamy pasta , steamed vegetables, fresh fruit platter da drinks har kala uku ma.

Creamy pasta ta zuba masa da steamed vegetables, sai fruit juice da ta saka masa a cup, wani d’an bowl d’in kuma tana ibar masa fruit platter din wajan. 

Ita kuma ta zuba fried rice da kuma grilled chicken, sai drink kawai..

Har ta gama serving d’insa bai ce komai ba , kuma bai ci abincin ba sai da ya gama serving nata ta zauna , sannan ya soma cin abincin nasa gentle as always .

Ita kuma duk da tana cikin damuwa kad’an haka ta dinga cin abincin sabida kar ya fahimci wani abu, duk da time to time idan ta ‘kurawa abincin ido tana ‘kara tunano maganganun Zarah da Mommy da har ‘kasan zuciyarta tana addua Allah yasa mafarki take bawai gaske bane .

Shi ya soma ajje spoon amma bai tashi ba , kuma bai mata magana ba , na kamar mintuna 5 ganin har time d’in bata gama cin abincin ba , kuma yadda take ci kamar me cin magani


“ Mimi ? Ya kira sunanta .

Da sauri ta furta “ Uhm Uhm
.”

“ Your food
” ya kuma fad’a ba tare da yayi acknowledging yadda ta d’an diri rice ba .

Cikin sauri ta kalli plate d’insa ganin ya gama cin abinci , itama ta mayar da hankali kan ta, ga baki d’aya tunanin da take , ta ajjesa a gefe , haka ta dinga tura abincin , har sai da taji zata yi amai tukunna ta ha’kura ta d’an sha lemo amma taci abincin sosai yadda ya kamata. 

Tana gamawa ta mi’ke zata tattara wajan, sai ta d’an tsinkayi muryarsa cikin low voice “ Leave it there .”

Jiyowa tayi ta kallesa kamar bata gane me yake nufi ba , alamar tana neman ‘karin bayani. 

Shi kuma wayarsa da take kan dinning ya d’auka ya mi’ke , sannan ya ri’ko hannunta suka dawo falo. 

Akan kujera ya zauna , hakan yasa itama ta zauna tunda hannunta yana cikin nasa . 

Sai da suka zauna su duka tukunna ya d’an same hannunta daga nashi , bai ce mata komai ba , kuma bai sake ri’ke hannunta ba illa ma d’an matsawa ma da yayi kad’an , yadda zata fi sake wa . 

After a long minutes of silent Mimi ta kallesa ganin idanuwansa a rufe , so take ta tanbayesa amma kuma tana tsoran yi masa tanbaya kar ya fahimce ta ba dai dai ba shiyasa ta d’an tsaya ‘karewa face d’insa kallo .

Tayi nisa a kallan fuskarsa ya bud’e ido, karaf idanuwansu ya shiga na juna , kuma ta kasa janye idanuwanta daga nashin kamar yadda shima d’in bai d’auke idanuwansa ba . 

Daga baya kuma taji idanuwanta na rawa sabida wani irin abu da take hangowa a cikin nasa idan wanda yasa mata jin tsoro da batasan ko na mene ne ba . 

‘Karamun smirk yayi , hakan yasa tayi saurin d’auke nata idon, tana juya tanbayoyin da suke zuciyarta , ba tare da tasan yadda zata yi masa su ba . 

“Asked what you want to asked
.” 
Yayi mata magana ba tare da ya kalleta ba . 

“ Uncle Moh me
 me .. me ..” sai tayi shiru ta kasa ‘karasawa. 

Sai da yace “ Uhm?”. Tukunna ta samu courage d’in cewa “ Meyasa kake kissing d’ina ko kasani a cinyar ka , bayan babu kyau? Kuma Allah ya hana.”

“ Are you asking me Mimi, or are you asking me to kiss you again?”. 


“ No Uncle Moh , am just asking
” ta ‘karasa a hankali.

