Free chapter · Read without an account
Page 40
by Ayshatou Galadima · MISHAL
MISHAL
By AYSHA GALADIMAđ€đż
***
BOOK 1
Page 40
A wannan lokacin Zarah batasan ta yar da jakar hannunta ba , sai lokacin da taji fadâuwarta a âkafarta .
Da âkarfi ta furta â OuchhhhâŠâ Tana tsugunnawa, hakan yasa suka kalleta , har da Mimi da zuciyar su take dukan 10-10.
Ita da Ameerah sun zo zasu dubata Aya ta dâan shiga tsakanin wajan, murmushin fuskarta har lokacin bai gushe ba â Karku damu kuyi tafiyan ku, I will help her âŠâ .
Mimi ta budâe baki Aya ta sakar da fuskarta zuwa seriousness sai dai bata hadâe face dâin sosai ba , idanuwanta ga baki dâaya akan fingers dâinta â Mimi ku wuce abunda na fadâa muku, kar ku âbata musu lokaci , and yes zan dubata bakwa buâkar damuwa . So now gooâŠâ yadda tace go dâin cikin dâan kaushi kaushin murya tayi sa, hakan yasa Ameerah ta dâan taâba Mimi tana mata alama da suzo su tafi.
Mimi ba tayi mata musu ba , ta juya suka soma tafiya , amma ko taku ashirin basuyi ba ga baki dâaya suka tsaya kusan a tare , kamar wadâanda suke karantar zuciyoyin junan su.
A dâan tsorace Ameerah tayi âkasa âkasa da muryarta â Mimi anya bawani laifi mukai ba ?âŠâ
â Lefi kuma ? Wana lefi mukai kodai wani aikin zasu samu?.â
â Ameerah nima wallahi ban sani ba , amma wana abu mukai , ji yadda fuskar ki duk ta soma rawa, wallahi Ameerah kika tona mana asiri zaki ga rashin mutumcin da zanyi miki Allah kuwa .â
â Aah Ahhh Mimi wallahi aka ritsani sai na fadâa uban wa yace kisa musha ice cream dâin?.â
â Mts*** Mimi ta dâan ja tsaki tana hararan Ameerahn kadâan â Dan kawai mun sha ice cream sai kice akan shi suke kiran mu, naga ai ba dole ice cream muka sha ba wallahi idan ma shine kawai muce shayin ice cream muka yi muka sha, chocolate kuma mukayi melting dâinsa mun dâan dan gwala kadâanâŠ..
Ai ba ko wace âkarya ce haramun ba , idan mun dawo sai muyi istigfari, Allah ya yafe mana .â
âDan girgiza mata kai Ameerah tayi â Wallahi nidai tsoro nake ji , baki ji yadda zuciyata take boom boom ba kamar zata fito waje?.â
â Toh nima zuciyar tawa ai dukan boom boom, wallahi idan muka zauna anan wallahi zamu iya âbata musu rai , dallah ki nutsu ai de ba zasu doke mu ba , ni zuciyata na bani wani aikin zasu ce muyi musu , kuma Uncle Alameen na nan may be shine dalilin da yasa ma ake kiran namu wallahi.
Allah Ameerah ki nutsu banasan rashin mutumciâŠâ
Numfashi Ameerah ta sauke da âkarfi, tana dafe zuciyarta kafin ta kalli Mimi da itama tayi zaro zaro , itama kuma ta sauke ajiyar zuciya kawai sai suka kwashe da dariya suna cigaba da tafiya duk da sun kasa gane dariyar dadâi suke ko ta wahala , duk da fuskokin su ya nuna dariyar rashin mafita kawai suke .
Suna zuna bakın door dâin Moh yau sai suka ganta abudâe kadâai basai sun budâe da kansu ba .
Ameerah tayi wa Mimi signal akan ta soma shiga , itama kuma Mimi tayi mata signal dâin akan cewa ta soma shiga itama .
Sunyi haka kamar sau uku kowa yaâki ya soma takawa, sai Mimi ta dâan âkara matsowa kusa da Ameerah sabida ta fi jin abunda za tace â Tsakani da Allah Ameerah kizo mu shiga , a shiga a tare tunda tare aka kira mu, yadda na taka âkafa dâaya kema haka zaki taka wallahi kin yadda ?â.
