Free chapter · Read without an account
Chapter 47
by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI
***
***
***
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
Chapter 47.
*
Sakin baki da hanci Zunaina ta yi, tana kallon Junaid a mamakance domin kuwa maganar cikin da ya yi ta dake ta da ƙarfi.
Sau bakwai tana buɗe bakinta da zummar yin magana, amma kuma maganar bata fitowa, tana tsayawa ne a cikin kanta.
Rintse idanuwanta ta yi tana sauraren adadin dokawar da zuciyarta ke yi a ƙirjinta, cikin rawar baki ta fara da ambatar sunan shi murya a raunane.
"Ju, Ju, JUNAID ina cikin ya ke, waye ke ɗauke da cikin, cikin Muhammad ɗina?." Ta ƙarashe maganar tana saka duka hannayenta ta dafe cikinta, wani ɗumi na saukar mata lokaci ɗaya.
Rintse rinannun idanuwansa Junaid ya yi, yana jin yanda kanshi ke sarawa da tunanin Masoyi, ɗan uwa, aboki kuma aminin shi Muhammad ko wane hali ya ke ciki.
"Na tabbar, ba ni dakaina na tabbatar ba, Doctor ne ya tabbatar min kina ɗauke da ciki na haihuwa a jikin ki, lokacin dana kaɗe ki da mota."
"Miyasa sai yanzu?". Ta yi tambayar murya a bushe.
"A'a ba sai yanzu ba, tun lokacin ne". Ya tabbatar mata.
"Muhammad fa! koya sani?." Ta yi tanbayar wani abu me nauyi na taushe zuciyarta.
"Bansani ba ko ya sani, bazan iya tabbatarwa." Ya amsata yanajin ɗaci a bakinsa.
"To ka sanar da shi please, zai yi murna, zai yi farinciki wataƙila har kukan daɗi zai yi, idan ya ji ina ɗauke da cikinsa." Ta faɗa tana hasaso yanayin da Muhammad ɗinta zai iya kasancewa idan ya yi tozali da labarin tana ɗauke da cikinsa na haihuwa.
"A ina zangan shi?." Tambayar ta kubto daga bakin shi.
Buɗe baki Zunaina ta yi da zummar yin magana, amma sai mi zai faru? wani dunƙulallen jini ne ya soma faɗowa daga bakinta guda-guda.
Wannan shine ga samu ga rashi, zuciyar Junaid ta faɗi.
A razane ya matsa kusa da ita, zai yi magana sai ya soma lura da numfashinta na sauyawa, bai daina fita baki ɗaya ba, amma yana iya gane yanda ya ke mata wahalar shaƙa. Cak ya ɗauketa cikin hannunwan shi ya nufi ƙofar fita.
"Innalillahi, mi yake faruwa haka miya sameta wai?." Uncle da fitowar shi kenan ya watsowa Junaid tambayar yana ƙarasowa inda yake saɓe da ita.
A kuma daidai lokacin ne Tambari ya soma bayyana, ba a wani waje na daban ba a jikinta akan fuskarta wajen goshinta, a nan tambarin ya bayyana, kamar yanda ya saba bayyana a mabanbanta wajaje, yana nan kamar yanda ya ke tambari ne me kalar ɗigon ruwa ko wani abu me kauri da za'a iya ɗigawa, amma kuma shi jah ne launin ja ne dake danganta tambari da jini kai tsaye 💧.
A mugun razane Uncle ya ja da baya, yana sharce gumin da ya soma tsatsafo ma shi nan take, a ɗimauce ya faɗa ɗakin Saminaka shi kanshi bazai iya cewa ga abin da yake yi ba, kawai de ya san ya ɗauko abu guda biyu a hannunsa, bai san kuma yanda aka yi ba sai ya tsinci kan shi da buɗe gora ɗaya ya matsa inda suke hannun shi na kakkarwa ya buɗe bakinta da ƙyar na soma bulbula mata shi.
Minti ɗaya, minti biyu, uku, huɗu.
Ƙwararan mintuna goma suka shuɗe shiru, babu hayaniya, babu kuma sauti me ƙarfi, haka kuma fitar numfashin Zunaina bai daidaita ba saide sannu ahankali tambarin ya soma ɓacewa yana bajewa, hayaƙi na fita daga goshinta, sannan wani tsinkakken jini ya sake ɓalle mata hanci da baki.
"Junaid, Innalillahi ya zamuyi da ita?."