“ Then asked me in a proper way
”

Shiru Mimi tayi, bata fahimce sa ba and ba ta fahimci yadda zata tanbayesa in a proper way ba . 
Tun daga nan tasan she can never asked him about Zarah ko kuma abunda su Zarah suka ce akanta , and beside that batasan yanke hukunci cikin sauri tunda har yanzu batasan actual dalilin su nayin haka ba . 


Kallan time Moh yayi , dare yayi sosai and takasan cewa komai. 
Finger d’insa d’aya yasa ya ta’ba goshin ta ita kuma ta d’ago kai ta kallesa da sauri. 

Da hannu ya nuna mata upstairs “ Dare yayi , go and sleep Mimi
”

Cikin sauri ta jinjina masa kai sabida daman tana san komawa d’aki, daga lokacin da tace masa “ Good night ..” zaka fahimci cikin excitement tayi maganar , har saida ya d’ago ya kalleta . 

Bata kalli hanyar sama ba , ‘kofar fita take kalla , dan duk tunaninta d’akinta yake nufi , ganin zata wuce ya kuma fad’in “ Mimi?.”

Kallansa tayi tana fad’in “ Naam Uncle Moh
”

“Haka nace ki kwanta a d’aki na .”

Zaro ido Mimi tayi zata yi magana , yayi mata wani irin kallo , babu shiri ta had’iye maganarta . Simi simi ta wuce saman, tana shiga d’akinsa ta soma safa da marwa tana tunanin yaya za’ayi tayi bacci a cikin d’akin bayan d’akinsa ne .

Idan kuma ta kwanta a d’akin shi kuma an ina zai kwanta?. Ga baki d’aya taji ta kasa samun nutsuwa a tattare da ita , tana cikin safa da marwa d’in nan , Joy da tun d’azu take kallanta , ta fito sosai yadda zata ganta .

“ Wannan kai da kawowar da kike na mene ne? Ko kina tunanin zai miki wani abu ne ?”.

Da sauri Mimi ta juyo ta kalli Joy. Tsawan sati bata Ɵaka ta a cikin idanuwanta ba sai yanzu . “ Haba Joy sai yanzu zan ganki? Kusan sati d’aya kin ‘ki zuwa ko nayi miki wani abu ne kike fushi?”.


“ No Mimi ba haka bane , dole ne yasa baki ganni ba , ba dan na so ba amma gashi yanzu kin ganni
 kai kawon me kike haka?.”

“ Joy taya zan kwana a d’akin Uncle Moh? Ni ga baki d’aya ma wani iri nake ji sai naji kamar an canza sa ne , not exactly kamar yadda na san Uncle Moh, ada ko kallo na ba yayi , and ba zai ta’ba ri’ke hannu na ba , amma yanzu fa ? He can even kiss me , kuma na fad’a masa babu kyau babu kyau , amma kamar baya fahimta na kwata kwata . 

Ya zanyi Joy?”.


“ Hhhhhh
” Joy ta d’anyi dariya har sai da Mimi ta d’an ’bata fuska. 

Hannunta Joy ta kama ta zaunar da ita akan d’aya daga cikin kujerun da suke wajan, amma ita bata zauna ba , tana dai kallan Mimi har lokacin. 

“ Mimi wani lokaci bada zahiri ake an fani ba wajan fahimtar abu. 

Wani lokaci da zuciya da ‘kwa’kwalwa ake anfani
.. ki zauna kiyi tunani , wane ne shi, meyasa yake haka, kuma taya zaki gane ma’anar hakan . 

Karki bari tsoron da take zuciyar ki yayi galaba a rayuwar ki Mimi.

Wani lokaci tsoro makami ne , idan kika juyasa ta zama makami. 

Wani lokaci tsoran ki zai iya fad’ar da ke idan har baki yi ya’ki dashi ba.