Itama Ameerah dâan matso da kanta tayi kusa da Mimi cikin radâa radâa ta furta â Toh Dan Allah Mimi tsaya mu karanta Tabara ( SURATUL MULK) kinga in ma wani abun ne ai munyi addua ko?â
â Lalle ma baki da hankali Ameerah sai mun gama full sural tare zamu shiga ? Wallahi ba zaki jazamun ba , kinsan yadda Uncle Moh ya tsani a âbata masa lokaci ,,, dallah taho mu shiga.â Mimi tadâan fincikota sukai gaba, amma suna zuwa daf da âkofar suka sake tsayawa, kamar wanda sukai gudu duka suka dâora hannu akan âkirji sannan suka sauke a hankali.
Da finger Mimi ta nuna mata dâan wajan da yake abudâe ita kuma Ameerah ta dâaga mata gida dâaya sabida ta gane abunda take nufi.
Dukan su suka je wajan da yake a budâe suna dan saka idanuwan su ko zasu ga abunda yake cikin falon.
Baâa ganin komai suma dâin kuma babu abunda suke gani kawai tsaâbar guilt da ya kamasu sun ma âki yadda da kansu haka suke ta faman turbuna ido ko zasu ga abunda suke san gani dâin.
Suna a haka kamar mintuna 2 daga bayan su kawai suka tsinkayi muryar Alameen yana fadâin â Me kuke nema toh?.â
Daga Mimi har Ameerah baya sukai a tsorace , hakan yasa suka fadâa cikin falon babu shiri, ko wanne sai faman zazzare ido yake , gashi sunyi baje baje akan tiles alamar rashin gaskiya.
Alameen dâin ne kuma a tsaye , hannunsa dâauke da wasu manyan fararan leda guda biyu , da car key a hannunsa , yasha âkananan kaya da p-cap , duk da dare ne kuma akwai baâkin glass akan fuskarsa.
Shi gashinan ba dariya yake musu ba , kuma ba murmushi yake ba , a tsaka tsakiya yake , kallo dâaya yayi musu ga baki dâaya ya karance su , ganin sun kasa magana balantana ma su tashi daga inda suke a zaune ya furta â Ba kwajin sanyin inda kuke ne?â. Ya dâanyi maganar yana dâan nuna tiles dâin da suke zaune .
Cikin sauri suka miâke tsaye , bawai a kan âkasa suka zauna ba amma kuma suna dâan karkadâe jikin su , har da dâan juyawa su kalli cikin falon suna roâkan Allah yasa Uncle Moh baya cikin falon, dan tabbas in yana ciki toh ya ga fadâuwar su kuma suma sun sani sarai kashin su ya bushe tasss.
Sun kasa tsayawa ma straight hakan yasa Alameen a karan farko yayi murmushi da ya fito da haâkwaransa , tun lokacin da ya tsaya , aushe tun lokacin da suke tsaye a wajan part dâin yake tsaye kuma yaji abunda suke fama amma ko a fuskarsa hakan bai nuna ba kwata kwata .
â You guys kun dena magana ne ? UhmmâŠ.?â Yayi maganar yana kallan su ga baki dâaya at once .
Da sauri suka dâan soma rawar bakin gaishe sa .
â Uncle⊠Unclee Alameen ina wuni?.â
Cikin falon da suke ciki ya nuna musu da fuska yana fadâin â Get go inside âŠ.â Daga nan ya shiga cikin falon ba tare daya kuma kallan su ba .
Kallan juna Ameerah da Mimi sukai, ita Ameerah tana dâan jijjiga fingers dâinta alamar sun shiga uku, ita kuma Mimi fuskarta har ta soma tara âkwalla kamar ance musu sunyi wani abu.
Da âkyar suka iya âkwaâkulo sallama sukai , kansu a duâke suka âkarasa shiga cikin falon, amma sabida baâa amsa musu sallamar su ba , yasa duk suka sake shiga taitayin su , dan ita Ameerah already zuciyarta fall danasanin shan ice cream dâin nan take , sabida tasan babu lefin da tayi sai ice cream da Aya ta hanasu sha , ita kuma Mimi zuciyarta bai kawo mata wannan ba , tafi karkata akan may be wani aikin zasu saka su , tunda har Alameen yace a kira masa Ameerah , even though tayi mamakin ma yadda akai yasan Ameerah har yasan sunanta, amma sanin cewar yanzu ba shine me mahimmanci ba , yasa tayi saurin kawar da zancen ma ga baki dâaya, a zuciyarta.
