Free chapter 路 Read without an account
TSORO DA TAUSAYI馃槡
INUWAR 茦ADDARA 馃枻
Book 1
Page 12 鉁嶏笍
"Sayyid"
Ammah ta kira sunansa, tsayawa ya yi cak tare da dawowa baya. Nuna masa inda ya tashi ta yi, hakan ya sa ya koma ya zauna a hankali, fuskarsa a daure. Ji yake kamar ya ha蓷iye zuciyarsa don ba茩in ciki.
Ita kuwa baiwar Allah, ba ta daina wannan ihu da sambatu da take yi ba, sai da Ammah ta kira sunanta sannan ta yi shiru.
"Leenah, ki yi shiru, kin ji? Tashi ki zo nan. Ki daina tsorata idan kika gan shi, yayan ki ne, babu abin da zai yi miki."
Rooman da ta tsayar da dariyarta saboda ganin yadda Leenah ta kwanta a 茩asa, abin ya ba ta dariya sosai. Hakan ya sa ta sake yin magana cikin dariya.
"Ammah, ki 茩yale ta. Ni ma na gaya mata babu abin da zai yi mata, amma ta 茩i yarda. Ji yadda take ihu, don Allah! Kamar ta ga aljani."
Wata harara Leenah ta jefa mata tana goge hawayenta, tare da zubar da wasu sabbi tana cewa:
"Ai yanzu na sake yarda da abin da ake fa蓷a a duniya, babu tabbas! Yanzu na ga zahiri. A gaban Rooman ake neman kashe ni, amma ba za ta iya kawo wa rayuwata 蓷auki ba. Hmmm, ai shikenan!"
Tana maganar tana hawaye, kuma tsakaninta da Allah take wannan kukan. Ita kuwa Rooman, maganar dariya ta ba ta sosai.
Sai da Ammah ta sake magana sannan Leenah ta mi茩e ta nufi gurin da take zaune, kuma har zuwa lokacin jikinta bai daina rawa ba.
Ba ta yarda ta sake kallon inda yake ba, kawai ta tunkari gurin da Ammah take zaune.
Tana zuwa, ta shige jikinta ta kwanta, har da sauke ajiyar zuciya. Shi kuwa Sayyid kamar zai cinye ta don harara. Mamakin yadda ta shige jikin Ammah yake yi, kamar ta samu jikin uwarta.
Shafa kanta Ammah take a hankali, cikin sigar rarrashi ganin yadda hankalin yarinyar ya tashi sosai. A hankali ta fara cewa:
"Me ya sa kika tsorata haka? Yanzu ga shi kin zubar da maganin, kuma shi nake ta jira. Na so ma na aika Sayyid ya amso min kawai..."
Ai da sauri ta 蓷ago kanta. Ta ma manta da wanda take kusa da shi, har wani zaro idanuwanta masu matu茩ar kyau da 蓷aukar hankali ta yi, ba tare da ta san ma ta zaro idanun ba.
"Ammah, wai shi Yaya Madugu 蓷in za ki aika gidanmu? Da mun shiga uku wallahi! Allah ya taimake mu. Ai duk sanda ya..."
Wata tsawa ya daka mata, wanda hakan ya sa maganar da take yi ta ma茩ale a ma茩ogwaronta.
"A gidan uban wa na zama yayanki? Iyeeh? Na ce, a gidan uban wa na zama yayan naki? Neman suna kike ko me? Tashi a jikinta, aljanar banza mai kama da mayu! Kin zo kin wani kwanta kamar kin samu jikin uwarki. Kuma idan ba ki tashi kin je kin gyara gurin da kika 蓳ata ba, yau babu abin da zai hana Rocky cinye wa蓷annan 茩afafun naki, tashi!!!"
Girgiza kai kawai Ammah ta yi. Ba ta san mene ne ha蓷in Sayyid da Leenah ba. Ita tana matu茩ar tsoronsa, shi kuma ya yi matu茩ar tsanarta, kuma tun tana 茩arama abin ya samo asali.
Yarinyar ta taso ne da wani irin surutu da kuma tsiwa. Ana kawo mara Leenah a lokacin kuma tana da cikin Rooman, shi kuma Madugu haushi da kishin yadda Ammah take goya Leenah tana lelen ta ya sa gaba 蓷aya ya tsani yarinyar.