Akwai lokacin da tsoro yake da mahimmanci , akwai kuma lokacin da fuskantar wannan tsoran shine abu na farko da zai canza maka rayuwar ka ga baki d’aya , Ciki kuma har da tunanin da kike akan Zarah
”

Sosai Mimi ta kalli Joy, duk da batayi mamakin yadda tasan abun Zarah ba , sai dai maganar yazo mata unexpected, hakan yasa ta furta “ Joy me kike nufi?”.

“ Mimi bani da hurumin fad’a miki wannan maganar kiyi ha’kuri, ki zauna dai kiyi tunani sosai , kuma ki fahimci abunda ya kamata ki fahimta , ki ajje soyayyar kowa a gefe ki fahimci ainahin abunda yake zuciyar kowa kafin ki sakar musu zuciyar ki Mimi


Ki zama mai kafin tunani, me basira , me kula sosai da abu, koda wannan abun ya kasance ‘kan’kani ne Mimi


Bani da lokaci sosai Mimi , ki samu ki huta , tunda yace miki ki kwanta kiyi bacci, ya kamata ki kwanta , karki makara, kuma kiyi ‘ko’karin goge tunanin da suke zuciyar ki , ki bar komai a muhallin da ya dace kinji?.”

Cikin sauri Mimi ta bud’e baki za tayi mata magana , amma Joy ta ‘bace ba tare da tabata wannan chance d’in ba. 

Fuskar Mimi kamar za tayi kuka sabida tafiyar Joy. 

‘Dan shiru tayi tana tunanin maganganun Joy, so take ta fahimci me Joy take nufi , amma ta kasa sai ma ciwan kai da taji kanta ya soma , dan dole ta ajje komai, ta kwanta a kan kujerar , kafin kace wani abu bacci ya d’auketa . 


1 and half hours later ya shigo d’akin ganin tana bacci akan kujera , sai ya kalli bed d’in, sannan ya kalleta . 

Baice komai ba yazo ya d’auketa daga kan kujerar ya kwantar da ita akan bed , ya lullu’ba mata duvet , ya kashe mata hasken d’akin sannan ya sake fita daga d’akin. 


WASHE GARI
Washe garı , ‘karan kiran sallah ne ya soma tashin ta . Da fari bata motsa ba sai da kiran ya soma tashi a karo na biyu tukunna, ta d’an motsa tana dalilin wayarta , ganin bata ta’bo wayar ba , ta soma mi’ka da hamma, tana mi’kewa zaune. 

Hannu ta saka tana muntsike idanuwanta, kafin ta bud’e su ga baki d’aya .

Kallan d’akin da take ciki tayi da idanuwanta masu bacci cike da mamaki. 

‘Kara sa hannu tayi tana shafa idanuwanta , tana ‘kara bin d’akin da kallo ganin inda take .

‘Dakin tane . Yes d’akinta ne dai nata da yake part d’in Mamy kuma akan gadon ta bayan tasan ba anan ta kwanta ba jiya. 
Mamakin hanakan yasa baccin da yake fuskarta d’aukewa ga baki d’aya tana ‘kara kallan d’akin da kallo, har sa da taji kamar lokacin sallah yana ‘ko’karin wuce ta , tukunna ta wuce toilet tayi alwala, tazo tayi sallah , Azkar da kuma karatun al-qur’ani. 

Ta gama da kamar mintuna 15, aka d’anyi knocking ‘kofar d’akin. 

Kallan ‘kofar tayi , kafin ta yun’kura aka sake ‘kwan’kwasa ‘kofar. 
Cire hijab d’inta tayi, ta nufi ‘kofar , tana bud’ewa wacce ta gani ya sata tsayawa so speechless , ta ma rasa wana reaction za tayi
. 

Murmushi Aya da take bakin ‘kofa tayi, tana kallanta “ Na koma ? Ko bakyasan gani na .”

Mimi batasan lokacin da tayi murmushi ba tana fad’in “ Aunt Aya ?”

Hannuwanta biyu Aunt Aya ta bud’e mata ta murmushi , babu musu Mimi ta matso kusa da ita tana hugging d’inta “ Daman dagaske zaki dawo?”.