A hankali Mimi ta sauke ajiyar zuciya a bayyane sabida ta shaâko abunda take tsoran shaâkowa wato âkamshin turaran Moh, gashi tana matsowa âkamshin turaran yana âkara shiga hancinta, yana âkarasawa ta zama very uncomfortable , a âbangaran Ameerah ma haka yake .
Da suka shigo cikin falon sosai da âkyar Mimi ta dâan iya budâe baki ta furta â Assalamu AlaikumâŠâ Tana shiru itama Ameerah ta dâora nata â Assalamu Alaikum.â
Alameen ne ya amsa musu, sabida muryarsa suka ji, amma kuma gaze dâin da suke ji a jikin su yafi na Alameen dâin .
Cikin dâan wasa Alameen ya furta â Mene ne kuke faman sun kuyar da kanku wai ? Are you guilty or what kunyi wani abu ne ?â.
Kusan a lokaci dâaya suka hadâa baki wajan fadâin â Babu abunda mukai..â
saura kadâan kuma Alameen yayi dariya akan respond dâin Ću amma kuma ya share .
âDago idanuwanta Mimi tayi a hankali tana âkoâkarin kallan side dâin Alameen da take tunanin yana zaune a wajan.
Ai kuwa dâagowar ta ta yayi dai dai da lokacin da shima ya dâago fuskarsa daga kan phone dâinsa , hakan yasa idanuwan su ya shiga cikin na juna , maâana sukai Eye contact ba , ita ce tayi saurin dâauke kanta tana fadâin â Uncle Moh⊠Ina wuni?.â
Bai amsa ba , itama kuma Ameerah jin ta gaishe dashi , itama tayi saurin fadâin â Uncle Moh ina wuni.â Still basu jin muryarsa ba , kuma kansu a duâke yake shiyasa ba zasu gane ya amsa musu ko bai amsa musu ba .
Miâkewa tsaye Alameen yayi , yana dâaukar dâaya daga cikin ledar daya shigo dashi falon, sannan ya nuna wa Mimi waje â Mimi zauna kuyi magana mana da Uncle Moh..â sai ya kalli Ameerah â Ameerah ke kuma letâs go , nima I want to discuss something with you.â A nanne zuciyar su ya dâanyi sanyi duk da ba sosai bane, alamar basuyi laifi ba kenan.
Akan dinning Alameen ya zauna , sannan ya nunawa Ameerah kujerar da take facing dâinsa alamar ta zauna akai .
Babu musu jiki na rawa taje ta zauna, tana jiran maganar da yace zai yi da ita, amma kuma sai taga ya hadâe fuskarsa ga baki dâaya , kamar ba shine yayi murmushi ba , yanzu fuskar ga baki dâaya ya mayar da ita seriousness babu wani wasa kwata kwata a kanta, ledar da ya taho da ita ya ajje mata a gabanta and ledar tana da girma fa , da farko ba ta gane me yake nufi ba sabida bai mata âkarin bayani ba , sai da ya dâan kalleta tukunna ya sake nuna ledar da hannun sa â Finish everything AmeerahâŠâ
Lokaci dâaya taji ta âkware da yawu sabida batasan mene ne a ciki ba kuma a bata âkatuwar leda ace ta cinye komai da yake ciki, dole yasa mutum ya âkware ai .
Ji tayi tana so tayi masa tanbaya akan ledar, sai taga yayi mata âkaramun murmushi , at the same time murmushi kuma yana âbacewa , yana komawa wani irin gaze â Ameerah baâayi mun musu , dan haka do what I asked you to do, okay!â.
Jikin Ameerah sosai yayi sanyi, ji tayi hannunta kamar baâa jikinta yake ba , sabida tama kasa motsa shi sosai , amma a hakan kuma tayi âkoâkarin soma budâe ledar.
Wani hadâiyar yawu tayi tana zaro ido sabida manya manyan robar ice creams da suke ciki, da kuma chocolate kala kala kunya bana wasa ba.
Ita kanta sai da taji âkwalla tana shirin tarar mata a ido sabida kawai ta yadda cewa Alameen so yake ya kasheta , shiyasa zai bata wannan abun yace wai ta cinye kamar wata mayya.
A wajan Mimi kuwa, tana tsaye ita bata zauna ba kuma bata bar wajan ba sabida ta rasa me za tayi , tunda ta gaishe sa bai amsa mata ba .
Shi kuwa sai da ya gama abunda yake da wayansa , lokacin har ta dâan gaji da tsayuwa , dâan yun âkurawa yayi ta dâan ka ma wani abun zai mata sai kawai taga ya matsar da center table dâin gabansa, ya ajje ledar da take kai a âkasa , da ido ya nuna mata ta zauna a can carpet dâin.