A duk unguwar nan, babu gidan da Ammah take shiga sai idan ya zama dole. Mahaifiyar Leenah ce suke zumunci sosai da Ammah, tun bayan haihuwar Leenah.
Da yake kuma Ammah ba mai yawan shiga mutane ba ce, babu inda take yawan zuwa. Ita kuma Ammah tana son Leenah, hakan ya sa idan aka yi mata wanka sai a kawo wa Ammah ita.
Shi kuwa Madugu ba ya so, saboda ya tsani ganin yadda Ammah take 蓷aukar Leenah ta goya ta. Tun daga lokacin shi ma ya tsane ta. Ita kuma tun farko ba ta zuwa ko kusa da inda yake saboda tsoron da yake ba ta.
Katse tunanin nata ta yi saboda jin muryar Rooman tana cewa:
"Kin ga ki tashi, na taimaka miki mu gyara gurin kafin lokacin makaranta ya yi. Tunda Yaya ya ce sai kin gyara, na san dole za ki gyara gurin nan. Ga lokaci ya kusa 茩urewa."
Wani kallo ya yi wa Rooman mai kama da gargadi, yana harararta kamar idanunsa za su fa蓷o. Cikin takaicin irin iyayin na Rooman, ya ce:
"Bari na ga 茩afarki a gurin nan, ki ga yadda zan dake ki!"
Aikuwa cak ta tsaya. Hakan ya sa Ammah ta 蓷ago Leenah da ke jikinta cikin sigar rarrashi ta ce:
"Tashi ki 蓷auko mop ki goge gurin, kin ji, yar albarka? Ki daina tsoron shi, babu abin da zai yi miki. Kuma zan yi maganinsa, kin ji ko?"
Ammah ba ta san yadda haushin da yake ji yake 茩ara 茩ule zuciyarsa ba.
Ita kuma sarkin tsoro, da 茩yar ta iya mi茩ewa. Gani take kamar idan ta bar kusa da Ammah, zai iya binta ya kashe ta.
Hanyar 蓷akin Rooman ta nufa ba tare da ta lura da inda take bi ba.
Muryarsa ta dawo da ita hayyacinta, tare da sake jefa ta cikin wani irin tsoro.
"Ke!!!"
Muryarsa ta dawo da ita hayyacinta. Ya waiga ya kalli Ammah kamar zai fashe da kuka don takaici.
"Haba Ammah, don Allah ki duba abin da yarinyar nan take yi fa! Kuma a haka kike bari tana shigowa nan? Wata rana idan ba kowa fa, ta zo ta rufe ki da duka? Ji abin da take yi! Kina gani, kin san tana da lalurar hauka, amma kina 茩yale ta!"
Ammah ta 蓷an yi shiru, tana kallonsa cike da mamaki. Ta san halin Sayyid sarai, in ta ci gaba da mai fa蓷a ba zai fahimta ba, hakan ya sa ta ce:
"Sayyid, ka daina fa蓷in haka. Leenah ba mahaukaciya ba ce. Yarinyar nan kana shiga ha茩茩inta da yawa, Sayyid. Me ya sa kake haka ne, don Allah? Yadda Rooman take 茩anwarka, ita ma haka ne."
Ya 蓷an juya kansa gefe yana fitar da iska daga bakinsa, 茩ara daura fuska ya yi.
"Ni kanwa 蓷aya gare ni a duniya, kuma ita ce Rooman. Ki daina fa蓷in haka, Ammah."
Yana maganar yana sake hararar Leenah. Ita kuwa cikin sauri ta 蓷auko mop 蓷in ta fara goge gurin, tana yi tana kuma kuka. Sosai take kuka, in ta goge ta goge sai ta tsaya ta share hawayenta.
Ga tsoron 蓷aga kanta kar ma ta gan shi, saboda duk da haka ji take a jikinta, domin girmansa take gani sosai.
"Idan na 茩ara jin kukan ki a nan, to ki sani sai na sa wu茩a na sake yanka wannan bakin naki kamar gidan tsutsa."
Yadda ta tsinkayi muryarsa ya sa ta yi tsit daga kukan da take yi, sai faman jan ajiyar zuciya.