‘Dago da ita Aya tayi tana kallan fuskarta “How can i leave you Little Mimi?”.

“ I thought ba zaki dawo ba fa , all this days.”

“ And here I’m. Can i ?” Aya ta nuna d’akin Mimi da hannu, cikin murmushin da har yanzu bai fita daga fuskarta ba ta furta “ Why not 
” ta matsa mata hanya ta shiga. 

Babu musu Aya ta shiga tana fad’in “ It’s been long, but i missed you terrible! Little Mimi.”

“ So ki zauna anan kar ki bari Uncle Alameen ya ‘kara tafiya da ke 
”

Jiyowa Aya tayi tana kallanta “ That man? Na gaji dashi, he’s so annoying atimes, i wonder yadda budurwarsa za tayi controlling d’insa
”

“Hmmm 
” Kawai Mimi tace sabida batasan me zata ce mata next ba , sabida ba wai zama suke suyi hira sosai ba , tunda . 

Ganin tayi shirun ne yasa Aya ta furta “ Oh yeah ! Ameerah tana ‘kasa tana shirya mana breakfast, nima yanzu nazo na dubaki ne, banasan barinta ita kad’ai a ‘kasa .”

“ Ameerah ?” Mimi ta tanbaya da mamaki.

“ Yeah Ameerah ! Jiya Moh Moh ya d’auke ki, so tayi bacci a d’akina , tace ta kira ki baki picking call d’in.”

“ So Aunt Aya , you’re here since yesterday?.”

“ Yeah ! Tun kafin Alameen yayi disconnecting wutar gidan 
.” Aya tayi maganar tana kashe mata ido d’aya.

Da mamaki Mimi ta furta “ But why?”.

‘Dan murmushi Aya tayi tana nufar ‘kofa “ You can ask him your self 
 for now kiyi sauri kiyi wanka ki sauko ‘kasa , Ameerah is looking for you 
” daga nan ta fice daga d’akin ba tare da ta waiwayo ba . 

Bin ‘kofar tayi da kallo, a tunaninta jiya wutar ce ta samu matsala , not knowing Alameen ne yayi disconnecting d’inta , and she have no right to asked him why , hakan yasa ta ajje tunanin nan , ta wuce toilet dan tayi wanka . 

Bata dad’e sosai ba , ta fito  ta shirya cikin ‘kananan kaya , but kayan basu kamata ba , sai ta saka hula akanta , ta d’auki wayarta zuwa ‘kasa .

Tana jiyo muryar Ameerah a kitchen suna hira , ta nufi haryar kitchen d’in kenan tajiyo muryar Shukura da ita fitowarta kenan, ta shigar cikin maroon d’in abaya alamar fita za tayi.

“ Mimi?.”

Kallanta Mimi tayi tana fad’in “ Naam Aunt Shukura ? Ina kwana?”

“ Lafiya ‘Kalau Mimi , Sorry jiya kinyi bacci da wuri na dawo late and Aya tace mun kina d’aki kina bacci, and kuma banaso na tashe ki a baccin shiyasa . 

How are you? Hope you’re not lonely?”.

“ Hmm A little bit Aunty Shukura , kinyi waya da Baffa ko Mamy? Bana samun number d’in su.”


“ Nima bana samun su, but Baffa ya turo mun message yace there fine , idan sun kammala abunda suke zamu ji su , and they even asked me to greet you for them.”


“ But Aunt Shukura dagaske sai sunyi week d’in nan kafin su dawo? Har na soma jin part d’in nan baya dad’i wallahi tun tafiyar su.”


“ Toh ya muyi Mimi? 1 week kamar yau ne , if your lonely you can go out with Aya since she’s back , ga kuma Zarah da Ameerah nasan zasu d’ebe miki kewa , you won’t be lonely for long.”

‘Karamun ya’ke kawai Mimi taji mata jin ta ambaci sunan Zarah , batasan jan maganar sosai shiyasa ta canza maganar zuwa “ Are you going out?”.