Duk da sheâs little bit suprise haka dai ta zauna akan carpet ta tan kwashe âkafarta tana jiran abunda zai ce , sai ya kawai taga ya matso mata ledar ga banta, murya a kausashe ya furta â Finish it all MimiâŠâ take taji waji rasssss gabanta ya fadâi duk da dai bata ma san mene ne a cikin ledar ba amma tunda yace ta cinye komai tasan ba abun alkairi bane .
Kuma yadda yayi magana bai bada wani second chance da zaâayi masa musu ba tunda cikin umarni yayi maganar.
Haka tana tsoro ta budâe ledar , ice cream ne da chocolate kamar yadda yake na Ameerah itama nata hakan yake, haka ta cuccuro komai da yake ciki, ta ajje a gabanta amma kuma ta kasa taâba komai sabida tasan dai bazata iya cin wadâan nan abubuwan ba dan dagaske cikinta a cike yake , wanda suka ci ma bai gama narkewa ba , balantana ma ace su kuma shan wannan ai ba zasu iya bacci yau ba .
Cikin sarâkewar murya ta furta â Uncle MohâŠâ bata âkarasa abunda zata fadâa ba , ta kuma jin saukar kausash shar muryarsa kamar bashi ba kuma bama ita yake kallo ba â Karki bari na sake maimaita miki magana ta Mimi! Finish it all .â
â Ni bana jin yunwa , bazan iya cin su ba wallahi .â Duk da a tsorace tayi maganar , amma sincerely speaking , gaskiyar ta kenan ta fadâa sabida dâazu ba âkaramun musun shan ice cream dâin nan sukai ba , har da na Allah ya isa sai da suka sha shiyasa ko waccen su cikinta yayi full sosai .
â Karki bari na sake maimaita maganataâŠ.â Yanzu a hankali yayi maganar yadda ita kadâai ce zata ji me yace.
Da sauri ta mayar da âkwallar idanuwanta sabida a yanzu kam ji take kawai zallan mugunta ne wannan yake mata tunda tace ta âkoshi amma kuma yaâki acknowledging hakan.
Strawberry ice cream dâin da yake gabanta ta soma janyowa , ta dâauki spoon dâin shan ice cream dâin, akaro na farko da ta saka a baki , sai taji ice cream dâin ma bai mata dadi ba ga baki dâaya , har wani dâaci dâaci taji harshenta yana mata.
Kallan ice cream dâin tayi, sai kuma ta kallesa ko zai ce ta barshi, amma bai ma san tanayi ba sabida fuskarsa ga baki dâaya bata wajan ma .
Haka ta kuma dâaukar wani spoon dâin tasha , duk da taji kamar za tayi amai amma haka ta hadâiye .
A spoon na hudu da tayi ne taji ba zata iya âkarasawa a bakinta ba , yasa ta dâan tsaya tana zaune numfashi , dan ji take ko wana irin lokaci ma zata iya amayar da wanda tasha âŠâŠ.
A âbangaran Ameerah ita ko taâba kayan ba tayi ba ta kalli Alameen â. Dan Allah kayi haâkuri shine maganar da ta soma fito mata bayan shi kuma babu wani abu da tayi yunâkurin cewa .
Babu yabo babu fallasa ya furta â Kar na sake miki magana akai , finish everything thing .â
Haka ta janyo ice cream itama ta budâe tana sha kafin ta dâan tsaya, gwanda ita ta âkoâkarta tayi spoon 10 ba kamar Mimi da tayi ba , kuma tana shan na goman ta ajje spoon tana fadâin â Allah ba zan iya sha ba , idan nasha wannan abun amai zanyi wallahi.â
Without any care a kan face dâin Alameen ya furta â Haka zaki shanye sa , ko kina so ko bakyaso, you guys love sweet thing ai ko? Am helping you , so maza jigaba da shaâŠ.â Yayi maganar yana tsareta da idanuwa , haka dan dole ta soma tura ice cream bakinta , ga sanyi gashi kuma taji ya dena yi mata dadâi .
Spoon 3 ta sakeyi ta ajje spoon dâin tana sun kuyar da kanta âkasa .
â Cikin ki ya çıka ko?â Yayi mata tanbayar yana kallanta .