Uncle ya tambaya yana duƙewa kamar yanda shima Junaid ɗin ya duƙe tare da kwantar da ita a saman lallausan carpet.
"Mu jira."
"Kaɗan."
Ya faɗa yana sake nitsar da ganin shi a kanta, zuciyar shi naharbawa fiye da ƙima.
A can cikin kwanyar shi kuma soma tarawa yana warwarewa ya yi, tare da tattaro bakunan zarurran da suka harɗe yana son daidaita komi.
"Jini."
Ya faɗa a fili kamar me son tabbatarwa, can ƙasan zuciyar shi na ƙullewa da wani abu, wani abu me kama da son ɗaukar mataki, matakin da zai datse ɗaurin zaluncin da azzalumai ke yi don cimma wata manufa da kuɗiri nasu, yayinda yakai matuƙa wajen hasala shi.
"Ta ina zan soma?."
Ya yi maganar a gajiye.
Kallon tuhuma Uncle yabi shi da shi, kafin ya girgiza ma shi kai cikin son kyautata ma shi zato ya ce.
"Ban sani ba."
"Amma kuma..." Sai ya yi shiru bai ƙarasa ba ya raba hankalin shi biyu, rabi ga Zunaina rabi ga Junaid.
"Uncle!." Junaid ya kira sunan shi kamar me son roƙon wani abu.
"Ina so ka kauda kanka matsawar kasan ba zaka taimaka min ba a wannan karon.
Bazan iya jure ganin wannan abin na faruwa ba ana cutar da bayin Allah basu jiba basu gani ba, ina da ikon dakatarwa amma ka hana ni aikata hakan."
A razane Uncle ya miƙe tsaye yana nuna Jay da yatsa, bakin shi na rawa, sai kuma ya kasa cewa komi, ya juya ya fice yana haɗe hanya.
"A wannan karon bazan takata ba dole ne inkawo ƙarshen du wannan, kobadan abin da suka yiwa Abeey ba, zan ɗauki fansar Muhammad da sauran rayukan da basu ji ba basu gani ba."
Wani abin mamaki daya sake ƙarfafa shi ne ya faru a lokacin.
Zunaina, a cikin yahayin ciwo da azaba take amma hakan bai hana ta riƙe wani sashe na Jay ba tana kokowa da fita da shigar numfashinta ta furta.
"Zan..zan.zankasance a.a.a.a.tare da kai, ina bayanka zamuyi yaƙi a tare na yi alƙawari da rayuwa da jinina wannan yaron da ke cikina bazai fito duniya ba face komi ya daidaita zamu kawo ƙarshen komi, zamu sauya komi, ni da kai da kuma abin da zan haifawa Muhammad."
Ta faɗa numfashinta na tsayawa cak.
Wani irin lumashe ido Junaid ya yi yana shaƙar iska da ƙarfi yana janta har cikin huhun shi.
*
A daidai wannan lokacin a ɓangaren Maryam wani alƙawari da yayi daidai da cikar wata ƙaddara ya afku.
Ta kama hannun Rimsha ta rintse a cikin nata hannun, sannan a hankali cikin sanyi wanda ke cike da sassarfa ta lumshe ido da sassanyan sauti me fitowa cakuɗe da bacin rai ta soma faɗin.
"Hafsa da du wani me hannu cikin aikata zalunci da son zuciya na yi alƙawarin kawo ƙarshen su."
Sai taja numfashin sannan taci gaba
"Ni kaɗai bazan iya ba amma kuma ina da tabbacin iyayena da suka raineni ba zasu barni haka nan ba, zasu agazamin har sai na cimma burina, Makafa, Ƙwaro, Hafsa da sauran muƙarrabansu su jirayi bayyanata a gare su."
Ta faɗa jikinta na kakkarwa har kokacin idonta na a rintse.
To masu karatu da Junaid da Zunaina da Maryam sun yi ƙuduri iri ɗaya.
Mi kuke tunanin zai faru, shin zasu cimma burukansu, ko kuma wani abun na daban zai faru?.
Ina labarin Ƙwaro ubangidan Makafa da tun da ya ɗanawa Makafa tarko ya kama gabanshi.
Kuci gaba da bina sannu a hankali dan jin yanda zata kaya.
Ina baku haƙuri akan rashin zuwan labari jiya, yauma kuma bai samu da yawa ba in sha Allah zanyi ƙoƙari zuwa goben idan rayuwarmu ta kai inyi muku me ɗan yawa.
MARYAM STAR.