“ Yeah Mimi , zanje school ne ..”

“ Okay take care , nima school naga nan da 2 weeks za’a koma , har na soma missing d’in gida ma wallahi , gasu Baffa basa nan atleast su zauna kullum na dinga ganin su.”


“ Iye sannu dad’i gida, mu da muke zuwa school kullum ba’a san mu kenan? Abeg karki sa na makara , su Aya ne a kitchen ko? Naji kamar muryarta.”

“ Yeah sune , nima kitchen d’in zani fitowar ki ne ma ya d’an tsayar dani.”

“ Okay muje kitchen d’in kafin na wuce.” 

Daga nan suka wuce kitchen d’in tare 
. 

Ameerah da Aya suna tsakiya da girki sai ga su Mimi


“ Chef Aya and Chef Ameerah
” Mimi ta kanne musu ido guda d’aya.

Fari Ameerah tayi mata tana juya idanuwanta waje d’aya “ Yes my lady, me kike bu’kata?.”

“ Anything Dear .” Mimi ta bata amsa , hakan yasa duka sukai dariya . 

Ganin Shukura da dressing alamar zata fita Aya ta furta “ You’re going out?.”

Shukura ta jinjina mata kai ..

“ Mun kusa gama breakfast , ki zauna kici kafin ki tafi mana?”.

“ No Aya , thank you ! Yanzu ma na kusa makara ne , nace bari nazo mu gaisa kafin na tafi
 Ameerah how far..” ta ‘karasa tana mayar da kallanta kan Ameerah.

“ Aunty Shukura ina kwana.”

“Lafiya ‘kalau Chef d’in mu, am going out , see you all . Idan akwai abunda kuke so you can tell me sabida may be yau na dawo gida da wuri but am not sure .”

“ See you Shukura , ina gida they won’t need anything, just take care of your studies okay? All the best.” Aya ce tayi maganar , hakan yasa Shukura ta jinjina mata kai, tana musu waving hannu kafin ta tafi. 

Kitchen d’in yayi saura su uku.

“ So now ladies , me zan taya ku dashi?”

“ No Mimi , you don’t need to worry your self , nida Ameerah ma mun isa , and we’re almost done , yanzu zamu gama babu wani aiki, kawai ki jira mu a falo,  if you’re bored ki danna wayar ki or relaxed kadin mu fito.”


“ But Aunt Aya
”

Aya ta katse ta “ No but Mimi .. just go.”

“ Okay ..” Mimi ta fad’a tana komawa kan kujera. 

Har ta shiga instagram, sai kiran Zarah ya shigo wayarta , kallan sunan kawai tayi ta cigaba da scrolling d’in IG d’inta. 

A karo na biyu Zarah ta kuma kiranta, but nan d’in ma batai picking ba ta cigaba da harkar ga banta sai ga message d’in Zarah ya shigo wayarta “ Mimi kizo inji Mommy.”

‘Dan shiru tayi tana nazarin maganar, taje ko kar taje. 

80% na zuciyarta yana cewa kar taje while 20% yana cewa taje , tunda batasan me zata ce mata ba. 

Wani kiran Zarahn ne ya sake shigowa , a wannan karan Mimi sai tayi disconnecting call d’in tayi relax tana cigaba da chart d’inta. 

Ta manta ma da kiran Zarah , sai kawai ga Zarah ta shigo falon sim sim kamar wata mara gaskiya . 

Sau d’aya Mimi ta kalleta ta d’auke idanta. 

Ita kuma Zarah ta sauke wani ajiyar zuciya sai da ta kalli falon ta tarar da babu kowa a cikin sa sai su biyu tukunna ta ‘karaso inda Mimi take a zaune.

‘Karamun gyaran murya tayi, kafin ta furta “ Besty
.”