Da sauri ta jinjina masa kai alamar â Eh âŠâ sai ya miâke tsaye yana rufe ice cream dâin, Ameerah ta sauke ajiyar zuciya a tunaninta ai ya haâkura ne , har yaje yasa ice cream a fridge, sai a time dâin Ameerah ta dâan samu chance dâin duba Mimi, ganin ta zaune da robar ice cream wani dariya yazo mata , amma kuma bata bari tayi dariyar ba ta hadâe abunta sabida Moh da yake wajan .
Tana cikin hadâiye dariyar Alameen ya fito ya kalleta â Letâs go Ameerah..â yayi maganar yana nufar hanyar fita , amma bawai ta main door ba , ta backdoor dâin part dâin .
A tunaninta shikenan an gama da ita , tayi saurin miâkewa tana fadâin â Nagode .â Bai ce mata komai ba kuma bai AMSA mata ba , suka fita backdoor.
Wajan so silent ne , sai kaga kamar wani gida ka shiga da ban sabida wajan akwai compound babba me kyau , yana da fadâi sosai da sosai, iska tana faman kadâawa wajan so dummy akwai haske amma bawai irin can sosai ba .
âDan tsayawa Ameerah tayi sabida batasan hanyar da zata bi ba ta koma part dâin nasu shiyasa cikin rashin sani ta furta â Uhm uhm Uncle Alameen ban.. bansan wajan ba..: tayaâŠâ sai tayi shiru ganin ya kalleta .
Lokaci dâaya yayi mata murmushi â Bakisan wajan ba ko?.â Tayi masa murmushi tana dâaga masa kai cikin confusionâŠ.â
â And kin âkoshi sosai ko?â Ya kuma yi mata tanbayar ita kuma ta sake jinjina masa kanta alamar eh .
Wani murmushi Alameen yayi yana nuna mata compound dâin â Donât worry yanzu zaki dawo dai dai trust me.
So now abunda zaki soma shine jogging , trust idan kika gudun 10 minutes zaki ji cikin ki yayi normal .â
â Jogging kuma?â Kamar za tayi kuka tayi tanbayar .
Shi kuma ya jinjina mata kansa â YES or ba zakiyi ba?,â
Shiru Ameerah tayi babu bakin magana hakan yasa ya furta â Then start . Kafin na canza shawara.â
Karo na farko da Ameerah take so ta fadâi abunda yake ranta tun dâazu , ga kwalla da suka soma sauko mata a zuciya , idan ta kalli idansa tace za tayi masa musu sai taga bata da wannan zarran hakan yasa ta goge kwallanta , ta soma gudu a cikin compound dâin.
Mimi kuwa tana zaune tuni âkwalla ya soma durowa akan fuskarta dan ba zata iya shan wannan ice cream dâin ba , bai ce mata komai ba , ya gama danne dannen da yake wayarsa kusan 25 minutes, tukunna ya ajje wayar.
Ganin yanzu hankalinsa zai dawo kanta ta soba zubar da âkwalla duk dan sabida ya haâkura da maganar shan ice cream dâin .
Kallan ice cream dâin da ya soma melting yayi, kafin ya kalleta , gashi itama dâin shi take kallo irin kallan tsoran nan da rashin mafita.
Gaze dâinsa ya canza,hakan yasa tayi saurin saukar da idanuwanta âkasa tana dâan wasa da hannunta.
â MimiâŠ.â Ya kira sunanta , ba cikin cold ba sannan ba gentle ba .
Da âkyar ta iya fadâin â NaamâŠâ
â Do what I asked you to do, 20 minutes na bakiâŠ.â
Cikin sauri ta hadâe hannayenta biyu alamar roâko tana zama akan âkafafuwanta â Dan Allah kayi hakuri Uncle Moh, wallahi ba zamu sake ba âŠ.â
Kallo dâaya yayi mata ya dâauke kansa, yama jinginar da jikinsa a kan kujera yana lumshe idanuwansa , hakan yasa taji kuka yanasan zuwan mata , rai a âbace ta dâan goge hawayen, ta dâauki robar ice cream bata ma dâauki spoon ba ta soma shan ruwan da yayi melting.
Tana tsakiya da sha tari ya dâan âkwace mata , shiyasa ta ajje da sauri, ga kuma aman da yake âkoâkarin tahowa.
Da sauri ta miâke tsaye , ta wuce dâakin da aka kwantar da ita lokacin da bata da lafiya tunda a âkasa ne, ta wuce tai amanta , kuma sosai tayi aman, tana gamawa ta gyara wajan , ta wanke face dâinta sosai da bakinta tana ajiyar zuciya, tukunna ta budâe âkofa zata fito.