Sai da ta gama gyara gurin tas, sannan ta tsugunna tare da rufe idanunta ta ce:
"Yaya Madugu, na gama gogewa, ban bar ko digo 蓷aya ba."
Ko lallonta bai yi ba, ya ce:
"Saita ma kanki hanya."
Aikuwa da gudu ta bar falon. Ba ta tsaya ba ma balle ta yi wa Ammah sallama. Sai Rooman ce da ta mi茩e ta shiga 蓷akinta ta 蓷auko hijab 蓷inta da jakar makarantar ta fito ta ce wa Ammah da Madugu ta tafi makaranta.
Haka ta fita ta bar Ammah tana yi wa Madugu fa蓷a a kan ya sauya halinsa. Amma jinta kawai yake yi. 茦arshe ma tashi ya yi ya fita daga 蓷akin, ya bar gidan gaba 蓷aya. A zuciyarsa yake ji yau duk wanda ya ta蓳a shi akwai 茩ura.
Ita kuwa Rooman tana fita, gidan su Leenah ta shiga. Ta tarar da ita tana can bakin bishiya tana wanke fuskarta, kuma ba ta daina kukan ba. Ga Mama sai fa蓷a take mata a kan ta yi maza ta shirya, kuma ta yi mata shiru kafin ta zo ta tarar da ita a gurin. Sai faman ajiyar zuciya take yi.
Gaishe da Mama Rooman ta yi sannan ta 茩arasa gurin Leenah tana fa蓷in:
"Haba kawata me capacity, duk tsoron ne har yanzu? Mama, wai fa Yaya ta gani a falon, shi ne ta sake maganin ya fa蓷i ya fashe a 茩asa, shi ne Yaya ya ce sai ta goge inda ta 蓳ata."
Rooman ta yi maganar tana kallon Mama. Ita kuwa Mama takaici ne ya sake kamata domin ba ta san cewa ta zubar da maganin da ta aike ta ba. Cikin takaici take kallon Leenah.
"Ai ban ji da蓷i da bai ha蓷a mata da bulala ba. Ai zan ga Sayyid 蓷in, duk ranar da ta sake ganinsa ta gudu, to ya sa bulala ya zane jikinta. Yanzu ga shi babu damar sake amso wani maganin a yau, dole sai gobe. Gaskiya ban ji da蓷i ba wallahi."
Tana maganar tana takaicin yadda Leenah ta zubar da maganin. Tsaki Mairo da take can bakin ma茩warara tana wanke-wanke ta yi tana cewa:
"A yi dai mu gani in ta so za ta hura wuta. Ba dai ke kin dage sai kin yi ala茩a da wa蓷annan annoba ba? a kaf unguwar ya addabi kowa,yar taki 蓷aya jal, ita ma da kika haifo mana bala'i, to shi ne zai yi ajalinta. Muna nan muna kallo. In ba munafurci ba, har meye na ala茩a da matar da 蓷anta ya addabi gari gaba 蓷aya? A nan a gaban idanunki ya shigo har gidan nan ya yi wa yaron nan mugun duka, amma da yake ba 蓷anki aka yi wa ba ai ba ki damu ba. Kuma kada ki 茩ara gayyato mana shi nan atohh."
Haka dai Mairo ta ci gaba da sababin ta tana jin ba茩in cikin dukan da Madugu ya yi wa yaron nata, da irin yadda karen sa ya yi kaca-kaca da shi. Shi ya sa a duniya ta tsane shi kamar mutuwarta.
Ita dai Mama ba ta ce komai ba har Mairo ta gama masifar ta. 茒aki ma ta shige bayan Leenah ta taso daga bakin bishiyar suka shiga gaba 蓷aya.
Sai da ta shirya sannan Mama ta yi musu addu'a suka tafi makaranta.
Yau kwana uku kenan da faruwar hakan. Da misalin 茩arfe goma da rabi na safe, ita Leenah tana 蓷aki tana bacci, da yake yau ba makaranta.
"Aishatu! Aishatu!!"
Kiran Baba ne ya tashe ta daga baccin da take yi, domin kuwa akwai 茩auna mai girma tsakanin ta da bacci. Tashi ta yi tana goge idanunta tare da sanya takalminta ta fito.