Wani irin kallon mamaki Mimi ta bita dashi, sai dai bata fito ta nuna mata ba , kawai dai sai yanzu ne ma ta soma mamakin audacity d’in Zarahn da har take iya biyo ta bayan abunda ta gama fad’a akanta. 

“ Besty 
” Zarah ta kuma kiranta tana d’an matsowa kusa da ita kad’an.

‘Karamun murmushi Mimi tayi , ta ajje wayarta akan cinyarta sannan ta d’ora both hannayenta akan ‘kirji tana kallan Zarahn da itama a yanzu ta ‘kura mata idanuwa sosai .
“ Zarah kenan, it’s better ki ajje pretending d’in nan , this Besty stuff of yours I think ai lokaci yayi da ya kamata ki ajje su a gefe . 

You can call me Mishal Or Mimi, any one.”

“ Am not pretending Mimi , kinsan cewa bani da kamar ki , you’re my best friend, kawai abunda kika ji ba haka bane , baki fahimce ni ba kuma jiya ina ta kiran ki sabida nayi miki bayani amma kin ki tsayawa, and nazo har part d’in nan sabida na ganki an’ki hanani ganin ki..

I think we can settle this, kuma zan iya miki bayani yadda zaki fahimta sosai, abunda kika ji ba haka bane , it’s just a slip of tongue.”

‘Dan lumshe ido Mimi tayi tana sake bud’esu akan Zarahn. 

“ Zarah if you’re done please you can go, all your explanations bana bu’katar su and am not interested on them so , thank you , you can go now.”
 
“ Haba Mimi wannan ai wulakanci ne , ina ‘ko’karin yi miki bayani amma kamar korata kike . 

Kinsan da gangan bazan cutar da ke ba and i will never do something similarly of that , kowa yana da secret d’insa and i don’t see why ma da jiya zaki hawo har wajan d’aki na bana nan, I never done that, da kika ga babu kowa wajan why not ki jira ni na sauko or something like that da duk hakan bata faru ba , but you’re here playing the victim. 

Bayan ni ya kamata nayi haka , why please! Why ?”.

“ So now Zarah idan na fahimce ki, you’re the victim here ? After all what you just said yesterday?.”

Ba tare da second though ba , Zarah ta furta “ Yes ..”

Mamaki ne ya çıka Mimi , she never thought haka halin Zarah yake sai yau , yadda take magana , bama ta d’auka cewa tayi laifi sai ma ganin laifin ta da take gani sabida ta hawo saman d’akin su.

Idan za’a ce mata Zarah can do that she will never believe that, ba zata ta’ba yadda ba ko wane ne ya fad’a mata, but gashi nan da kunnanta taji maganar Zarahn , and bata ta’ba kawo Zarah tana da hidden agenda ba irin wannan.

“ Zarah you can go , if you’re done please.”

“ Am not done Mimi, yanzu ma Mommy take kiran ki, na kira ki baki d’auka ba and na tura miki message shima baki bani reply ba atleast you can respect her as a mother , kije kiji abunda za tace.”

“ Hmm okay muje.” Mimi ta mi’ke hakan yasa wani murmushi ya fito akan la’b’ban Zarah da ya ‘ki ‘boyuwa . 

Zama su fita daga falon su Aya suka soma fitowa da abu a hannun su . 

Ameerah ce ta kalli Zarah “ Zarah yaushe kika shigo?” 

‘Dan ya’ke Zarahn tayi mata tana fad’in “ Yanzun nan na shigo .”

“ Okay to ki zauna muyi breakfast mana , mun gama .”

“ No Ameerah Mommy ce take kiran mu, ki wari wani lokacin idan nazo.”

“ Take kiran ku? Iya ku biyu kuma?”. Ameerah ta sake tanbaya .

“ Yes..” itama Zarah ta bata amsa tana kallan Aya da ko inda take bata kalla ba , hankalinta yana kan Mimi da take kallo.