âKırgınsa da yake wajan ne ya dâan tokareta, bata san yana wajan ba har sai da ta dâan buga kanta da jikinsa, tana saurin komawa baya kadâan da mamakin ganin sa a wajan.
Amma sanın cewa ta dalilinsa tayi aman haushinsa ya kamata , ta raâba zata wuce , yasa hannu a âkugunta ya dawo da ita cikin ban dâakin.
Again ta kuma âkoâkarin wucewa za ta fita , sai bai riâko ta ba , ya bari ta fito daga cikin toilet dâin, sai dai hannunta da ya riâko, ya dâan janyo ta kadâan yana jinginar da ita da jikin bango .
Take zuciyar Mimi ya soma bugawa boom boom boomâŠ..
â âDago ki kalle ni.â Yayi maganar kamar cikin radâa .
âDan dâagowa tayi ta kallesa, zata janye idanuwan amma ya tsayar da ita ta hanyar shigar da nasa idanuwan.
Sosai ya âkure âkwayar idanuwanta da kallo na wasu mintuna, lokaci dâaya wani murmushi ya dâan sauka akan laâbâbansa wanda ta kasa ganewa maâanar murmushin, sai kuma ya kama hannuwanta guda biyu yana kallan tafin hannun nata , nan dâin ma wani dirty smile yayi , sannan ya kama hannun zai kai baki, maâana zai yi kissing dâin hannun sai tayi saurin janye hannunta tana âboye su duka a bayanta , yadda bazai âkara kamawa ba .
â What? Hannun naki ne bakya so nayi kissing?â
Yau da confidence dâinta ta furta â Yes ai ba miji na bane kai kuma kasan Allah ya hana wannan kuma zunubi ne , idan kayiâŠâ bata ma âkarasa ba yayi mata peck a baki , ita kuma tayi saurin dâauke fuskarta , tana dâaukar hannu zata saka a bakın, cikin sauri ya janye hannun yana dâan dâago wuyanta da âkarfi har sai da taji zafi sabida aush dâin da tace .
â Ni zanyi kissing dâin ki , ki saka hannu a baki? Me zakiyi? Donât you dare try that , if not you will regret it.â
â Uncle Moh wai ya kake so nayi, taya zaâai dan Allah ka dâinga kissing dâina bayan ni da kai munsan hakan haramun ne , ni wallahi banaso ka dena , banaso Allah yayi fushi da mu, nidai ka bari Allah banaso.â
Shiru yayi for second, tayi tunanin ko be ji abunda tace sosai ba , shiyasa ta dâan dâago da fuskarta tana kallansa, aushe shidâin ma kallanta yake kuma har ta saukar da idanuwanta âkasa bai dena kallanta ba .
â Mimi can you wait for another 7 days ?â Kamar Wanda yayi magana a zuciya haka yayi maganar, ita kuma bata jisa sosai ba sai tace Uhm?â.
â in the next 7 days your birthday right?â.
Ta dâaga masa kanta alamar â eh .â
â Then you can asked me anything you want to know and I promise to tell you everything! I mean everythingâŠâ.
Batasan lokacin da ta furta â But why?ââŠ.
Sauko da face dâinsa yayi dai dai face dâinta , ya dâan dâora goshinsa akan nata , sannan ya dâora karan hancinsa akan nata , hakan yasa suke iya shaâkar numfashin junan su sosai.
Hakan da suke ya furta â Donât worry , ki soma counting in the next 7 days but you will pay a huge priceâŠ. Let go back , ki shanye ragowar ice cream dâinkiâŠâ ya dâan matsa yana riâko hannunta ita kuma taâki motsawa hakan yasa ya kalleta .
Kamar za tayi kuka â Uncle Moh wallahi bazan iya shaba , idan nasha amai zanyi sosai .â
â Then sai ki yi aman, but you most finish it âŠ. Thatâs your punishment.â Bai ma bata wani chance dâin magana ba ya soma tafiya da ita , ita kuma sai faman âbata fuska take amma babu abunda ya canza zani a hakan, ya dawo da ita falo ya dâauko ice cream da da ya saka a fridge ya miâka mata , ita kuma ta dâan marairaice masa fuska tare da turo lips dâinta , shi kuma a maimakon yayi acknowledging yadda tayi da fuska sai ya saka hannu yana shafa lips dâin , har sai da taji wani iri ta mayar dashi.