A tsakiyar gidan ta tarar da Baba, ga yayarta Karima tana tsaye kusa da Baba. Zuwa ta yi ta tsugunna ta gaishe shi. Kallonta ya yi cikin kulawa da son da yake yi wa yarinyar, domin ita ce autarsa, kuma ita ka蓷ai Mama ta haifa, sauran duk yaran Mairo ne.
"Aishatu, sarkin bacci, ga shi kuma na katse miki baccin naki. Ga yar uwarki nan, ku shirya yanzu ku je gidan gwaggon ku, ba ta jin da蓷i. Ku gaishe ta sannan ku yi mata wasu ayyukan. Idan an yi la'asar sai ku dawo. Kada ku bari magriba ta yi, kun san ba na son unguwar yamma."
Yana maganar yana mi茩awa Karima ku蓷in da ya ciro daga aljihunsa. Amsa ta yi suka ha蓷a baki gurin amsa masa da toh.
Addu'ar dawowa lafiya Mama ta yi masa, yayin da Mairo take ta faman cika tana batsewa. Babu wanda ya bi ta kanta. Baba ya sa kai ya fita daga gidan.
Yana fita, Karima ita ma ta koma 蓷akinsu domin shiryawa. Ita kuwa Leenah ba ta tashi a gurin ba har sai da Mama ta yi mata magana sannan ta tashi. Har zuciyarta ba ta ji da蓷in ha蓷a ta da Karima da aka yi ba, domin ba sa shiri ko ka蓷an. Karima ta girme ta domin ta ba ta shekara kusan biyu, kuma Karima ita ce autar Mairo.
Ba sa shiri ko ka蓷an da Leenah. Sanin haka ya sa Mama ta yi mata magana a kan ta tashi ta je ta yi wanka ta shirya, domin kuwa in ta tsaya ba ta lokaci ba, jiran ta za ta yi ba. Ita kuma ba ta iya zuwa gurin mai nisa ba ita ka蓷ai.
Haka ta tashi ba don ranta ya so ba, ta shiga ta shirya. A gaggauce ta yi wanka ta fito, wata doguwar riga ta 蓷auko mai sawai-sawai, da yake ba ta shiri da kaya masu nauyi. Sai da ta sa kayan sannan Mama ta ce mata:
"Da kin koma kin canza wannan riga, Leenah. Kin ga ba ta da kauri, ki saka atamfa mana. Ni ban san mene ne ha蓷inki da kaya ba, ga su jibge, sai dai na gaji na yi kyauta da su."
Cikin maganar ta ta shagwa蓳a ta ce wa Mama:
"Ni fa Mama, ba na son atamfa, damun na take a jiki, duk in yi ta faman zufa, ga 茩ai茩ayi."
"Allah ya shirye ki to. Ga abinci ki ci da sauri kafin ku wuce..."
Mama ba ta gama maganar ba suka ji maganar Karima tana fa蓷in:
"In yarinya ta tsaya ,wucewa zan yi na barta a to, don ba baiwarta ba ce da zan zauna jiran sai ta gama iyayi."
Ko abincin ba ta tsaya ci ba, ta ce wa Mama idan sun je can za ta ci, sannan ta bi bayan Karima da gudu, har ta fita daga gidan ma.
Ko da ta fita, har ta yi nisa, ita domin ta san Leenah ba ta iya sauri ba. Ita kuma tana bakin cikin jerawa da Leenah 蓷in, duk da take fara sol, ga shi kuma tana 茩arawa da mai, kuma tana ganin ta girme wa Leenah. Amma duk inda za su shiga tare sai an yaba da halittar Leenah 蓷in. Haka ake fa蓷a, duk gidan babu mai kyawunta, duk da kasancewarta ba fara ba.
Har ta kai bakin titi, Leenah ba ta 茩araso ba. Sai da ta ga tana niyyar tafiya ta bar ta, hakan ya sa ta 茩ara da gudu ta cimma ta, ita ma ta shiga.
Ranar dai a gidan gwaggonsu suka wuni, wanda sam wunin bai yi wa Leenah da蓷i ba saboda yadda Karima take yawan yi mata shagube da zagi. Don ma ita ma wani lokacin idan abin ya kai ta bango tana ramawa, ga shi gwaggonsu bayan Karima take bi saboda ba sa shiri da Mama.
Har biyar saura sannan Karima ta tashi ta ce za su wuce, bayan Leenah na ta magana a kan Baba ya ce su dawo da wuri.