“ Little Mimi, har mun gama breakfast , let’s go yanzu zamu shirya dinning d’in
”

“ Uhm Uhm daman Mommy ce take kiranta 
” Zarah tayi maganar a d’arare tana kallan Aya kamar me tsoran magana .

Ba tare da damuwa ba Ayan ta kalleta sannan ta furta “ And so? Babu inda zata , zaki iya zama in kinaso , and zaki iya fita idan kin gaji , the choice is yours
” ga baki d’aya d’akin akai shiru , ita kanta Mimi tayi shock da irin reply d’in Aya duk da tun ba yau ba ta gane Aya ‘yar I don’t care ce , she don’t care and bata tsoran ta fad’i magana agaban kowa idan taso magana . 

Kuma duk cikin su babu wanda yaga fuska da zai ja da abunda tace , hakan yasa Zarah ta kalli Mimi ko zata ce wa Aya d’in wani abu. 
Sai taga Mimi ta share , ta bi bayan Ameerah da Aya da suka wuce dinning . 

Sosai Zarah tasha jinin jikinta , Ameerah da Mimi kuma suka zauna akan dinning , lokacin da Aya zata kuma wucewa , wani mugun kallo da ta jefawa Zarah , sai da Zarah ta kuma d’an ja baya kad’an , dan ta tsorata da kallanta .

Aya tana barin wajan , kallo d’aya tayi musu both Ameerah da Mimin , tayi saurin ficewa daga part d’in. 

Tana fita Ameerahn ta kalleta “ Mimi wai what’s wrong with Zarah ? Daga jiya zuwa yau na kasa gane mata , infact a cikin kwanakin nan tanayin wasu abubuwa so strange , especially jiya da nace mata tazo muje part d’in ku, tace ba zata je ba zata zauna a wajan Momy, on like before da babu abunda take ‘kaunar ji kamar tazo part d’in ku.”


“ Ameerah may be she have her own reason ne
.”


Kallanta sosai Ameerah tayi , yanzu kam sun dena bata mamakin ma su biyu, zata yi magana Aya ta sake fitowa shiyasa Ameerah ta fasa fad’an abunda take san fad’a d’in. 

Zama sukai , sukayi breakfast d’in su sosai. 

Da suka gama suka mayar da abubuwan kitchen suka dawo falo, sabuwar kira ya ‘barke a tsakanin su , anan ne Mimi take sake fahimtar Aya , is a simple and loving person. 




_____________
ISTANBUL

.

‘Karfe 5:40am na safe Ahmet ya fito daga d’akin sa , yana kallan hanyar d’akin Aylin, amma bai ce komai ba ya fito falo ya zauna , idanuwansa ga baki d’aya akan ‘kofar shigowa falo kamar me expecting wani abu.

Gidan yayi tsif babu hayaniya ko kad’an. 
Wayarsa ya ‘d’auka ya duba time , sannan ya soma duba messages d’in ciki na few minutes ya mi’ke zuwa sama . 

Direct d’akin Aylin ya shiga . 

Sau biyu yayi knocking , ‘kofar d’akin amma bai ce komai ba . 

Jin babu motsi kwata kwata ya bar wajan zuwa d’akinsa . 

Wanka yayi ya shirya cikin suit . 

Lokacin da ya sauko ‘kasa , Anne ta shirya ta fito itama tare da Nunu da take sanye da uniform d’in school itama . 

Tana ganin Ahmet ta soma d’aga masa hannu. 
Murmushi yayi mata yana amsar ta daga hannun Anne . 

“ My Nunu
.”

“ My Memet
” itama ta amsa masa . 
Kallan Anne yayi “ Good morning Anne .”

“ Good morning Abi, fatan ka tashi lafiya.”

“ I’m good Anne , ya kuka tashi?”

“ Same as always Abi
”

“ Let me prepare something for you Anne 
”

“ No we’re good , already nayi order a hanya kawai zamu amsa mu wuce school , ko Nunu? 