â Donât try what you did again MimiâŠâŠ if not , I wonât forgive you Mimi kinji?â. Da sauri ta dâaga masa kai alamar tohm .
Sai ta juya zata bar wajan, ya dakatar da ita ta hanyar sake ambatan sunanta â Mimi?.â
Ta dâan waigo ta kallesa .
â You can goâŠ.â Ya fadâa yana dâauke kansa, ita kuma tayi saurin fadâin â Good night..â .
Da kai kawai ya amsa mata ba tare da yace komai ba, ita kuwa da sauri ta bar wajan sabida kada ma ya tsayar da ita , yana ganin irin saurin da take kuma amma sai yayi kamar bai ganta ba , har ta fice daga sashen.
Sai a lokacin ya dâan dâago face nashi ya kalli hanyar da tafi â Mimi will you really take whatâs coming?â. Yayi maganar cikin low voice da duk âkwaâkwâkwafin ka ba zaka gane me yace ba .
Mimi tana fita kuwa âkafa kif mai naci banbaka ba , ya gudu part dâin sun.
A nan ta tarar da Aya da kuma a kwati guda biyu, Aya dâin kuma tana tsaye , da waya a hannunta , hakan ya nuna waya take.
âDan tur⊠Mimi tayi tana kallan jakun kunan da mamaki duk da dai bata fito tayi magana ba , har abunda Moh yayi mata yanzu yaso kauce mata ma.
Aya da take waya kuma da hannu tayi mata nuni da part dâin Mamy.
Babu shiri Mimi tayi saurin ajje ice cream dâin ta nufi part dâin Mamy a guje .
Tana zuwa bata ma tsaya âKwanâkwasa âkofa ba kawai ta budâe âkofar , wadâan da ta gani a tsatstsaye ne yasa ta âkwalla wani âkara ta nufar su za tayi hugging dâin su .
Mamy ne da Baffa suka dawo sai Shukura da take tare dasu .
Gabaki dâaya dariya ma suke mata sabida abunda tayin yanzu,
Baffa ne ma ya furta â Oh ni Mimi na har yanzu dai batasan ta girma ba , ko dai mu koma bakiyi kewar mu ba?â.
Turo baki Mimi tayi â Haba Baffa wallahi 2 days dâin nan da kukayi nayi missing dâin ku sosai , ka tanbayi ma Aunty Shukura , zata sheda hakan wallahi naji dadâi da kuka dawo , thank god ma da bakuyi kwanakin da kuka ce za kuyi ba .â
âToh Allah ya shirye ki Mimi , tunda ba zaki bari mu huta ba kafin ki soma complain dâin nan naki MimiâŠ.â Cewar Mamy tana dâan hararar ta.
â Baffa , kaganta ko ?.â Tayi maganar cikin turo lips .
â Rabu da ita Mimi, kisan halin Mamyn nan taki , bata so taga muna rahanmu sai tayi kishi, ya kike Mimi na ? Hope you enjoyed your dayâŠâ
â No Baffa gidan is so Boring wallahi da bakwa nan , but why did you guys change your mind? Like kunje zakuyi weeks a think.â
â Dole kema kinsan zamu dawo ai sabida school dâin ki , and muma mun kasa zama sabida bakya nan, wajan so boring Mamy har cewa tayi dama mun taho dake.â
Kallan Mamy, Mimi tayi ganin ta dâauke face dâinta tana dâan âbaâbâbata rai na wasa yasa dĂŒk kowa yayi dariya Mimi kuma ta âkarasa wajanta tana rungumeta tare da fadâin â Mamy naâŠ. My mozaaâŠ..â
â Yanzu Mamy ni bakuyi kewata ba sai Mimi , ni da nake zuwa school atleast ai ya kamata ku bani duk attention dâin ku, ku âkyale Mimi haka .â Cewar Shukura.