Ko da suka tafi, Karima cewa ta yi ba za su tafi a mota ba, wai wani saurayinta ne zai zo ya 蓷auke su. Hakan ya sa ta kashe ku蓷in motar da Baba ya ba su.
Babu yadda Leenah ta iya domin akwai nisa, ba za ta iya tafiyar 茩afa ba, kuma ita tsoro take ji. Hakan ya sa sai da ta bi Karima har inda saurayinta yake aiki. A nan ma suka 蓳ata lokaci, sannan bai zo kawosu ba sai ku蓷in mota ya ba su, ya ce su hau su tafi gida, yana da uzuri.
A bakin kan layinsu aka sauke su, a lokacin Leenah ta kai wuya da haushin abin da Karima ta yi. Ga shi yanzu kusan biyar da rabi, kuma Baba cewa ya yi su dawo da an yi la'asar.
Ko sauraron Karima da ke mata magana ba ta yi ba saboda ta yi fushi. Hakan ya sa ta bi bayanta tare da jan hijab 蓷in ta ta baya, wanda tana jan shi ya yage tare da biyo hannunta. Dama irin mai V 蓷in nan ne fashion, wanda ake yi da doguwar riga.
Take kanta, wanda babu ko 蓷ankwali, ha蓷i da gashinta wanda yake kitse, ya bayyana. Jikinta, wanda ko bra babu, kana ganin shatin yan madaidaitan 茩irjinta suka bayyana.
Ita kuwa bayan jan hijab 蓷in take ta jefa shi cikin kwatar da take kusa da su. Aikuwa me Leenah za ta yi in ba kuka ba? Ga shi ko 蓷ankwali babu a kanta. Rasa yadda za ta yi kawai ya sa ta tsugunna ta fara kuka.
Ita kuwa Karima zagi take mata na rashin mutunci tare da aibata ta. Tsaki ta yi ta juya za ta bar gurin, sai ta ji muryarsa.
Duk abin da suke yi yana kallonsu, domin shigowarsa unguwar kenan. Hakan ya sa ganin yarinyar nan, wacce yake cewa mahaukaciya kamar yadda yake fata, kawai sai ya yi niyyar wucewa. Amma kuma sai zuciyarsa ta darsa masa tausayinta, domin rauninsa shi ne ganin hawayen mace. Yana ganin inda Rooman ce zai iya wucewa kuwa. Kuma yadda take kukan har cikin zuciyarta abin yake ta蓳a wa.
"Ke kuma aikinki da kika zo yi duniya kenan, kuka? Aikuwa kin yi asara!"
Abin da ya fito daga bakinsa kenan. Duk da irin tsoron da muryarsa ta dasar a zuciyarta, amma ba ta iya daina kukan ba, domin ta muzanta sosai, ganinta a bakin titi babu ko 蓷ankwali bare kuma hijab.
Ita kuwa Karima tun jin muryarsa hanjin cikinta yake juyawa. Yau kuma wace 茩addara ce ta ha蓷a ta hanya da Madugu? Sosai jikinta yake rawa.
"Cire hijab 蓷in jikinki sannan ki cire kallabin da ke kanki hatta da takalman kafarki ki ciresu!"
Shi ne abin da ya fito daga bakinsa cikin sautinsa mai ban tsoro. Har ita da ba da ita yake ba sai da ta firgita, amma Karima da ta yi suman wucin gadi ba ta cire hijab 蓷in ba.
Marin da ya sau茩a wa fuskarta shi ne ya yi sanadin dawo da ita hayyacinta. Aikuwa babu shiri ta yi abin da ya umarce ta cikin gigicewa da azabar marin da ta sha.
"Madugu baya maimaita magana."
Shi ne abin da ya fa蓷a ba tare da ya kalli inda take ba.
Ita kuwa a garin saurin cire 蓷ankwalin, acuci mazan da ta yi da 蓷an kamfai ya fa蓷o 茩asa, ga kan kamar hammatar 'yan iska. Hakan sai ya ba Leenah dariya, duk da halin da take ciki. Ba ta san sanda ta 茩yal茩yale da wata irin dariya mai matu茩ar 茩arfi ba.
Da mamaki Madugu ya waiga ya kalleta, domin yanzu dai ya tabbatar da maganarsa a kan ciwon hauka ke damun yarinyar.
Sai dai kuma shi ma ganin abin da take yi wa dariya da kuma yadda take dariyar, bai san wani 蓷an 茩aramin murmushi yana niyyar bayyana a fuskarsa ba.
Da sauri ya daure fuskarsa damau, amma a zuciyarsa abin ya ba shi dariya. Hijab 蓷in ya 蓷auka ya mi茩a wa Leenah, wacce har lokacin dariyar ba ta tsaya ba.
"Ke!"
Ya daka mata tsawa. Aikuwa take ta ha蓷iye dariyar, jikinta kuma sai ya sake 蓷aukar rawa. Mi茩a mata ya yi, ta sa hannu ta amsa ta saka a jikinta.
Ita kuwa Karima kallonta ya yi ya ja wani dogon tsaki.
"Shegiya mai kama da maza,mummunan,Wai Kuma Nan mace kike? sannan ki fara tsallen kwado tun daga nan har zuwa gidanku."
Abin da ya umarce ta ta fara yi, domin har lokacin ba ta dawo daga azabar marin nasa ba.
Kamar mahaukaciya haka take tsallen kwadon, zuciyarta kamar za ta fito. Ita babban tsoronta ma shi ne ta kai gida ta daina ganin sa.
"Ke kuma mahaukaciya, wuce ki tafi, wawiya kawai."
Suf-suf ta fara tafiya. A zuciyarta tana fa蓷in, wai dama yana da kirki? Tunda ga shi ya taimake ta.
Tana tafiya shi ma ya biyo bayanta. Jin takunsa sai kuma zuciyarta ta fara bugawa da 茩arfi, tsoronta ya dawo farko.
Har suka kai 茩ofar gidan nasu, Karima tana tsallen kwadon, ga mutane masu wucewa, da masu son su yi magana. Amma suna hango Madugu sun san aikinsa ne, kowa sai ya ja bakinsa ya yi shiru.
Ita ma Leenah Allah-Allah take ta kai gida, domin har yanzu ba ta cire tsammanin zai iya janyo ta ita ma ya yanka ta ba.
Ko da ya kai 茩ofar gidansu, kamar ma bai san abin da ya faru ba ya shiga gida. Ita ma Leenah hakan ce a gare ta, domin gida ta shiga. Karima kuwa dama ta riga su isa gida.
Last free page 馃檹鉁嶏笍
Yanzu za mu tsunduma cikin wannan 茩asaitaccen labarin. Kada ku bari a yi ba ku, domin labari ne na musamman.
馃枻馃敟 INUWAR 茦ADDARA 馃敟馃枻
Shin me zai faru idan mutumin da ya fi kowa 茩in ganin mutum, shi ne ya zama wanda zai fara taimaka masa a lokacin da duniya ta juya masa baya?
Madugu! Mutumin da sunansa ka蓷ai yake sa Leenah rawar jiki. Wanda tun tana 茩arama bai ta蓳a 蓳oye 茩iyayyarsa gare ta ba.
Amma fa wannan karon, 茩addara ta ha蓷a su a wani yanayi da ba ta ta蓳a zato ba. 馃槶
Wani hijab da aka yaga...
Hawaye da suka cika idanun Leenah...
Da kuma hukuncin da Madugu ya yanke wa Karima! wannan shine sanadiyar kulluwar wani al'amari na musamman.
Amma tambayar ita ce: Shin wannan tausayi da ya fara ji a kanta zai iya sauya 茩iyayyar da ya da蓷e yana mata?
Ko kuwa wannan ma wata hanya ce ta 茩ara shiga cikin INUWAR 茦ADDARA?
shin Wai wanene sayyid ma gaba daya???
馃敟 Kada ku bari a ba ku labarin, ku karanta da kanku!
馃挰 Bayan karantawa, ku zo 馃枻馃敟 INUWAR 茦ADDARA 馃敟馃枻
馃敟 Kada ku bari a ba ku labarin, ku karanta da kanku!
鉁嶏笍 Marubuciyar INUWAR 茦ADDARA 馃枻
meelah bazata na alfahari daku鉁嶏笍馃グku shirya ku sake gyara zama,zaki nishadantu sosai鉁嶏笍鉁嶏笍