Kanta Nunu ta jinjina masa tana ma’kale hannuwanta duka biyu a wuyansa , tana fad’in “ Memet
”

“ Yes Love
 Good Morning
” ya fad’a yana d’an shafa bayanta .

A hankali ta kuma fad’in “ Memet
”
Shima kuma ya kuma fad’in “ Yes Love
”

Muryarta a rarrabe ta furta “ BU BU.”

Shiru Ahmet yayi mata , sai kallan Anne da yayi, ita kuma Anne ta d’auke idanuwanta daga kansa tana barin wajan. 

Ganin hakan yasa jikinsa yin sanyi kad’an yana d’an d’ago da ita sai yaga hawaye kan face d’inta . 

Da sauri ya soma goge mata hawayan, ganin wani yana saukowa ya sake hugging d’inta “ it’s Okay , idan kuka dawo school zan kira miki shi kinji?.”

“ Yaushe zai dawo?”. 

“ Kwanan nan Bubu zai dawo so stop crying in baki dena kuka ba ai bazai zo ba. 

Stop crying okay ?”.

Kanta Nunu ta d’aga masa da sauri tana d’an turo bakinta . 

Wajan Anne suka nufa , kallo d’aya tayi musu ga baki d’aya sai ta amsa Nunu d’in tana kallan d’akin Aylin.

“ Ahmet please kafin ka fita ka tabbatar da inda Aylin take kaji?.”


“ Sure Anne
”

“ And please nasan halinka , kar ka biye mata idan tayi maka wani abu , nasan halinta da rashin kunya kai kuma baka d’aukar wannan abun but please, banasan fad’an ku.”

“ Yeah Anne , karki damu  you can just go 
. Ki bar komai a hannuna .”

Anne har ta juya sai kuma ta sake waigowa wajan Ahmet “ Ahmet karka fad’awa Emir kaji?.”

‘Dauke kansa Ahmet yayi yana murmushi , sai dai baice mata komai ba , ya dai d’aga mata kansa kawai . 

Anne bata ce komai ba suka fita daga falon Nunu kuma ya d’aga masa hannu , shima kuma sai da ya dena ganin su tukunna ya sauke hannunta yana ‘kara kallan d’akin Aylin d’in. 

Bayan kamar 20 minutes yana tsaye a falon , lokacin ya tabbatar da cewa su Anne sun fita daga gidan gabaki d’aya . 

Ya shiga d’akinsa ya d’auko wata ‘yar ‘karamar jaka yana sake knocking d’akin Aylin. 

Jin shiru ya d’auki wayarsa yana d’an danne danne , sai ya d’auko wani abu ya saka a jikin ‘kofar , ya cigaba da danne dannen sa kamar na mintuna 5 , sai fit. 
Wani ‘karamun sound ya fito daga ‘kofar da kuma bud’ewa da tayi kad’an alamar lock d’inta ya bud’u. 
Komai da yayi anfani dasu ya kamar cikin jaka , sannan ya bud’e d’akin. 

‘Karewa d’akin kallo yayi , yana kallan how messy it looks like 
. 
Da kuma abun allurar da yake ‘kasa , da magunguna. 

Sai da ya saka hand glove tukunna ya soma d’aukar magungunan d’aya bayan d’aya yana karantawa , sannan yayi snapping. 

Yayi Snapping Aylin da take a kwance tun jiya kamar gawa . 

‘Kafarsa d’aya ya saka ya d’an ta’bata , bata motsa ba kamar wata gawa .

‘Kara ‘karewa d’akin kallo yayi , sai ya nufi toilet d’inta , shima it’s not that clear ,kowama d’akin yayi daman har zuwa lokacin bai cire Handglove d’insa ba , yana zuwa kawai ya jawo kanta kamar wata kayan wanki zuwa toilet d’in , haka ya saka ta a cikin bathtub d’in, sannan ya kunna mata ruwa, yana fitowa daga toilet without looking back
..


_________________

To be continued
 đŸ”„


Aysha Galadima đŸ€đŸż
( Black Queen) 
***



***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol