Free chapter 路 Read without an account
DADDY'S SPOILED SON
by Miss Nasir 路 DA茒IN HARAM
馃毈 (DA茒IN HARAM馃毈
By Maryam sulaiman
Miss Nasir 鉁嶏笍
Complete book 馃摎
Page 9-10
Da misalin 茩arfe goma na safiya, gari ya waye a wani katafaren gida da ke 蓷aya daga cikin manyan unguwannin Abuja, gidan Alhaji Abubakar Matawalle鈥攚ani attajiri da sunansa ya shahara a duniya sakamakon manyan kamfanoni da harkokin kasuwancinsa a 茩asashe daban-daban.
Rameez ne ya gama shiryawa tsaf cikin farar designer shirt da ba茩in wando, idanunsa sanye da tabarau. Ya fito daga 蓷akinsa ya nufi babban falon gidan. A can ya samu Daddy da kuma mom 蓷insa, Hajiya Safiya, zaune tare da wasu manyan ba茩i suna tattauna harkokin kasuwanci.
Amma duk da kasancewar iyayensa da ba茩i a wajen, ko gaishesu bai yi ba; ya wuce abinsa kamar bai ga kowa ba, lamarin da ya nuna tsantsar takamarsa da miskilancinsa.
Da zarar Alhaji Abubakar ya ga 蓷ansa, sai fuskarsa ta washe da murmushi duk da rashin gaisuwar da Rameez 蓷in bai yi masa ba.
"My boy! Come here," Daddy ya fa蓷a da kulawa.
Rameez ya 蓷an tsaya ba tare da ya sake fuska ba. Daga 蓷aya gefen falon kuwa, Hajiya Safiya ce zaune tana kallonsu da idanu cike da halin ko-in-kula da rashin amincewa. Ta ta蓳e baki, domin ita ka蓷ai ce a gidan da ba ta goyon bayan halayyar Rameez ko ka蓷an; ta tsani yadda mahaifinsa ke 茩ara ba shi gindin zama a duk abin da yake aikatawa.
"Abubakar, yaushe za ka daina 茩arfafa masa wannan halin ne?" Hajiya Safiya ta fa蓷a da muryar da ke nuna tsananin 蓳acin ranta.
Alhaji Abubakar ya 蓷ago kansa, yana kallonta da murmushi. "Wane hali kuma, Safiya?"
"Ka ga yadda yake shigowa babu girmamawa, kuma ka san irin abubuwan da ake ta ya蓷awa a kansa a gari, amma kai sai ka ri茩a binsa da hakan," ta fa蓷a tana hararar Rameez.
Rameez ya 蓷an ja tsaki a hankali, ya ciro wayarsa yana latsawa ko a jikinsa.
"Daddy, tell her to relax. It's too early for drama," Rameez ya fa蓷a a ta茩aice, ba tare da ya nuna wani daraja ga mahaifiyar tasa ba.
"Rameez!" Hajiya Safiya ta kira sunansa a tsawace. "Ba ka da kunya ko ka蓷an ko? Kana ganin saboda mahaifinka yana da ku蓷i ne za ka ci gaba da wulakanta kowa a gidan nan?"
Alhaji Abubakar ya 蓷aga hannu yana katse ta, kasancewar ya fi kowa son Rameez a duniyar nan. "Safiya, enough! Yaron nan ba 茩aramin mutum ba ne. Ya san abin da yake yi, kuma ya isa ya sarrafa kansa."
"To idan ya san abin da yake yi, me ya sa kullum sai an kira ka an sanar da kai wata sabuwar matsalar da ya jawo a gari?"
Rameez ya juya da niyyar barin wajen. "I'm heading out. You guys enjoy your morning."
Alhaji Abubakar ya bi shi da kallo cike da 茩auna. "Go, son. I'll see you later."
Hajiya Safiya ta bi shi da wani kallo mai cike da ba茩in ciki har ya fice daga falon. Ta juya ga mijinta tana girgiza kai. "Abubakar, wata rana za ka yi nadamar wannan goyon bayan da kake ba shi har ya lalace gaba 蓷aya."
Alhaji Abubakar ya 蓷auki takardun da ke gabansa yana murmushi. "Safiya, ina da manyan matsalolin kasuwanci da zan warware. Kada ki 茩ara mini da maganar Rameez, domin shi 蓷in na musamman ne a wurina."
Bayan fitar Rameez daga babban falon gidan, ya isa inda aka parke sabuwar motarsa ta alfarma kirar Rolls-Royce Ghost. Ya bu蓷e murfin motar ya shiga, sannan ya kunna kade-kade masu sanyaya zuciya a cikin sautin da ya wadatar da kansa kawai. Tare da hura turakin sigararsa ta Dunhill, ya fizgi motar a guje, ya fice daga harabar gidan Alhaji Abubakar Matawalle kamar wanda ke gudun hijira.
A titi, gudu yake ba ji ba gani, yana mai nuna cewa shi 蓷in wani ne da babu wanda ya isa ya isa da shi a birnin Abuja. Duk inda ya wuce, mutane na biye masa da ido saboda tsananin tsada da kasaitar motarsa, amma a wurin Rameez, hakan abu ne da ya saba da shi tun fil-al'azal.
Bai zarce ko ina ba sai wani shahararren lounge da ke tsakiyar birnin, inda abokinsa Zayyad da sauran takwarorinsa na daren shagala suka riga suka yi masa reserving na musamman. Yana isa, maigadi da ma'aikatan wurin suka gaggauta bu蓷e masa kofa cikin girmamawa, domin sun san wanene Rameez Matawalle鈥攂abban abokin hul蓷arsu da ke watsa ku蓷i ba tare da ya kalli lissafi ba.
Yana shiga cikin lounge 蓷in, hayaki da sautin waka suka bugi fuskarshi. Zayyad ya daga masa hannu daga nesa, nan take ya karasa ya zauna a babban kujerar da aka kebe masa.
"Bro, ka makara yau fa," Zayyad ya fada yana dariya tare da tura masa wata kwalbar wine mai gwanin tsada.
Rameez ya lumshe idanunsa, ya ajiye sigararsa a gefe, sannan ya ce da wata muryar takama: "Akwai dan wani tarna茩i ne da safe a gida, amma komai ya wuce. Ina sauran mutanen?"
"Suna nan zuwa. Amma ka ji labarin sabuwar yarinyar da ta shigo gari kwanan nan kuwa? Wanda ake cewa ita din ba mai sauki ba ce?" Zayyad ya tambaye shi yana mai kallonsa da wani irin kallo na zolaya.
Rameez ya saki wani 蓷an guntun murmushin rainin hankali, fuskarsa cike da miskilanci da zafin zuciya. A wurinsa, babu wata mace a duniya da ta isa ta gaba da shi ko ta fito ta nuna masa tana da taurin kai.
"Wace ce ita da har zata gagara a wurina?" Rameez ya fada, yana mai jin cewa daren yau zai zama daren da zai sake nuna wa duniya cewa shi ne sarkin da babu mai bugar da shi a fagen takama da iskanci.
Miss Nasir 鉁嶏笍