Kafin kowa yayi magana Mimi tayi mata gwalo â Eh dâin waya ce ki âki zuwa a âyar auta .â
Fito Shukura ta dâauko zata âkwala mata Mimi tayi saurin âbuya bayan Mamy tana fadâin â Mamy kin ganta ko?â
â Wallahi daga dawowar mu Mimi ba zaki soma sani magana ba , naga lokacin baccin ki yayi , kema Shukura lokacin karatun ki yayi duk kowa yaje yayi harkan ga bansan bawai kuzo kuyi ta samu magana ba , ku in magana baya damun ku , toh mu yanayi ya kamata ku bar Baffa haka ya huta âŠâ
â Kai MamyâŠ.â Kusan time dâaya Mimi da Shukura suka hadâa baki, hakan yasa Mamy ta miâke tsaye, duk sun san halinta kuma shiyasa sukayi saurin yi musu good night suna fitowa , a time dâin ne ma Mimi take cewa Shukura â Aunty Shukura daman kin san zasu dawo shine kika âki fadâa mun?.â
â Ke nima bansan zasu dawo ba , kawai gani nayi Aya ta shigo dasu , aushe already tasan da dawowar su ? Kuma kika tafi shan ice cream ke da Ameerah? Dan naga Zarah yau sabida shim
Sheâs less busy kawai sai naga tana sharan part dâin nan bayan all maid da suke cikin gidan nan but ace za tayi sharan falo da daddare ? Wai âkafarta ciwo yake , and ku kuma kun tafi shan ice cream , ina ma kuka je?.â
A maimakon Mimi ta amsa mata sai ta jefa mata nata tanbayar itama â Zarahn ce ta zauna shara kuma da daren nan?.â
Kai Shukura ta jinjina mata duk d itama tayi mamaki , da sauri Mimi ta furta â Ina zuwa Aunty Shukura âŠâ daga nan tabar wajan da sauri bata bari ma Aya ta tsayar da ita ba ta wuce part dâin su Ameerah , lokacin tasan Mama tana part dâin Uncle Bashir tunda taga motar sa alamar ya dawo shima.
âDakin Ameerah ta nufa tana zuwa ta âKwanâkwasa sau dâaya sannan ta budâe âkofar .
A kan gado ta hango Ameerah tayi nashe nashe ko motsin kirki ma bata yi .
Ganinta da Mimi tayi a haka ta wani âkyalâkyale da dariya tana âkarasowa wajan nata .
Hannu ta sa ta dâan dâaka mata duka cikin wasa , ita kuma Ameerah ta dâago da fuskarta ta harareta tana âkara komawa kwancen da take .
Cikin dariya Mimi ta furta â Haba âkawalliya , wannan hararar ta mece ce ? Bani na kar zoman ba fa.â
â Toh idan bake bace wacce ne? Aushe wannan guy dâin mugu ne , sai yayi ta faman yin murmushi kamar na Allah aushe âkasun gumin mugu ne . Har da Jogging fa ya sani, Wlh inayi sau dâaya nayi sumar âkarya shikuma ya juya zai dâauko ruwa tuni na arcs duk da bansan hanya ba haka na samu na dunga zagane har na gano hanya wallahi babu ni babu biye miki.
Ke kin riga kin saba da mugancin Uncle Moh ni kuma ban saba ba Allah dai ya isa na , wallahi abokin Uncle Moh dâin nan mugu ne .â
Wani dariyar Mimi ta kuma âkyalâkyalewa dashi har da hawaye tana fadâin â Aa fa , kar muje ayi irin na novel ku fadâa soyayya daga baya .â
â Allah ya tsaye , wallahi babu me rabani da Abdul dâina ( Her boyfriend)âŠ.â
â Lalle yayi miki kyau me boyfriendâŠâ
Ameerah bata ce mata komai ba sai da ta soma janyo hannunta ta zauna â Mimi kinga Zarah kuwa yanzu?â.
â No why?.â
â Lokacin da na fito fa naganta zata je part dâin su sai na tsayar d Ita , wallahi wani irin harara ta bankamun tana ja mun tsaki kamar wacce tayi mata wani abu.
Kamar irin taga wata maâkiyarta , naga dai lafiya muka barta .â
Hannu Mimi ta budâe cikin halin ko ina kula ta furta â Thats her own cup of tea âŠâ
đą LITTLE ANNOUNCEMENT đ€đ
Book 1 zai Æare a Page 50 đ„čđ
Duk wanda yake son ci gaba da karanta Book 2 & 3, farashin yanzu shine âŠ800.
Once Book 1 ends, the price will be âŠ1,000.
So idan kina/kana son ci gaba da journey Éinmu, âŠ800 offer Éin nan yana nan har zuwa Page 50. đ€
Payment Details:
đŠ Bank: ZENITH BANK
đ€ Account Name: AISHA UMAR
đł Account Number: 2681892316
Bayan kin biya, ki turo proof of payment + sunan ki domin a tabbatar da payment Éin. â€ïž
Thank you so much for all the love and support! đ„čđ€đ
_________________
To be continued⊠đ„
Aysha Galadima đ€đż
***
***